Wai shin ‘yan Nijeriya za su koma su cigaba da girmama shugabanni?

Daga KWAMARED IBRAHIM ABDU ZANGO

Na rasa dalilai ƙwarara ta yadda al’adunmu na ƙwarai suka shuɗe babu girmama shugabanni: wannan abu ya biyo bayan cewa wai kai ya waye! Babu wani addini cikin Duniyar nan da yake sako-sako da tarbiyyar al’umma ko ina a Duniya kuwa.

Tarbiyyar jama’a ita ce ke tafiyar da rayuwar al’umma gabaɗaya. Mene ne dalilin daje jawo rashin tarbiyya a yanzu cikin al’umma, kususan tamu a wannan lokaci? Da ɗai babu ko shakka siyasa ta cikin wata aba dimokraɗiyya su ne asalin kawo cikas ga tarbiyya saboda ƙarairayin da suka rataya bisa waccan kalma dimokraɗiyya.

Gaskiya ne ita siyasa hanyar mulki kenan, wato kalma ce wacce take nufin mulkar jama’a ta hanyar zaɓe irin na dimokraɗiyya. Gaskiyar lamari ga duk mutumin da ya iske siyasar 1960–1966, su waɗancan ‘yan siyasar sun bi hanyoyi na taimaka wa jama’a bisa hanyoyin gaskiya da kyautata wa jama’a bisa yadda ya kamata, ba tare da nuna bambanci ba.

Gaskiyar lamari, sojoji sun yi mulki shekaru masu yawa wanda ‘yan Nijeriya sun koyi tarbiyyar sojoji waɗanda suka banbanta da na ‘yan siyasa. Gaskiya soja bin umarni kawai ya sani, su kuma ‘yan siyasa wai bin ra’ayin jama’a kawai koda kuwa hanyoyin tarbiyyar sun sha banban da al’adu da kuma tsari mafi girma na addini.

Matuƙar mutum yana son kyakkyawar rayuwa, to tarbiyyar addininsa ita tafi kyautatuwa gare shi. Duk da cewa, tun shekarar 1999 muka dawo da mulki irin mulki na dimokraɗiyya, amma bamu ci burin wannan kalma ba tunda komai ya lalace ta fuskoki da dama, saboda jama’armu kususan samari ba sa girmama manya.

Ba wai kawai masu mulki ba, kowa bashi da ƙima wurin waɗannan samari a wannan zamani! Ku duba dai yadda mutane kususan ‘yan Arewa suke kushe shugaba Buhari wataƙil saboda ‘yancin Ɗan adam da siyasar dimokraɗiyya ta kawo ta yau Ɗan adam wanda ko da marar gaskiya ne, take ɓoye tasa cutar har yake da ikon faɗar wasu bankaɗe-bankaɗe.

Gaskiya duk mai mulki idan ababe marasa daɗi suka faru to fa koda na asali ne, to fa shugaba shi ne yake da alhakinsu. Yanzu na ga wasu mutane suna caccakar shugaba Buhari cewa domin me yake zuwa Daura kuma akan me? Gaskiya faɗin haka wauta ne daga wawa domin babu wani ɗa na halal wanda za a hana shi shiga gidan mahaifinsa matuƙar aibunsa bai shafi addini ba.

Yana da kyau idan mutum zai yi batu, to ya tsaya ya Ankara da ababen da zai ambata. Gaskiya ne mulkin janar Buhari ya sami kansa ciki kwanzama domin irin ra’ayin da gwamnatinsa ta runguma akwai waɗanda da yawansu suka takura wa ‘yan Nijeriya gabaɗaya!

Ababen a bayyane suke, domin ‘yan Nijeriya kususan talakawa mun shiga halin ni-‘ya-su, saboda tsananin talauci da ya addabe mu. Kuma wannan ya faru saboda matakai da gwamnati ta ɗauka tun lokacin janar Babangida na shigo da wata hanya ta karya wuyan arziƙin Nijeriya, wato wata muguwar hanyar karya tattalin arziqi wai ita “SAP”.

Wannan mashahuriyar ƙeta ce wacce take lanƙwame duk wata ƙasa da ta rungume ta tun wancan lokaci har lokacin da Janar Buhari ya hau mulki a shekarar 2015. Daga nan kuma sai ma abin ya yi ƙamari gwamnatin ta ƙara azamar buɗe hanyar rugurguza tattalin arziƙin Nijeriya domin daɗaɗawa Bankin Duniya da wata muguwar kafar Turai wai ita IMF.

Gaskiya domin ƙara wa gyambo gishiri sai rufe bodojinmu, ance wai domin hana shigowar makamai! Wannan rufe bodoji ya shafi ‘yan Arewa domin kayayyakin dake shigowa domin buƙatar jama’a babu su. Kodayake, mu nce ‘yan arewa, amma bodojin sun shafi ‘yan kudu kususan garuruwan Yarabawa da kuma Kurosribas tsakaninsu da ƙasar Kamaru. Kodayake yake sun yi boda da Biniwai ne ko Taraba, domin na ga Katsina Ala ko Biniwai ne ko Taraba! Gaskiya waɗannan da wahalar rayuwa ta jawo wa gwamnatin Buhari baƙin jini, duk da cewa har gobe jama’a basu san cewa akwai mutanen ɓoye masu assasa wanga lamari domin gurgunta gwamnatin ba.

Ita gwamnatin Buhari ta gaji wasu abubuwa kamar Boko Haram, kama mutane domin a nemi kuɗin diyya – wannan ya faru tun sojoji a wurare kamar Delta da kudancin Nijeriya ta gabas, wannan kuwa ya san da haka – amma ababen sun yi ƙamari a Arewa wurin da shugaba Buhari yace musu ci ma zaune sun fi yawa.

Kodayake, ga duk mai zirga-zirga cikin ƙasar nan zai fahimci cewa abin ya shafi kowanne gefe. Ɗauki lokacin soja a Bendel ta da wanda kowanne ƙaramin yaro yana da bindiga kususan zamanin wani mugun ɗan fashi wai shi Anini!

Ka ga ababen sun yi nisa tuntuni Nijeriya tana cikin matsanancin rikici tun wancan lokaci, sai dai yanzu inda idanuwa suka buɗe kususan a nan arewa inda a da bamu san haka ba. Kamata ya yi mutane su gane cewa, kamar yadda Turawa kance “Several theatres of conflicts” wato “yawaita yaɗuwar masifu”.

Duk ƙasar da ta sami kanta cikin waɗannan masifu sai addu’a ita ce kawai mafita tare da ƙarfafa gwiyoyin sojoji da sauran jami’an tsaro amma ba kushe ba. Kuma duk wata gwamnatin da ta zo waɗannan masifu ba za su kau cikin ƙiftawar ido bs, domin yaƙi ake yi da ‘yan gida, Allah ya tsare.

Gaskiya tsarin Allah muke nema tun farkon wannan mulki daga 2015 zuwa har ƙarshen siyasasr Nijeriya. Laifuffukan wannan gwamnati wataqil baya fice cewa za ta yi bincike-bincike na gwamnatoci bayan, wanda abin mamaki har marigayi Janar Sani Abacha!

Gaskiya mutanen boye idan ance ko ana zarginsu da yadda Nijeriya take ciki tuntuni musamman fitowar Boko Haram, satar shanu, rikice-rikicen Filato, wannan abu har can jihar Delta na fasa bututun man fetur, waɗannan abubuwa tun kafin mulkin Buhari suke sanadinsu shi ne ba a son bincike koda Allah Ta’ala ya hana bincike, domin tada fitina yake kawowa. Ka san ba a san gwamnatin farar hula da bincike ba, koda kuwa za a yi, sai dai cikin sirri!

Kwamared Ibrahim Abdu Zango.
Ciyaman ɗin Kano Unity Forum,
No. 260, Zango Quarters, Kano, Kano State, Nijeriya
GSM: 08175472298

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *