Wang Yi ya jaddada buƙatar aiwatar da matakan gudanar da cuɗanyar sassa daban-daban a zahiri

Daga CMG HAUSA

Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga ƙasashe mambobin ƙungiyar G20, da su nacewa aiwatar da matakan gudanar da cuɗanyar sassa daban daban a zahiri, domin wanzar da zaman lafiya, da ingiza ci gaban bai ɗaya a duniya baki ɗaya.

Wang, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Juma’a, lokacin da yake halartar taron ministocin wajen ƙasashe mambobin G20 a Bali na ƙasar Indonesia.

Ƙungiyar G20 dandali ne na ƙasashe 19, masu samun saurin bunƙasar tattalin arziki da tarayyar Turai EU.

Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa