Daga CMG Hausa
Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya kira taron ganawa da manema labarai a yammacin jiya, bayan ya halarci tarukan ministocin harkokin wajen ƙasashen gabashin Asiya da aka shirya a birnin Phnom Penh, fadar mulkin ƙasar Cambodia domin kyautata haɗin gwiwa a tsakaninsu.
Yayin taron manema labaran, Wang Yi ya ce, “Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosy, ta yi watsi da adawar gwamnatin ƙasar Sin, ta kai ziyara yankin Taiwan, bisa amincewar gwamnatin ƙasar Amurka”.
Ya ce a bayyane yake cewa, ziyararta ta keta ‘yancin mulkin kan ƙasar Sin, kuma ta tsoma baki cikin harkokin gidan ƙasar, haka kuma ta saɓa wa alƙawarin gwamnatin Amurka, tare kuma da lahanta zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.
Don haka, tabbas ƙasar Sin ta mayar da martani ta hanyar ɗaukan matakai masu karfi da suka dace bisa matsayar adalci. Kuma ko shakka babu, atisayen soja da rundunar sojojin ƙasar Sin take yi a fili, ya dace da dokar ƙasar, da ta ƙasa da ƙasa, da kuma ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
A cewar Wang Yi, manufar ita ce, yi wa masu tayar da tarzoma kashedi, da kuma hukunta masu neman ‘yancin kan Taiwan. Haka kuma, za a ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kiyaye ‘yancin mulkin kan ƙasar Sin da yankunan ƙasar, da murƙushe yunƙurin Amurka na hana ci gaban ƙasar Sin bisa fakewa da batun yankin Taiwan, tare kuma da murƙushe maƙarƙashiyar mahukuntan yankin Taiwan na neman ‘yancin kai bisa dogaro da goyon bayan Amurka.
Bugu da ƙari, Wang Yi ya ce ƙasar Sin na ƙoƙarin kare dokar ƙasa da ƙasa, da ƙa’idar hulɗar dake tsakanin ƙasa da kasa, musamman ma ƙa’idar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran ƙasashe ta MƊD, yana mai cewa, “Idan aka yi watsi da ƙa’idar, manyan ƙasashe kamar Amurka za su zalunci ƙananan ƙasashe kamar yadda suke so, amma ba zai yiyu ƙasar Sin ta amince da faruwar irin wannan al’amari ba, kuma ya dace ƙasashen duniya su hada kai domin hana koma bayan wayewar kan bil Adam.”
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa