Wata ta kwana sanye da kayan barci kusa da Masallacin Harami na Makkah

Manhaja logo

Wata mai suna Lauren Issa sanye da kayan barci, ta kwana kan tsaunin da ke kallon Masallacin Harami a Makka, sannan ta wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na intanet.

Matar ’yar asalin ƙasar Siriya ta kwana a kan tsaunin ne kwanciya ta jin daɗi irin ta masu yawan shakatawa, gari na wayewa, ɗauki hoton kanta, ta kuma sa a shafinta na Instagram.

Hakan na cikin wani gajerin bidiyo ne da wasu masu kishin abubuwan da ke faruwa a ƙasar Saudiyya suka wallafa a shafin sada zumunta na Facebook domin ankarar da jama’a.

Hoton bidiyon matar ya nuna ta sanye da riga mai gajeren hannun da dogon wando, kanta a buɗe, gashinta a waje, kwance a cikin bargo wanda ta lulluva, sannan ta tashi daga shimfiɗar tana rangwaɗa.

Hakan ya harzuqa mutane da dama, yayin da wasu ke nuna takaici, wasu kuma na kira da a kama matar a hukunta ta da kuma waɗanda suka ba ta damar hawa wannan wuri da kuma ƙeta alfamar wurin.

Wasu kuma sun yi tir da ita, sannan suka dora alhakin hakan ga Yarima Saudiyya, Muhammad Bin Salman, da ya bayar da ƙofar hakan ta hanyar irin buɗe ƙofar badala da ya yi da abin da ya kira ‘sauye-sauye na zamani’.

A makonnin da suka gabata ne aka yi bikin gargajiyar Turawa na dodanni da ake kira da Halloween, aka kuma yi bikin casu a salo irin na Turawan a Riyadh, babban birnin ƙasar, lamarin da ya janyo cece-kuce.