Aure ya wuce maganar ɗaukar nauyi kawai

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon mako a jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Maudu’inmu na wannan mako shi ne maganar ɗaukar nauyin iyali da yadda ya shafi zamantakewar aure. A sha karatu lafiya.

Ma’anar ɗaukar nauyin iyali

Ɗaukar nauyin iyali yana nufin ɗaukar nauyin da maza suke yi na matan da suka aura da yaran da suka haifa ta fuskar sha’anin kuɗi. Ɗaukar nauyi ya haɗa da ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, kula da lafiya, ilimi da sauran madangantansu.

A al’adar Bahaushe da addinin musulunci, nauyi ne a kan kowanne magidanci ya kula da waɗancan buƙatu na iyalansa. Kuma akwai hukunce-hukunce da addinin Islama ya tanada na yadda za a yi da kuma ga wanda bai iya kula da iyalinsa bayan yana da hali.

Batun ɗaukar nauyin iyali da muhimmancinsa a ƙasar Hausa

A ƙasar Hausa, an mai da ɗaukar nauyin iyali a matsayin abu mafi muhimmanci a zamantakewar aure. Ko da a wajen bincikar wanda ya zo neman auren ‘ya’yansu suna ba da muhimmanci ga hanyar da yake samun kudinsa (sana’arsa) fiye da dukkan wani abu.

Kuma mafi yawan lokuta idan ya tsallake wannan gwajin an samu yana da sana’a mai ƙwari sosai, da wuya sauran halayen nasa su yi tasiri. A ƙasar Hausa idan mace ta girma a gidansu musamman masu ƙaramin ƙarfi, sai ta ji ta a takure, kullum ba ta da buri sai dai ta yi aure ta huta da wahala. Kuma kowa ma haka ya zata.

Su kuma maza suna tunanin kawai ita matar sun aure ta sun taimaka mata sun raba ta da takura. Shi ya sa mazan ba sa gane cewa su ma fa rufa musu asiri aka yi aka ba su gudan mutum ɗungurugun suka aura. Sannan kuma ke ma mace ki ɗauki kanki da ƙima da daraja.

Ba wai taimakonki aka yi ba aka aure ki. Domin wasu matan sun ɗauka iya arzikinta iya biyayyarka. Kuma ko yana da shi, ko bai da shi Allah ne ya ce a yi aure ba don ki huta ba. Kuma ba a ce sai yana iya ɗaukar nauyin ki za ki yi masa biyayya ba.

A ƙasar Hausa ne kaɗai ake da wannan tunanin. Na taɓa ganin wani rubutu a kan auren indiyawa. A ciki suka kira miji da Ubangiji. Haka ake nusar da yara mata tun suna kanana. Yarinya za ta tashi tana ganin mijin da za ta aura wani garkuwa ne a gare ta, wanda za ta yi wa biyayya fiye da mahaifanta. Amma a ƙasar Hausa saniyar tatsa ne, wanda ba shi da daraja sai wannan hidimar da yake miki.

Ya kamata kuma dai a san aure taimakon juna ne. Namiji shi ne mai ba wa mace kariya da ɗaukar nauyi, amma cikin girmama nata ƙoƙarin. Ita kuma mace ayyukanta ta kula da miji da gidansa, ta sarrafa cefanen da ya kawo, ta haifar masa zuriyya,ta yi tarbiyya da sauransu. Ka ga kenan ba zancen shi ya taimaka mata ko ita ta taimaka masa. Kowa na buƙatar kowa.

Hakazalika ya kamata a sani, ci da sha da ɗaukar nauyi da sauransu Allah ne ya shar’anta ba wai taimako ba ne. Wata ma gatan da take da shi na ci da sha da asibitin da ake kai ta a gidansu ya ninninka wanda za ka kai ta a daraja. Ka ga kenan ba taimaka mata ka yi ka auro ta ba.

Biyayyar Allah ce ta sa iyayenta suka ba ka ita. Allah ne ya ce a aurar da yara mata idan sun kai munzali. Kwaɗayin wannan ya sa suka ba ka ita, ba wai sun gaji da ita ba ko suna gudun ɗaukar nauyin ta ba. Sai don ta je ta raya sunnar mahalicci.

Hakazalika, kada namiji ya dinga ganin mace a matsayin maƙasƙanciyarsa wacce zai iya wulaƙantawa duk lokacin da ya so. Allah ne ya raba ya ba shi wannan aiki na ɗaukar ɗawainiyar iyali. Ita ma macen an raba an ba ta nata aikin.

Kuma kamata ya yi da mijin da al’ummar Duniya su jinjina mata a kan wannan aiki nata na sadaukarwa. Ita ce mai kula da gida, da dukkan wasu ayyuka nasa. Haka ita ce mai tarbiyyar yara, bayan ta ɗau ciki tsahon watanni ta haife shi. Ko haɗarin da rayuwarta ke shiga a wannan lokuta. Ba don ita ta zaɓa ba, Allah ne ya raba ya ba ta kamar yadda kai ma ya ba ka.

Wasu matan sun fi karfin abinda ake ba su a gidan mijin, kuma ba sa samun kyautatawar da ta dace daga mijin, amma suna zaune ne saboda kare mutuncinsu da son da suke yi wa mijinsu da kula da yaransu. Ka ga ba maganar tana zaune saboda ta samu mai ɗaukar ɗawainiyarta ba ne.

Hakazalika akwai wasu da su suke ɗaukar nauyin mijin da yaransu. Sai ka ga gidan ma da ake zaman auren ma fa nata ne. Amma sun zavi su zauna don kula da yaransu da yin bautar aure. To a ina muka samo zancen wai aure rufa wa mace asiri ne?

Idan ma rufin ashirin ne dai ba ta fuskar ɗawainiya ko ɗaukar nauyi ba ne. Mata ma masu arziki sosai suna jin ba za su iya rayuwa ba namiji ba. Kuma har su samu namijin da bai kama ƙafarsu a arziki ba su aura. Ka ga kenan akwai wani abu dai a cikin auren bayan ɗaukar nauyi.

Wannan ya kamata iyaye da malamai su dinga kwaɗaitar wa mata a zaman aure. A yi zaman aure don ibada da kare mutunci. Ba wai a tsorata mace a ce ta yi aure ko kada ta fito daga gidan aure saboda za ta rasa ɗaukar nauyi. shi ya sa wata sai ta ga idan tana da aiki ko sana’a ba ta buƙatar aure.

Wata kuma nauyin da iyayenta suke yi wani zubin ya fi darajar na gidan mijin. Wasu lokutan ma a gidan mijin iyayen ke ɗaukar ɗawainiyarta da ‘ya’yanta. Iyayen ba su son ta dawo gida duk da su suke wahalar. Amma kuma suna son ‘yar su ta zauna saboda sun fahimci aure ne mutuncin ɗiya mace.

Wasu al’adun ma a Nijeriya mace ce ke zuwa ta nema da kanta ta yi duk abinda za ta yi. Maza suna gida suna kwance aikinsu kawai su sadu da ita, shikenan.

Amma kuma wannnan bai hana a girmama namiji ba da dagewar da yake wajen ɗawainiyar iyali. Hakan ba ƙaramin jihadi ba ne. Ke macen da kike ɗaukar ɗawainiyar gida kin fi kowa sanin haka. Nan da nan za ki ga kin gaza.

Amma shi kullum ya samo dare da rana, kafin ya yi wa kansa abu guda ya yi miki ɗari ke da yaranki.

Kuma macen da take gani don ta samu Duniya ba ruwanda da aure, ta sani aure ba maganar ɗaukar nauyi ce ba kaɗai. Akwai maganar kare mutunci da ibada. Idan kuma da aure ba wanda ya isa ya keta miki alfarma. Namiji shi kaɗai a wajenki garkuwa ne. Ballantana jajirtacce wanda zai iya nemowa yana ɗaukar nauyin iyalansa.

Hakazalika, su ma maza wannan faɗar Allah ce, sai a kiyaye. Kada a dinga gori don ana ɗaukar nauyin iyali kuma daga nan a zobe ladan da aka samu. Kada a dinga ganin taimaka wa mace kawai ake yi don idan ka sake ta za ta tagayyara.

Kai ma tana rufa maka asiri da za ka yi karatun ta-nutsu. Duniya ce kawai take maka zuga kana ganin kamar kai ne a sama. Dukkanku bayin Allah ne kuma bauta kuke a zaman aure.

Kuma kowa zai samu sakamakon bautar a wajen Allah. Allah ya sa mu dace. Allah ya zaunar da ma’aurata lafiya a gidajensu. Sai mun haɗu a wani makon idan Allah ya kai mana rayukanmu.