WHO ta ziyarci Zannan Askar Sarkin Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Zannan Askan mai Martaba Sarkin Gombe, kuma Sarkin Askan Bolari ta Gabas a Jihar Gombe, Dokta Yunusa Adamu, ya nuna matuƙar farin cikin shi akan ziyarar da Hukumar Lafiya ta Duniya, wato World Health Organization (WHO) ta kai mishi a harabar warakar shi kwanan nan, inda jami’an hukumar suka yi bincike da nazari a kan irin ayyukan shi daga bisani kuma suka gamsu da su.

Malam Yunusa Adamu wanda ya yi wannan tsokacin a Gombe a makon jiya yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai, ya furta cewa, ziyarar da jami’an na WHO suka kai mishi manuniya ce ga irin muhimmancin da suka ga waraka irin tasu na maganin Islama da na gargajiya yake da shi a tsakanin al’umma, kuma ya ƙaryata zargin da ake yi cewa magungunan gargajiya ba su da alfanu a wurin al’umma.

Ya ce, a baya can ma Hukumar UNICEF mai bada tallafin ilimin yara ta duniya, ta ziyarce shi kuma jami’an hukumar sun gamsu da warakar sa da yake yi ga al’umma waɗanda suka haɗa da yara, yana mai ƙarawa da cewa, “lalle ziyarar manyan hukumomin nan biyu na duniya zuwa wuri na, ya ƙara mini ƙwarin gwiwa, kuma ina musu godiya da gamsuwar su a kan warakar da nake yi. Allah kuma ya taimake su, su ci gaba da ziyara zuwa wurin ire-iren mu.”

A nan, sai Dakta Yunusa ya nunawa wakilin mu lambar yabon da hukumar ta ba shi mai taken “The Best Traditional Herbalist in Gombe”, ma’ana, mai maganin gargajiya mafi ƙwarewa a Gombe.

Dakta Yunusa sai ya jinjina wa Gwamnan Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya akan dashen bishiyoyi da yake yi a faɗin jihar, yana mai cewa, ba ƙaramin tasiri ne bishiyoyin za su yi a wurin mutane ba, musamman irin su masu waraka da maganin gargajiya kuma ya zama musu dole su kare bishiyoyin daga irin masu sassare itatuwan nan ba ji ba gani.

“Muna godiya ga Maigirma Gwamna,” inji shi.

Daga ƙarshe, Zannan Askan Sarkin Gomben sai ya roƙi gwamnan cewa duk lokacin da gwamnatin sa ta shirya bada tallafi ga masu sana’a a jihar, to suma wanzamai da takwarorin su masu bada magungunan gargajiya, a tuna da su.

Shi dai Dakta Yunusa ya yi suna wajen warkar da masu jinya ko suna da kuɗi ko ba su da shi, kuma takwarorin sa masu irin sana’ar shi da dama a Gombe, sun yi amanna da ƙwarewar shi akan aikin shi. “Ai shi Zannan taimako yake yi tsakanin shi da Allah,” inji tagwayen wanzamai Hassan da Husaini na Sabon Layi, Gombe.