Daga WAKILINMU
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ƙara yawan waɗanda suke yi masa hidima daga mutum 100,000 zuwa 200,000.
Wike ya bayyana haka ne a wajen bikin rantsar da runkunin farko na hadimai na musamman su 100,000 wanda ya gudana a mazaɓar Sanatan Ribas ta Gabas da ke Ƙaramar Hukumar Ikwerre a ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa, sakonni mara adadi da yake samu daga ‘yan jihar dangane da neman muƙamin ya sa ya naɗa hadimai da yawa.
Ya ce, jama’arsa na ganin ayyuka sun yi masa yawa don haka akwai buƙatar ya ba su dama su taya shi gudanar da wasu harkokinsa.
Kazalika, ya ce da yawan ‘yan jihar sun amince su bayar da tasu gudunmawa ba tare da yanka musu albashi ba.
A cewarsa, hakan ya sa ya ga dacewar ya ƙara yawan hadiman nasa daga mutum 100,000 zuwa 200,000.
Gwamnan ya ce, ya umarci shugabannin siyasa na jihar kowa ya bincika a yankinsa sannan ya zabo masa waɗanda ake ganin sun cancanta a bai wa mukamin.
