Canja fasalin Naira: Mu na sa ido kan wasu gwamnoni da ke yunƙurin biyan albashin ma’aikata a hannu – EFCC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta ce tana sa ido kan gwamnonin ƙasar uku sakamakon yunƙurinsu na halasta kuɗin haram da biliyoyin kuɗin da suka tara ta hanyar biyan ma’aikata albashi a hannu maimakon ta banki.

Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa dakarunsa za su ci gaba da kai samame kan ‘yan canji game da zargin ɓoye Dalar Amurka wanda hakan ke sa darajarta na hauhawa.

Duk da cewa Bawa bai faɗi sunan gwamnonin ba, ya ce biyu daga cikinsu daga Arewacin Nijeriya suke, inda ɗayan yake a Kudanci.

Ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa gwamnonin sun kammala shirin fito da kuɗin ta hanyar biyan ma’aikatansu na jiha da garin kuɗi maimakon ta banki kamar yadda aka saba.

“Bari ku ji, a rahoton sirri da na samu jiya, tuni wasu gwamnonin jiha da suka ɓoye garin kuɗi a gidaje yanzu suka fara ƙoƙarin biyan albashi a hannu a jihohin nasu,” inji shi.

Da aka tambaye shi ko EFCC za ta yi wa gwamnonin sammaci, Bawa ya ce suna dai saka musu ido zuwa yanzu.

EFCC na ɗaukar matakan ne a baya-bayan nan bayan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da shirin sake fasalin takardun Naira na Naira 200 da Naira 500 da Naira 1,000, inda ya bada wa’adin kwana 47 ga ‘yan ƙasar da su kai tsofaffin banki.

Wasu masana na ganin cewa hakan na da nasaba da ƙarin karyewar darajar nairar. CBN ya ce za a fara amfani da sabbin takardun kuɗin daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.

By Editor