Gwamna Wike ya naɗa masu ba shi shawara 100,000 cikin sa’o’i 24

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya ƙaddamar da masu ba da shawara na musamman sama da 100,000 kan harkokin siyasa a jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wani sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafin sada zumuntansa a ranar Alhamis, 3 ga Nuwamba, 2022.

Gwamnan ya rubuta cewa, “a yau na ƙaddamar da kashin farko na mataimaka na musamman 100,000 kan harkokin siyasa na yankin Kudu maso Gabas da Ribas.

Wannan dai shi ne karo na farko da wata gwamnatin Jiha ta naɗa irin waɗannan lambobi a Nijeriya duk da cewa ana maganar zaɓe ne.

Idan dai za a iya tunawa, a baya gwamnan ya bayyana naɗin mataimaka na musamman ga sassan siyasa 28,000, da kuma masu ba da shawara na musamman ga sassan siyasa 14,000 da kuma jami’an hulɗa da unguwanni 319.

Da ya ke kare lamarin a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a ranar 14 ga watan Oktoba, gwamnan ya ce zai ƙara yawan mataimakansa na musamman zuwa 100,000.

Wike ya ce, yana daga cikin alƙawarin da gwamnatinsa ta ɗauka na rage raɗaɗin talauci tare da ƙarfafawa matasa gwiwa.

By Editor