Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An ceto mutane 37, wasu biyu kuma sun samu raunuka yayin da ake fargabar wasu da dama sun maƙale a lokacin da wani gini ya rufta a titin Legas da ke unguwar Garki a Abuja.
Jaridar Blueprint Manhaja ta tattaro cewa Kakakin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Tarayya (FEMA) Nkechi Isa ta tabbatar da faruwar lamarin da safiyar ranar Alhamis.
“Ana ci gaba da aikin ceto yayin da ake ci gaba da neman ƙarin waɗanda abin ya shafa a wurin da ginin ya rufta a titin Legas, a ƙauyen Garki daura da ofishin ‘yan sanda na Garki a babban birnin tarayya Abuja,” inji ta.
“Tawagar haɗakar Hukumar bada agajin gaggawa ta FCT (FEMA), da Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta Tarayya, (FRSC), da kuma Rundunar ‘yan sanda ta FCT, da VIO suna nan a wurin domin gudanar da aikin ceto.
“Gini mai hawa biyu wanda ke ɗauke da mazauna da masu kasuwanci ya ruguje ne a daren ranar Laraba.
“An ceto mutane 37 da ransu, yayin da wasu 2 suka samu munanan raunuka.”
A cewarta, tawagar bincike da ceto ta hukumar na jiran masu aikin tono don ƙara tsananta bincike tare da tabbatar da cewa babu wanda ya mutu a cikin baraguzan ginin.
A nashi ɓangaren, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayar da umarnin kama mamallakin ginin mai hawa biyu.
Wike, ya bada umarnin ne a lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru jiya Alhamis, ya kuma buƙaci babban sakatare na hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, Adesola Olusade, da ya biya kuɗaɗen jinyar waɗanda ke kwance a asibiti.
Ministan ya kuma buƙaci ma’aikatar kula da ci gaban ƙasa, FCTA da ta gaggauta samar da matsuguni da abin ya shafa a yankin.
Ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su haɗa kai da jami’an gwamnati domin amfanin kowa.
“Wannan shi ne abin da muke magana a kai lokacin da mutane ke gina gidaje ba tare da bin ƙa’ida ba.
“Wannan ne ya sa ake tsara birane, don daqile irin wannan lamari.
“Ina jajenta wa waɗanda suka rasa rayukansu yayin da za a biya kuɗaɗen jinyar waɗanda ke asibitoci nan take,” inji shi.
Rushewar gini dai abu ne da ya zama ruwan dare a wasu garuruwan Nijeriya.
A watan da ya gabata, wani gini mai hawa huɗu ya ruguje a unguwar Life Camp da ke birnin tare da jikkata da dama. Hakan ya faru ne yayin da ma’aikata ke aikin ginin a unguwar Dape kusa da asibitin Berger.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa yin aiki mara kyau, rashin ingancin kayan aiki, da cin hanci da rashawa don kaucewa sa ido a hukumance galibi ana zarginsu da haddasa iftila’in rushewar gini a Nijeriya.