Daga USMAN KAROFI
Ministan birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo kan lafiyarsa, yana mai cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana aiwatar da ayyukansa ba tare da wata matsala ba.
A wata tattaunawa da manema labarai, Wike ya musanta rahotannin da ke cewa an garzaya da shi Landan don neman magani a makon da ya gabata. Ya ce lafiyarsa tana nan daram, kuma hakan ne ke ba shi damar gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Hadiminsa, Lere Olayinka, ya kuma yi watsi da labaran da ake bazawa, yana mai cewa babu wata hujja da ke nuna cewa an kai ministan Landan don jinya. Ya ƙara da cewa Wike ya kasance a Abuja a ranar Juma’a, inda ya kai ziyara wurare da dama a FCT.
Wike ya bayyana cewa yana mai da hankali kan aikinsa, kuma ba zai bari raɗe-raɗin da ba su da tushe su hana shi aiwatar da ayyukansa ba. Ya buƙaci al’umma su guji yaɗa jita-jita marasa tushe da wata manufa ta siyasa.
