Ya aika budurwarsa lahira kan ragargaza masa wayar iPhone

Spread the love

Saurayin mai suna Godspower Adigheti ɗan shekara 23 ya kashe budurwarsa mai suna Gift Ojoku, inda ya aikata hakan saboda tsananin fusata da kuma kishi.

Rahotanni sun rawaito cewa, fusataccen saurayin ya halaka masoyiyar tasa, wadda ta kasance ɗaliba a makarantar koyon Fasaha da ke jihar Delta. Kuma ta tarwatsa wayar tasa ne mai ƙirar iPhone 13 pro max.

Wannan tashin-tashina ta faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata. Wata majiya ta shaida mana cewa, soyayya ta yi nisa tsakanin waɗannan masoya guda 2, domin kuwa akwai ƙaruwar ’ya a tsakaninsu.

An dai ce rigimar ta fara ne bayan budurwar ta dawo gida daga wani wuri, sai ya tambaye ta cewa daga ita ta ke? Daga nan ne fa sai cacar baki ta ɓarke, wadda ta juye ta zama gagarumar rigima.

Ana cikin haka ne sai budurwar ta ɗauki wayarsa mai tsada, ƙirar iPhone 13 pro max, ta tarwatsa ta. Daga nan shi kuma cikin fushi ya ɗauki gatari ya sassara ta kamar itace, har sai da ya aika ta lahira.

Bright Edafe, wanda shi ne kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Delta, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai.

By Editor