Cikin watanni uku an haifi yara sama da 27,000 a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa cikin watanni uku an haifi jarirai 27,490 a faɗin jihar.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, babban daraktan hukumar da ke kula da asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Nasiru Alhasan Kabo, ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke ƙaddamar da shirin rarraba kayan kula da lafiya ga asibitocin kula da lafiya na matakin farko da na biyu da kuma na uku.

Dakta Nasiru ya ce, kayan da aka raba da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 15 na haihuwa ne da kayan bayar da na sashen kula da bayar da agajin gaggawa da na kula da yara.

Ya ƙara da cewa, a cikin adadin, an yi tiyata ga mata masu ciki guda 681(CS), kuma irin magungunan da ake bayarwa suna taimakawa.

Sannan ya jinjinaw a abokan hulɗa saboda taimakon da su ke bai wa harkar lafiya a jihar.

Bugu da ƙari ya buƙaci ƙungiyoyin fararen hula da su ci gaba da tallafa wa ɓangaren lafiya.