Ya gwammace zama a kurkuku da zama da matarsa

Wani magidanci mai shekaru 30 a duniya ya bayyana cewa, ya gaji da rigimar matarsa, inda ya roƙi jami’an ’yan sanda da su tsare shi.

A cewarsa, sam ba zai iya ci gaba da kasancewa tare da matar ta sa ba saboda irin tada masa da hankali da ta ke yi da fitinarta a kullum, inda ya ce, gara masa zaman gidan kurkuku.

Ya ce, “Ina son tafiya gidan kurkuku, domin ba zan iya ci gaba da jure halin matata ba.”

Mutumin ɗan ƙasar Albaniya wanda ya fito daga Guidonia, wani gari a wajen birnin Rome ya shafe tsawon watanni da dama tsare a gida kan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi. Kuma ya rage masa shekaru da dama kafin ya kammala hukuncin ɗaurin da aka masa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ta rahoto.

A ranar 23 ga watan Oktoba, ya je ofishin ’yan sanda na Tanenza Carabinieri da ke garin Guidonia domin roƙonsu a kan su jefa shi a gidan kurkuku saboda ba zai iya ci gaba da hukuncin ɗaurin da aka yi masa a gida ɗaya da matarsa ba.
Matashin ya faɗa wa ’yan sanda cewa, “ku kama ni, ba zan iya jure zama gida ɗaya da matata ba, kuma na gwammaci zaman kurkuku.”

A cewarsa, matarsa tana da fitina sosai ta yadda kullum sai sun yi faɗa, lamarin da yasa ya gwammaci zaman kurkuku fiye da gidansa kenan.
An nakalto Kyaftin Francesco Giacomo Ferrantte na Tivoli Carabinieri yana cewa, “yana zama a gida tare da matarsa da iyalinsa. Abubuwa sun daina tafiya daidai.”

Ya ce, “rayuwar gidana ya zama tamkar a wuta, ba zan iya ba, Ina son tafiya kurkuku.”

Bayan roƙon da magidancin ya yi, sai Carabinieri ya sanar da hukumar shari’a sannan aka mayar da shi gidan yari kan karya dokar tsare sa da aka yi a gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *