Ya kamata ƙasashen Larabawa su ɗauki darasi daga Ƙasar Sin, su daina biye wa ƙasashen yamma

Daga FA’IZA MUHAMMAD MUSTAPHA

Rahoton Arab Barometer da kafar yaɗa labarai ta BBC ta wallafa a baya bayan nan, ya ce ƙasashen Larabawa sun yanke kauna da tsarin demokuraɗiyyar ƙasashen yammacin duniya, saboda yadda tattalin arzikinsu ya yi rauni a ƙarƙashin tsarin.

Wannan rahoto ya tuna min da ziyarar da shugaban Amurka zai kai yankin gabas ta tsakiya a cikin wannan mako, wadda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci ga tsaron ƙasarsa da kuma neman nasara a takararta da Sin.

Amurka ta gaza gane cewa, kan al’umma ya waye, babu wanda ke buƙatar danniya da fifiko irin nata da kuma katsaladan da take yi cikin harkokin da ba su shafe ta ba. Ƙasashen sun ba ta dama, kuma sun ga aikin hannunta, sun ga yadda ta ingiza yake-yake ko ma kaddamar da yake-yake da tashin hankali a yankin.

Don haka, dukkan ƙasashe masu tasowa sun fahimci cewa, Amurka ita kanta kaɗai ta sani, ba ta damu da sauran ƙasashe ba.

A daya ɓangaren, a matsayinta na ƙasa mai tasowa, an ga yadda ƙasar Sin ke kiyaye cikakken ’yancin ƙasa da ƙasa da martabawa da mutunta su. An ga kuma irin jajircewarta wajen kyautata dangantakar moriyar juna da hadin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Kana ta zama misali na ƙasar da ta samu ci gaba na a zo a gani, bisa dabarun da ta ɗauka bisa la’akari da yanayinta, ba wai koyi da wata ƙasar yamma ba. Don haka, ƙasar Sin ta zama abun koyi a fannin tsarin demokraɗiyya da ci gaba.

Abun da ya kamata ƙasashen gabas ta tsakiyar su yi a yanzu shi ne, ɗaukar darasi daga Sin, su tsara yanayin demokraɗiyyarsu ta hanyar da ta dace da muradu da moriyar al’ummominsu domin samun ci gaban da suke muradi. Su kaɗai suke san yanayin da suke ciki da abun da ya fi dacewa da su, don haka su kaɗai ne za su iya magance matsalolinsu ba wai biyewa Amurka da ƙawayenta ba.

Ita kuma Amurka, kamata ya yi ta fahimci cewa, ba takara ya kamata ta yi da Sin ba, domin ba za ta ci nasara ba. Abun da ya kamata ta yi shi ne, haɗa hannu da ƙasar Sin a matsayinsu na manyan ƙasashe, domin samun moriyar juna da tallafawa tabbatar zaman lafiya a duniya da bunƙasa tattalin arzikinta da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai ɗaya a duniya.

Fa’iza Muhammad Mustapha