A kiyaye amfani da addini don son zuciya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Nijeriya na daga cikin ƙasashen duniya na sahun farko da jama’ar ƙasar ta ke da son addini. Wata majiyar ma na cewa, Nijeriya ce ƙasar da mutanen ta ke da tsananin son al’amarin addini. Komai na ‘yan Nijeriya sai ka samu addini a ciki, ko da kuwa a sautin ƙarar waya ne, sai ka fahimci ƙarar wayar Musulmi da ta wanda ba Musulmi ba. Muna nuna son junan mu saboda addini, mu taimaki bare saboda addini, mu gujewa ɗan uwa saboda addini. Akwai masu addini na tsakani da Allah, akwai ‘yan na gada, ‘yan son zuciya da kwaɗayin samun ɗaukaka ko wani matsayi na ƙungiya ko na ɗariƙa, a masallaci ko a majami’a.

Saboda kishin addini irin na ‘yan Nijeriya suna juya duk wani al’amari na addini yadda zai dace da son zuciyarsu, ko da kuwa hakan zai sa wani ya rasa ransa, ko a yi asarar zumunci da tsohuwar alaƙa ta zaman tare. Ɗan Nijeriya ba ya saurarawa kowa in dai a kan addini ne, daga kowanne ɓangare na Musulmi ko Kirista. Shi ya sa a duk lokacin da aka samu wata rashin jituwa a tsakanin mabiya waɗannan manyan addinai biyu ɓarnar da ake yi tana da yawa. Kowanne ɓangare na zargin ɗan uwansa da rashin tauye haƙƙin, danniya ko mamaya.

Babu inda abin zai fi baka mamaki sai idan siyasa ta kunno kai, nan ne kowanne ruɓaɓɓen ɗan siyasa da ya daɗe ba bai yi sallah ko ya je ibada a majami’arsa ba. Amma daga lokacin da ya ga wani abokin takarar shi da ya ke daga wani addinin to, sai a lokacin kishin addinin sa zai tashi. Ya koma cikin jama’ar sa yana ba su kuɗi da shirya musu maganganu na tunzurawa don dai ya samu goyon bayan su. Ko da kuwa wancan ɗaya abokin adawar tasa shi ma abokin cin mushensa ne, wato ma’ana tare suke harkokin su na nishaɗi, ba tare da tunanin addinin wani ba.

Ina ta wannan bugun iska ne, don in nuna muku yadda ‘yan Nijeriya suka mayar da addini ya zama matakalar cimma burisu. Wasu ‘yan Nijeriya sun zama masu yi wa addini fuska biyu, suna munafurtar abokan hulɗa da mabiya, alhalin wani abin ba don Allah ake yi ba. Tsantsar son zuciya ce kawai!

Duk da yadda sunan Nijeriya ya yi fice a duniya, saboda son addini da kiyaye koyarwar littafin Allah, amma da mamaki a ce kuma ƙasar ce ta biyu a yankin Afirka ta Yamma bayan ƙasar Guinea Bissau, wajen cin hanci da rashawa. Mutanen Allah masu kishin addini, amma kuma gurvatattu a ɗabi’a, anya son addinin mu na gaskiya ne? Mai ya sa tsarkin zuciyar mu ba zai gyara ayyukan mu da mu’amalar mu ba ne?

A yayin nake wannan rubutu kimanin Musulmi ‘yan Nijeriya dubu 43 ne suke ƙasa mai tsarki, don gudanar da aikin Hajjin Bana a Saudiyya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Musulmi masu yawan mahajjata. Yayin da hukumomi a Nijeriya ke bayyana cewa, maziyartan Kirista masu zuwa ƙasar Isra’ila ziyarar ibada sun kai har dubu 10, a wannan shekarar kawai. Wannan yana ƙara tabbatar da yadda ‘yan Nijeriya ke sadaukar da rayuwarsu da dukiyarsu ga aikin addini, yayin da suke murna da farin ciki.

Amma sakamakon yadda wasu ke sanya son zuciya suna aikata wasu abubuwa da ke ɓata sunan addini, ko sanya ƙyamar addini a zukatan wasu da ke ganin addini ne ya ke sa wasu aikata ɓarna da ta’addanci. Sai dai babu wani mai aiki da hankali da nazari kan addini da rayuwa da zai yarda cewa, addini yana sa mutane aikata ba daidai ba, sai su mutanen su aikata rashin gaskiya da sunan addini.

Dubi misalin yadda ‘yan ta’adda suke aikata varna iri iri, da ya haɗa da kisan gilla, sace mutane da bautar da su, lalata dukiya, da wuraren ibada, sanya yara cikin ƙuncin rayuwa da tilasta musu ɗaukar makamai. Waɗannan duk abubuwa ne na ƙyama da wasu baragurbi suke aikatawa da sunan kare addini ko aiki da koyarwar addini.

Miliyoyin dukiya da dubbannin rayukan ‘yan Nijeriya sun salwata saboda jahilci da son zuciyar wasu, har ma da rashin lafiyar ƙwaƙwalwar wasu.

Amfani da sunan addini ana tauye haƙƙoƙin iyali, ko sanya talakawa suna cire ɗan abin da suka samu daga ƙwadagon da suke yi suna arzuta wasu cima zaune da sunan aikin Allah, duk saɓa wa koyarwar addini ne. Wannan bai taƙaita ga wani addini guda ɗaya ba, daga kowanne addini da kowacce al’umma ana samun ɓatagarin da ke aikata abubuwan da ba su dace ba, suna fakewa a cikin rigar addini.

Ba da jimawa ba wasu rahotanni daga Jihar Filato da Jihar Ondo suka bayyana wani aiki da jami’an tsaro suka gudanar na gano wasu yara almajirai da aka sato daga Jihar Gombe zuwa wani gida a Jos, inda aka killace su ana koya musu addinin Kirista, duk kuwa da kasancewar yaran Musulmi ne, kuma ba bisa son ransu ko na iyayensu aka kai su gidan ba. A Jihar Ondo ma wasu yara ne da adadinsu ya kai kimanin fiye da 50 aka gano a ƙasan ginin wata majami’a, inda bincike ya gano an raba yaran da iyayensu ne don a tarbiyyar da su kan wata sabuwar hanyar koyarwar addinin Kirista da babban jagoran majami’ar ya ce an yi masa wahayi a kai. Ko da ya ke jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake cigaba da tsare babban malamin addinin.

Sai dai abin da zai ba ka mamaki shi ne yadda wasu daga cikin mabiyan majami’ar suka yi dafifi a ofishin ‘yan sanda na yankin da abin ya faru suna buƙatar a sako musu jagoran su, wanda suka yi imanin aikin Allah ya ke yi, kuma da amincewar su suka ba da yaran nasu. Ko da ya ke wasu iyayen sun yi ƙorafin malamin addinin yana rinjayar ƙwalwalwar yaran ne, inda ya ke sa su gudu daga gidajen iyayensu su koma zaman coci.

Wannan ya tuna min labarin wani malamin addini a ƙasar Amurka da ya rinjayi wasu mabiyansa su 909 a shekarar 1978, waɗanda ya sa suka sha guba suka mutu gaba ɗayansu, don kwaɗayin tafiya mulkin sama. Wannan na daga cikin mafi takaicin abubuwa da suka faru a tarihin duniya, da aka aikata da sunan addini.

Ba za mu manta da yadda a shekarun baya aka riƙa samun wasu ‘yan ta’adda suna ɗaura abubuwan fashewa a jikinsu ko a jikin wasu yara mata don su shiga cikin jama’a su tayar da bam, domin tarwatsa rayukan dubban jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba. Duk da sunan in sun yi haka za su samu shahada su je wajen Allah ya sa su a Aljanna.

Lallai ne ‘yan Nijeriya su tashi tsaye su kare mutuncin su da ake gani a matsayin su na masu son addini da kiyaye dokokin ubangiji, su riƙa tantance irin mutanen da ake bari suna jagorantar mutane da sunan harkar addini, don kaucewa faɗawa hannun ɓatagari, waɗanda ba addinin ne a ransu ba, sai son zuciyarsu. Wasu kuma jahilci da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ne ke sa su aikata wasu abubuwan da ke sa a riƙa zargin masu addini cikin ban gaskiya, da tsoron Allah.

Ya kamata kafin a amincewa malamin addini damar yin wa’azi lallai a duba lafiyar ƙwaƙwalwarsa da ingancin iliminsa da inda ya samu tarbiyya, domin kada a bar shi ya ja mutane ga halaka ko rabuwar kai a tsakanin mabiya.

A riƙa sa ido a majami’u da makarantun Islamiyya na ƙauyuka da lunguna kan yadda suke gudanar da karantarwarsu da harkokin su na addini, domin ɗaukar mataki kan duk wasu ɓata gari da za su cutar da al’umma, saboda wasu dalilai na jahilci da rashin samun kyakkyawar tarbiyyar addini.

Addini babban al’amari ne da ke taɓa zuciyar kowanne ɗan Nijeriya, don haka mu yi masa riƙon girma da mutunci.