Tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, wai waye yake ƙoƙarin kawo wa ɗalibai cikas?

Daga NAFI’U SALISU 

Yajin aikin Malaman Jami’o’i ba sabon abu ba ne a Nijeriya, musamman a lokacin da ɗalibai ke ƙoƙarin kammala zangon karatu, ko kuma lokacin da ya kamata a ce sun kama karatun ka’in-da-na’in.

Wannan wani al’amari ne da faruwarsa kan sosa rayuka da dama, a ciki har da na iyayen ɗaliban da ‘ya’yansu dake karatu a Jami’a. Hakazalika, a duk lokacin da aka ce Malaman Jami’o’i suna yajin aiki, a kan daɗe ana kai ruwa rana tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya, wanda kuma daga bisani a kan samu maslaha a ɗinke bakin zaren domin ɗalibai su dawo makarantu su ci gaba da karatu.

To, sai dai yajin aikin na wannan lokacin za a iya cewa ya sha bamban da sauran yajin aikin da Malaman Jami’o’in kan yi, wanda ba ya wuce na ‘yan watanni kaɗan ko satittika. Ba kamar wannan da a yanzu ya doshe watanni tara ba, wanda sakamakon sa ya jefa ɗalibai da dama a cikin mawuyacin halin rashin sanin ya ya al’amurran karatunsu zai kasance?

A cikin irin waɗannan ɗalibai akwai waɗanda suke gab! Da kammala karatunsu a Jami’a, yayin da wasu kuma sabbin shigowa ne ba su daɗe da fara ɗaukar darasi ba. Kuma a kan kashe kuɗi da yawa kafin a fara karatu a kowacce irin Jami’a a ƙasar nan. To sai ga dukkan alamu Gwamnati da ita ƙungiyar Malaman Jami’o’in basu yi la’akari da yadda ‘ya’yan talakawa suke yin fafutaka da faɗi-tashi wajen samun gurbin karatu a jami’o’i ba.

A cikin binciken da na yi kafin na fara wannan rubutu, akwai abubuwa da dama da na binciko waɗanda su ne dalilan da ya sa su ASUU suka tafi wannan yajin aiki wanda za a iya kiransa da (Sai baba ta gani), wato dai ba a san ranar dawowar su ba. Daga cikin dalilan Malaman akwai rashin biyan haƙƙoƙinsu nasu na ƙashin kansu wanda ya rataya a wuyan Gwamnati, wanda a kan ɗauki tsawon lokaci ba a yi, yayin da hakan ke jefa Malaman cikin taskun rayuwa da ƙa-ƙa-nika-yi. Sannan alawus-alawus (allowance) nasu Gwamnati bata biyansu, ballantana kuma ta inganta albashinsu duba da irin wahalhalun da suke sha wajen koyar da ɗalibai a jami’o’i.

Akwai wani abu da na lura da shi, wanda kusan shi ne ya fi ci wa su malaman tuwo a ƙwarya, wato adadin ɗaliban da kowanne malami zai koyar da shi. A kowanne aji a bisa doka Malami zai koyar da ɗalibai (25) da biyar ne kawai, to amma wani ajin sai a sami sama da ɗalibi ɗari, ko ɗalibi ɗari biyu ko a dubu kuma Malami ɗaya ne yake koyar da su, wanda kuma hakan ya sava wa doka.

To amma saboda kowa ya samu ya yi karatun shi ya sa malaman suke daurewa su yi haƙuri su ɗauki nauyin a kansu, ba tare da yin la’akari da ɗan albashinsu da suke samu daga Gwamnati ba, wanda idan suka ce za su tsaya a iya koyar da ɗalibai (25) a cikin kowanne aji, to ɗalibai da dama sai dai su haƙura da yin wannan karatu.

Baya ga haka, akwai kuɗaɗe waɗanda Gwamnati ta ware a ke bai wa kowacce jami’a domin gudanar da karatu da sauran abubuwa da suka danganci kula da Makaranta, wanda a cikin kuɗin da ake baiwa kowacce Jami’a don tafiyar da ita salin-alin, kuɗi ne da idan aka yi lissafi dalla-dalla basa iya tafiyar da dukkan wasu al’amura na gudanarwa a jami’o’in, to amma bisa jagorancin ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sukan lallava kuɗaɗen da Gwamnati ke ba su, tare da yin haƙuri da wasu buƙatunsu domin tafiyar da al’amuran karatu da sauran abubuwan da suka shafi gyare-gyare, samar da wuta a cikin makaranta, kula da wuraren kwanan ɗalibai (Hostel), ruwan sha, man inji janareto, tsaro na makaranta, masu share-share, littattafan karatu da sauran abubuwa da dama.

Dukkan waɗannan abubuwa da suke faruwa Gwamnati ta san da su, ta kuma san irin matsalolin da jami’o’in ƙasar nan (musamman na yankin Arewa) suke ciki, wanda sai ɗan talaka yayi da gaske yake samun gurbin karatu a Jami’a, sannan idan ya samu ɗin ma kafin ya gama sai ya ji a jikinsa.

Bayan ya gama kuma samun aikin yin ma abu ne mai zaman kansa, wanda shi ma wani ƙaramin yaqi ne wanda sai mutum ya kai gwauro ya kai mari yake iya samu. Don haka, duk wancan ƙoƙari da malaman jami’a suke yi na haƙura da ɗan albashin da ake ba su da bai taka kara ya karya ba, da kuma tarin yawan ɗaliban da suke koyarwa ba tare da la’akari da cewar mutum (25) ne dokarsu ta ce kowanne  malami ya koyar, to amma idan an yi hakan wasu ba za su sami damar yin karatun ba, shi ya sa Malaman suka haƙura suke ɗaukar nauyin duk da ya yi musu yawa.

Sannan kusan Malaman za ka same su sai sun yi wata ‘yar buga-buga ta harkokin samun kuɗi wajen tafiyar da al’amuran gidajensu da iyalansu, domin idan suka ce za su dogara da albashinsu, to hakan kan zamo ƙalubalen rayuwa a gare su.

Ba tare da yin la’akari da waɗancan matsaloli ba, Gwamnati ta yunƙuro ta rage kuɗin da ake baiwa Jami’o’i, sannan kuma kayayyakin gudanar da karatu suka yi tsadar gaske, ga man fetur da gas shi ma ya yi tashin gwauron zabi. Ita kuma makaranta tana buƙatar wuta dole, ruwan sha, kayan karatu, titina, gyaran ɗakunan kwana da na karatu da sauran abubuwa.

Idan babu wadatacciyar wuta a cikin makaranta ta yaya ɗalibi zai iya shiga ɗakin karatu (Library) ya yi karatu? Haka nan idan babu wuta a cikin makaranta, ya ɗalibi zai yi rubutu ko karatu a wayarsa ko na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer).

Don haka, hatta waɗanda suke da wuraren aikin Computer na kuɗi (Business Center) a cikin makarantun jami’a da wasunsu, dole ne su ƙara kuɗin buga takardu da sauransu. Kuma dole ne sai ɗalibi ya yi wannan, dole ne ya sayi ‘handout’ ya yi karatu, dole ya sayi littafi ya yi karatu, dole yana buƙatar wuta, yana buƙatar ruwa, yana buƙatar kayayyaki da dama.

To duk idan ka tattara waɗannan abubuwan, sai Gwamnati take so jami’o’i su tsaya da ƙafafunsu (a cewarta) su gudanar da al’amurran karatu su tafi dai-dai, bayan babu isasshen kuɗi, babu wutar lantarki, babu wadatattun ɗakunan karatu da ɗakunan kwana da kayan karatu, ga ma’aikata waɗanda ake biyan su albashi tun daga masu shara, masu gadi, masu kula da tsaftar banɗakuna dakunan ɗalibai da sauransu.

Don haka, ta ina jami’a za ta samu kuɗin gudanar da dukkan waɗannan abubuwan? Domin wasu malaman a kan tura su wasu jami’o’in na wasu garuruwan, shin malami da kuɗin aljihunsa zai je wata jami’ar ya koyar don kawai yana son a yi karatu ko kuwa gwamnati ce ya kamata ta kula da wannan a aljihunta? Sannan idan har aka ce jami’o’i su fito da waɗannan kuɗaɗen, shin a jikin ɗalibai ‘ya’yan talakawa za su tatso kuɗaɗen? Wannan abin dubawa ne.

To, ire-iren waɗannan abubuwan da dama su ne suka sa (ASSU) suke ganin Gwamnati ba ta shirya bai wa ‘yan qasa ingantaccen ilimi ba, domin idan da da gaske Gwamnati take yi, to da ta duba dukkan buƙatun Malaman Jami’o’i da abinda ya kamata a yi wa jami’o’in domin a inganta harkar ilimi, ta yadda ‘yan ƙasa za su yi karatu cikin salama ba tare da jinin jikinsu ya wahaltu ba, har su fara yanke tsammani da karatu. 

Idan aka ce an bar komai na gudanarwa a hannun jami’o’in ƙasar nan, su za su samar da kuɗin tafiyar da su na komai da komai, to babu wani ɗan ƙasar nan (musamman ‘ya’yan talakawa) da za su iya yin karatu a Jami’a, domin abinda za su biya tun daga kuɗin yin rijista, wallahi sai dai su haƙura da karatun bakiɗaya.

Haka kuma idan malaman jami’o’i suka ɗauki ɗalibi (25) kowanne aji, to sai dai sauran ɗalibai su haƙura da karatu. Don haka wannan babban al’amari ne da ya kamata Gwamnati ta yi duba a kai, ta kuma ɗauki hanyar gyara domin dawo da martabar Jami’o’in ƙasar nan matuƙar ana son ‘yan ƙasa su yi karatu, kuma ba tare da an bautar da malamai ba, domin abinda ake yi musu ya yi kama da bautarwa.

Ba zai yiwu a ce idan ɗan Nijeriya yana muradin yin karatu a cikin kwanciyar hankali don ya samu ingantaccen ilimi sai ya bar ƙasarsa ya tafi wata ƙasa ba. Kowanne irin arziki ne a duniya Allah (Subhanahu wata’ala) ya yi masa shi a wannan ƙasa tamu Nijeriya. Baya ga haka muna da ƙwararrun Malamai waɗanda suka san me suke yi.

Muna da haziƙai a cikin ƙasar nan, kuma duk wani abu na inganta ilimi idan gwamnati taso za ta iya yin sa ba tare da vata lokaci ba. Amma abinda na lura da shi kawai shi ne, gwamnati ta iya ciwo bashi don gyara hanyar Jirgin ƙasa ko samar da sabuwa, amma kuma hakan bai hana a tare jirgin a yi garkuwa da mutanen ciki ba. Kullum ana magana a kan siyo makaman yaƙi don yaƙar ‘yan ta’adda, amma shi ilimi ana ta yi masa ta’addanci an ƙi a yi masa gata.

Duk wasu kuɗi da ake kamfata a ce za ayi noman shinkafa, za a yi noman kaza da kaza, za gyara matatun man fetur, za a yi, za a yi da ta ƙi ƙarewa kuma yin ya zama tatsuniya, duk ba su kai inganta ilimi ba, domin shi ilimi shi ne ginshiƙin rayuwar bakiɗaya.

Don haka, idan har gwamnatin Tarayya tana son ‘yan ƙasa su samu ingantaccen ilimi, ta lallai ta tabbatar an kawo ƙarshen wannan yajin aikin da Malaman Jami’o’i suke yi, a kuma biya wa Malamai buƙatunsu ta yadda za su dawo su ci gaba da ba wa al’umma ilimi. 

Sannan ina kira ga ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su dubi halin da ɗalibai suke ciki, su kuma dubi halin da ƙasar take ciki a fannin ilimi, matuƙar fa aka cigaba da yin yajin aiki irin haka, to lallai ilimi zai mutu murus a Nijeriya. Kuma ina kira da lallai (ASSU) ku fito ku shelanta wa Duniya halin da ku ke ciki dangane da dalilan da ya sa kuke wannan yajin aiki, don kar mutane su riƙa yi muku kallon rijiya ta bada ruwa, guga ta hana.

Ma’ana, kar a riƙa yi muku kallon Gwamnati ta yi muku duk abinda kuke so, amma ku ne ku ke da wasu buƙatu da ku ke son a biya muku su haka kawai kuma ba su zama dole ba. Idan ku ka fito ku ka faɗa duniya ta ji halin da ku ke ciki, to hatta al’ummar gari za su taya ku yaƙin neman haƙƙinku.

Amma muddin kuka ja bakinku kuka yi shiru, sai ku da gwamnati da ɗalibai ne kaɗai kuka san halin da ake ciki, to lallai mutane za su cigaba da yi muku kallon waɗanda suke yaƙi da buqatunku kaɗai ba yaƙi da dawo da martabar ilimi ba, ta yadda ‘yan ƙasa za mu same shi a cikin sauƙi ba.

Sannan Gwamnatin Tarayya ke ma idan da gaske kuna kishin ‘yan ƙasa, kuna fatan su sami ilimi, to ku sasanta tsakaninku da ASUU, ku biya musu haƙƙoƙinsu na baya da suke bin ku da kuma waɗanda ba a biya musu ba a yanzu. Wannan yajin aikin ba zai taɓa haifar ɗa mai ido ba, kuma kullum zai ci baya ne maimakon gaba.

Domin yanzu wani ɗalibin koda an dawo an ci gaba da karatu, to fa zai tsinci kansa ne tamkar sabon zuwa koda tsohon ɗalibi ne. Dalili kuwa shi ne, dogon lokacin da aka ɗauka ba a karatu ya sa ya manta abubuwa, domin a wannan Gwamnatin hatta ƙaramin yaron da mahaifiyarsa take goyonsa yana ji a jikinsa, domin ba kowa ne yake iya samun abinda zai saka a cikinsa sau uku a kullum.

Don haka matuƙar gwamnati bata yi wani abu a kai ba, to mun tabbatar da cewa bata son ‘yan qasa suyi ilimi, kuma ta tabbata wannan gwamnatin ba ta kishin ilimin baki ɗaya.

Nafi’u Salisu
Marubuci/Manazarci,
[email protected],
[email protected],
08038981211