Har da kawuna a waɗanda suka nemi gurɓata min rayuwa – Aisha Kallari

“Mata ku cire kunya, ku sanar da iyayenku idan aka ci zarafinku”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Duk da yake ana ɗaukar jinsin mata a matsayin mutane masu rauni, wato raunin jiki da na zuciya, amma ba duk mace ce ta ke da wannan raunin ba. Wasu matan Allah ya ba su zafin nama, kaifin ƙwaƙwalwa, hangen nesa, da ƙarfin zuciya. Suna iya tunkarar kowacce matsala kuma su yi nasarar kawar da ita. Matan da ake cin zarafin su tun suna ƙanana ko wulaƙanta rayuwarsu ta wasu hanyoyi daban daban, sukan fuskanci ƙalubale mai yawa a rayuwarsu, wanda yake jirkita mu su rayuwa na wani lokaci ko ma dai gabaɗaya rayuwarsu ta zama abin tausayi. Aisha Hamza Kallari, wata matashiya ce da ke zaune a Jos babban birnin Jihar Filato, wacce ta yi fama da ƙalubalen rayuwa iri iri, amma saboda ƙwarin gwiwa da taimakon ƙwararru da ta ke samu, rayuwarta ta zama abin misali ga sauran ýan mata da ke rayuwa cikin ƙunci da fargaba. Wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya samu ganawa da wannan matashiya, da ta kasance ma’aikaciyar jinya, marubuciya, mai kishin kare haƙƙin mata da ƙananan yara. 

MANHAJA: Ki fara gabatar mana da kanki. 
AISHA: Sunana Aisha Hamza Kallari. Na yi makarantar firamare da sakandire a makarantar Asasul Islam da ke Masallacin Idi a cikin garin Jos. Na kuma yi karatu a kwalejin koyar aikin jinya da ke makarantar Islamiyya Pilot Science a titin Bauchi duk a cikin garin Jos. Yanzu haka kuma ina karatun digirina ta hanyar yanar gizo a Jami’ar ƙasa da ƙasa ta International Open University wato IOU, ina karanta ilimin halayyar ɗan Adam, ma’ana Psychology. 

Yaya rayuwarki ta kasance lokacin tasowarki?
Rayuwata ta kasance cike da ƙalubale masu tarin yawa wanda na fuskanta, daga ɓangarori daban daban, kamar daga gida, makaranta da kuma al’umma bakiɗaya. Amma babu babban ƙalubale kamar tasowar kanta, na fuskanci abubuwa iri iri da sauya min tunanina, burina da ma duk wani abu da ya shafi rayuwata. Na haɗu da azzaluman maza waɗanda suka canja mafarkina a ciki har da wani kawuna da ɗan’uwana a cin zarafi na. Na shiga mummunar damuwa da tashin hankali ganin yadda suka riƙa nemana da lalata. 

Yaya ki ka iya samun ƙwarin gwiwar iya tunkarar waɗannan ƙalubalen? 
A lokacin da matsalolina suka fara yin yawa, sai makusantana, kamar ‘yan’uwa da abokan arziƙi suka dage akan cewa na yi haƙuri da abubuwan da suke faruwa, jarrabawa ce ta rayuwa, kuma kowa da yadda yake samun nasa ƙalubalen rayuwar. Duk da yake na lura suna ƙoƙarin nuna min in koyi dauriya ne da kuma riƙe sirrina da kare mutuncin gidanmu. 

Ta yaya abubuwan da suke faruwa da rayuwarki suka canza yadda ki ke hulɗa da mutane?
A lokacin da na fara samun waɗannan matsalolin rayuwa, abubuwa da dama sun dagule mini, na kasa samun yarda da mutane, na kuma zama mai tsargar kowanne namiji da ya zo kusa da ni, har ýan’uwana na jini. Rayuwata ta cika da tsoro da fargaba, na samu kaina ina tsargar irin rayuwar da nake ciki. Amma alhamdulillahi, sanadiyyar shawarwari da ƙarfafa gwiwa da na ke samu daga wasu ýan’uwa da mutanen arziƙi a hankali a hankali na samu natsuwa a zuciyata, na kuma yi ƙoƙari na cire dukkan wasu mutane marasa amfani a cikin rayuwata. 

Idan a ce za a ba ki damar mayar da hannun agogo baya ki canza wasu abubuwa na rayuwarki, waɗanne za ki so ki canza su?
Zan so a ce na koma yarinya ƙarama, wacce ba ta san duk wani ƙalubale na rayuwa ba. Koda yake a kowanne mataki na rayuwata ina alfahari da kaina da kuma irin jarumtar da na ke nunawa, wajen dauriya da amfani da dabarun inganta tunanin kan rayuwa.

Yaya ki ka tsara gudanar da rayuwarki, idan da so samu ne?
A cikin tsare-tsaren rayuwata, zan so na kasance mai taimakon jama’a. Na taimaka domin ganin ƙananan yara da mata sun samu gata. Sannan kuma ina son in ga na taimaka wajen ƙwato haqqin qananan yaran da aka ci zarafin su. Ina da burin ganin ƙananan yara masu talle a titi kwararo kwararo da almajirai su ma an ‘yanta su tare da tura su zuwa neman ingantaccen ilimi da zai gyara rayuwarsu. Ina so ace ina da hannu a cikin wannan taimakon.

Wacce shawara ki ke so ki bai wa sauran yara mata masu tasowa dangane da kula da kansu?
Shawarata gare su shine, su dage da neman ilimi, kuma su riƙa taimakawa iyayensu da aikin gida, sannan kuma su tabbatar da cewa suna kula da mu’amalar su da maza ýan’uwansu na gida, maƙwafta, na makaranta da duk wani da hulɗa ta haɗa su ko da a wajen talle ne ko wajen aikin gida inda ake tura wasu. Su kula da tsaftar muhalli da kuma tsaftar jikinsu. Idan sun kai lokacin jinin al’ada su yi ƙoƙari su cire kunya su bayyanawa iyayensu, don su samu shawarwarin da suka kamata wajen kula da kansu. 

Yaya ki ke samun taimako da ƙwarin gwiwa da ke dawo miki da walwala a rayuwa?
Gaskiya duk duniya babu mai bani ƙwarin gwiwa da kulawa sosai fiye da mahaifiyata, tana ƙoƙari sosai wurin ƙarfafa min gwiwa tare da nuna min cewa komai zai wuce. Tana cewa wata rana har ciwon abin zan manta shi, kuma zan yi rayuwa mai kyau da inganci, kamar kowa. Kuma alhamdulillahi, ina jin daɗin waɗannan kalamai nata, ina ganin canji a rayuwata. Sannan akwai malamaina, ýan’uwa da masoya da su ma suke taimakawa wajen ƙarfafa min gwiwa. 

An ce ki na tava rubuce rubucen littafi, wanne littafin ki ka rubuta? 
Eh… Ni marubuciya ce, na rubuta littattafai guda biyu, sai dai ba littattafai ne na labaran hikaya ba, na faɗakarwa ne. Littafina na farko shi ne, ‘Mafita Ga Lafiyar ‘Ya Mace’, wanda na rubuta shi da Hausa, kuma na rubuta shi ne don faɗakar da yara mata da suka kai shekarun fara jinin al’ada har ma da ýan mata, muhimmancin kula da lafiya da tsaftar jikinsu. Sai kuma wanda na rubuta da turanci, ‘Shackles of Abuse’, shi kuma jan hankali ne ga iyaye da ýan mata kan yadda za su tunkari ƙalubalen cin zarafi da tozarci daga mugayen mutane. 

Aisha Hamza Kallari

Wacce shawara ki ke so ki bai wa iyaye maza da mata dangane da kula da tarbiyyar yaransu?
Iyaye yana da kyau su kula da tarbiyyar yaran su maza da mata, domin kuwa amana Allah ya ba su. Kuma idan suka kula da yaransu, Annabin rahama zai yi alfahari da su da kuma ‘ya’yansu bakiɗaya. 

Wa ki ke kallo a matsayin tauraruwarki kuma abin koyinki a rayuwa?
Mahaifiyata.

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai, ko kuma in an yi shi yake ɓata miki rai?
Babu abin da yake faranta min rai kamar na ga ƙananan yara suna karatu, na addini da na zamani. Babu abin da yake vata min rai kamar hassada, ƙyashi, gasa da sauran ire iren waɗannan halayen marasa kyau.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?
Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.

Mun gode.
Ni ma na gode.