Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soki jam’iyyar APC bisa kalaman da sakataren watsa labaranta na ƙasa, Feliɗ Morka ya yi game da bayanin sabuwar shekara na tsohon ɗantakarar jam’iyyar LP, Peter Obi, inda Obi ya ce kalaman tamkar barazana ce ga rayuwarsa.
Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce, “Wannan barazanar, da cigaba da riƙe ɗan gwagwarmaya Mahdi Shehu, abin takaici ne, kuma tamkar kama hanyar mulkin kama-karya ne, inda ake shaƙe ‘yan hamayya.”
Ya ce kalaman sakataren watsa labaran na APC cewa Obi “ya wuce iyaka”, “ba su da muhalli a cikin al’ummar da ke da girmama ‘yancin furta albarkacin baki. Don haka ya kamata APC ta bai wa Obi da ‘yan Nijeriya haƙuri.”
“Dimokuraɗiyya ta gaskiya tana girmama adawa da suka mai ma’ana, domin ana amfani da adawar irin su Peter Obi ne a matsayin gudunmuwarsu wajen ciyar da ƙasar gaba.
Ya ƙara da cewa ba su san me Morka yake nufi da ya ce Obi ya shirya ɗanɗana ƙudarsa ba, “ya kamata jam’iyya mai mulki ta fayyace me yake nufi, domin ba za a aminta da irin waɗannan kalaman ba.”