Assalamu alaikum, kamar yadda na saba aiko da wasiƙu na duk mako a wannan jarida mai albarka, yau ma na zo da wata babbar wasiƙa na kira ga matasa, domin tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowace al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda suke gudanar da rayuwa sakaka. Wajibi ne da ya hau kan al’umma ta yi tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da saƙonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su ƙaurace musu.
Duk wata ƙasa da ta ci gaba a wannan duniyar, idan aka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar ci gaban, za a ga a hannun matasansu yake. Saboda ba su yi sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasan ba.
Haƙƙi ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye su kasance mataki na farko ta inda ’ya’yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane da kiyaye dokokin ƙasa da kauce wa ayyukan ɓarna da sauransu.
Idan iyaye suka gaza aikata hakan ga ’ya’yansu, babu tantama a daidai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (matashi) ya fara mu’amala da waɗansu abokai a waje, za su koya masa dukan ɗabi’un da suka ga dama. A wasu lokutan ma yanayin mu’amalar da ke tsakaninsa da su ne zai sa ya riƙa kwaikwayon yadda suke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina tasa ɗabi’ar.
Shekaru da dama muna ta addu’ar Allah Ya kawo mana shugabanni nagari a ƙasarmu, shekaru a baya iyayenmu suna ta cewa mu ne manyan gobe amma har yanzu ba mu da shugabanni masu tausayinmu, kuma har yanzu ba mu zama manyan goben ba.
To me ya jawo haka? Me ya sa har yanzu ƙasarmu ta ƙasa zama yadda muke fata kuma muke ta yi mata addu’a? Amsa ita ce mu matasa mun kasa fahimtar irin gudunmawar da za mu iya bayarwa domin ƙasarmu ta gyaru. Mun yi shiru mun kasa cewa uffan kan yadda ɓarayi ke ta kwashe dukiyoyinmu, mun yi shiru mun kuma kasa haɗuwa wuri guda domin mu haɗa kai mu gyara ƙasarmu.
Ba komai yake sa ni takaici ba illa yadda matasa muka yi sakaci da harkar ilimi! Ga mu da yawan gaske amma ba mu da aikin yi sai kallon ƙwallo da taɗin ƙwallo da kuma yawon bangar siyasa. Ga mu da yawan amma mun ƙi yarda mu nemi ilimi domin mu tallafa wa ƙasarmu.
Kamar da yadda muka sani ne cewa, a halin yanzu, taɓarɓarewar tarbiyya a wannan zamani ya zaburar da al’umma yin hoɓɓasa don yi wa tufkar hanci ta hanyar haɗa hannu wuri guda da waɗanda lamarin ya shafa don ɗaukar mataki. Tarbiyya a wannan zamanin ya zama abu mai wuyar samu, domin ba a ko ina ake samun sa ba. Shin wai me ke jawo taɓarɓarewar tarbiyyar yara? Tarbiyyar yara na ci gaba da fuskantar barazana Nijeriya, abinda mahukuntan ke ɗorawa akan amfani da shafukan sada zumunci.
A gani na, rashin tarbiya ce ta sa yanzu komai ya taɓarɓare, matasa da dama suka lalace suka ɓalɓalce. Iyaye suka gaza wajen sauke nauyin da Allah Ya ɗora musu, gwamnati ta zama wajen handama da baba-kere. Makarantun suka lalace, malamai suka zama jahilai kuma ɗalibai suna koyon jahilcin a wajensu. Wannan shi ake kira malami ya ɓace, kuma shi ma ɗalibin ya bace.
Duk abin da zayyana a sama suna da nasaba da alamun ranar ƙarshe wato kiyama domin Manzon tsira Muhammad (SAWW) ya mana nuni da hakan.
Matsalar a nan ita ce, sau da yawa za ka ga ɗa ya lalace amma iyayensa ba su ma sani ba. Su a tunaninsu yaronsu yana kan hanya madaidaiciya ne saboda rashin kula, sai abin ya yi ƙamari kuma sai su zo suna kuka suna da-na-sani. Dama ance ice tun yana ɗanye ake tankwara shi.
Babban abin da ke janyo taɓarɓarewar tarbiya a wannan zamani shi ne kwaɗayi da son abin duniya. Mutane da yawa suna tsoron mutuwa, amma kuma suna so su shiga Aljanna.
Irin tarbiyar da iyaye suke ba ‘ya’yansu a halin yanzu shi ne ke janyo lalacewar komai. Maimakon irin wannan wasiyoyi da iyaye suke yi, me zai hana iyaye su riƙa yi wa ‘ya’yansu wasiya da jin tsoron Allah? Da nuna musu gudun duniya da taimakon al’umma? Irin wannan wasiyoyin ne manzanni da salihan bayi suka yi wa ‘ya’yansu, wanda hakan ya taimaka musu wajen sauke nauyi da ke wuyarsu na tarbiyantar da ‘ya’yan.
Hakanan idan ka koma ɓangaren shaye-shaye abin ba a cewa komai. Watarana wani abokina yake ba ni labari cewa an yi gasar shaye-shaye, amma abin mamakin shi ne yadda ya faɗa cewa wai mace ta lashe gasar, domin dukan waɗanda suka shiga gasar sun yi mankas sun kasa tashi, amma ita ta tashi har ta fito waje. Yanzu haka maganar da ake yi ɗaya daga cikin waɗanda suka yi gasar ya haukace. Me ye amfanin irin wannan haukar?
Wani abin da ke janyo lalacewar matasa kuma shi ne, yadda iyaye suke sakaci wajen biya wa ‘ya’yansu buƙatunsu. Za ka ga mahaifi ko mahaifiya suna ganin ‘ya’yansu da abin da ba su ne suka saya musu ba, kuma sun san cewa ‘ya’yan ba sana’a suke yi ba, amma su yi shiru. Wani lokacinma za ka ‘ya’yan suna taimakon iyayen da irin wannan kuɗin ko wani abun duniya da suka samu. Abin tambayar a nan ita ce, wai ina suka samo wannan kuɗin? Amsar it ace, idan mata ne, to samarinsu ne suka ba su, kuma duk yarinyar da saurayinta ke ɗaukar nauyin al’amuranta tun kafin su yi aure, tana iya yiwuwa ya ɓata maka yarinya duk da cewa ana samu waɗanda suke taimakawa don Allah. Kuma irin wannan abin yana sa yarinyar ta raina iyayenta. Idan kuma namiji ne, to ko dai yana roƙon abokanansa, ko kuma yana ɗauke-ɗauke. Idan kuwa roƙon abokai yake yi, idan ba a yi sa’a ba, idan abokanan banza ne, to suna iya tunzura shi ya yi duk abin da suke so. Ko dai su koya masa shaye-shaye, ko su koya masa sata.
A ƙarshe nake tambayar iyaya, a matsayinka na uba, sau nawa ka taɓa tashi cikin dare ka yi addu’ar Allah ya shiryar maka da ‘ya’yanka? Idan baka taɓa yi ba, to ka dage domin tarbiyar ‘ya’yanka dole ne, kuma Allah zai tambayeka. Kuma yanzu muna wani lokaci da tarbiya ta yi wahala. Aiki ne babba a gabanku iyaye, sai kun yi haƙuri. Allah Ya baku ikon sauke wannan nauyin, Allah kuma ya saka wa iyayenmu, waɗanda suka yi tsaye wajen ganin sun ba mu tarbiyyar da ta dace a rayuwa. Ilahee Ya Rabbi.
Wassalam. Daga Mustapha Musa Muhammad
08168716583.