Hukumar tace finafinai ta gudanar da taron Maulidin Annabi S A W karo na farko

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A wani yunƙuri na haɗa kan ƙungiyoyin Sha’irai da ke faɗin Jihar Kano domin su haɗu su zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano ta shirya haɗin gwiwa da gamayyar ƙungiyoyin sha’iran Jihar Kano inda suka gabatar da wani gagarumin taron mauludi domin tunawa da zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta Manzon tsira Annabi Muhammad S A W.

Taron maulidin wanda aka gabatar a harabar gidan talabijin na Abubakar Rimi ARTɓ da ke titin Maiduguri a Unguwar Hotoro a cikin garin Kano, ya samu halartar ɗinbin al’umma, malamai, attajirai da manyan jami’an gwamnatin Jihar Kano.

Tun da farko da yake jawabi, shugaban Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, gode wa Allah ya yi da ya ba shi nasarar shirya maulidin wanda shi ne irinsa na farko da hukumar ta taɓa shiryawa domin nuna ƙauna ga fiyayyen halitta manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W).

Ya ƙara da cewa, “Manufar shirya wannan taron, baya ga murna da zagayowar ranar da aka haifi Manzo S A W shi ne, samar da wani dandamali na haɗuwar ƙungiyoyin sha’irai su haɗu a wajen guda domin kyautata alaƙar juna da kuma tafiya tare, domin a duk wani al’amari na tafiya ana buƙatar samar da haɗuwa da tafiya tare domin cimma manufa. To mu a namu tsarin tun da na samu jagorancin a wannan hukumar, babban abin da na saka a gaba shi ne, samar da haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin dukkan wanda yaka a ƙarƙashin wannan hukumar. Don haka muka tashi tsaye babu dare babu rana saboda a samu kyakkyawan haɗin kai da kuma jagoranci a tsakanin mu da ƙungiyoyin da suke ƙarkashin wannan hukumar.

Wannan taro ya zama abin misali da irin yadda manufarmu take tafiya a bisa tsari, saboda wannan shi ne taro na farko da ya haɗa dukkanin ƙungiyoyin sha’irai da suke faɗin Jihar Kano, aka taru a waje guda domin gudanar taron maulidin kuma a nan za ku ga shugabanni da kuma mambobin su na dukkan ƙungiyoyin sha’irai da suke faɗin Jihar Kano sun haɗu a nan suna gabatar da ƙasidun yabon Manzon Allah S A W, don haka ina kira ga dukkan ƙungiyoyin sha’irai, da sauran ƙungiyoyin da suke ƙarkashin wannan hukumar, da mu haɗu mu yi aiki tare domin cimma manufar wannan hukumar ta kyautata tarbiyya da kawo tsarin da ya dace da addini da kyawawan al’adu na Jihar Kano.

A yayin taron maulidin dai sha’irai da dama maza da mata sun gabatar da ƙasidu na yabo ga Annabi. Cikin waɗanda suka rera ƙasidu a wajen sun haɗa da; Malam Sidi Abba, Malam Bashir Dan Musa, Malam Bashir ɗandago, Munhamina Hafiz Auwalu Umar Gawuna, Jamilu Nalado, Faruƙ Ibrahim Ayagi, Mustapha Ali Indabawa. Sai a ɓangaren sha’irai mata inda Sayyada Murja Hafiz Abdullah ta gabatar da ƙasida sai Fatima Labaran Kabara, Naja’atu ta Annabi da Sayyada Rumaisa Muhammad da dai sauransu.

Taron ba iya ƙasidu ya tsaya ba, domin kuwa Sheikh Ibrahim Khalil Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano ya gabatar da jawabi a kan muhimmancin yin koyi da ayyukan Manzo S A W, inda yake cewa, shi son Manzo S A W ba ya tsaya a fatar baki ba ne, a rinka ana son sa ba ne, aiki da biyayya a kan dukkan yadda ya gudanar da rayuwar shi ne abin da ya zama wajibi a kan duk wani Musulmi, domin haka babban abin da za mu nuna na son Manzon Allah shi ne a ga ayyukan sa a tare da mu a wajen mu’amala wannan shi ne tsantsan son Manzo S A W. 

Shi ma a matsayin sa na babban baƙo a wajen, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano Baba Halilu Dantiye, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi riƙo da halaye na Manzon Allah kuma su suffantu da shi, sannan ya yi kira ga ƙungiyoyin sha’irai da su tashi tsaye wajen faɗakar da jama’a haƙiƙanin yadda son Manzo S A W yake, sannan kuma su cire ƙyashi da yake tsakanin su don a taru a yi tafiya tare. 

Haka ita ma Kwamishinayar Raya Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano, Hajiya Ladidi Garko, ta yi jawabi tare da bayyana jin daɗin ta da shirya taron maulidin inda ta yi fatan ɗorewar hakan. Manyan mutane da kuma shugabanni daga hukumomin Jihar Kano suka halarta cikin su akwai shugaban Hukumar Raya Al’adu da yawon Buɗe Ido na Jahar Kano Alhaji Tukur Sagagi, shugaban Tashar Radio Kano Alhaji Adamu Abubakar Rano, Shugabar tashar talabijin ta Abubakar Rimi Hajiya Hauwa Muhammad dai sauransu.