Kwamishinan ’yan sanda a jihar Delta da ke Nijeriya, Olufemi Abaniwonda ya ce jami’an rundunar suk kama wasu mutane huɗu da ake zargin su da kashe wani mutum.
Cikin waɗanda aka kaman har da asalin wanda ya kitsa kisan bayan ya damfari mutumin kuɗi naira miliyan 30 tare da karɓan kuɗin fansa naira miliyan 20 daga iyalin marigayin.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce a ranar 8 ga watan Oktoban 2024 ne aka sanar da rundunar ’yan sanda game da ɓatan marigayin mai suna Paulinus Okon, mai shekara 30 a duniya bayan ya bayyana wa iyalinsa cewa zai kai wa abokin nasa ziyara.
Sai dai abokin ya je gidan su Paulinos yana tambayan inda marigayin yake, tare da bayyana wa iyalin cewa bai san inda yake ba.
Daga baya ya buƙaci iyalin su bayar da kuɗi naira 500,000 da za a kai wa wani boka, wanda zai yi addu’ar gano abokin nasa.
Daga baya ya sake komawa inda ya shaida wa iyalin cewa an yi garkuwa da Paulinus, sannan ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan 20,715,000 domin karɓo shi.
Sai dai an kama shi a lokacin da aka fara zargin cewa yana da hannu a ɓatar marigayin.
Binciken da aka gudanar ya sanay an kamo waɗanda ke da hannu a lamarin, inda ɗaya daga cikin su ya shaida wa ’yan sanda cewa abokin ne ya kai marigayi Paulinus domin a kashe a rafin Orere da ke yankin Otokutu.
