Yadda ta kaya tsakanin Sarkin Bauchi Mallam Yakubu da Shehun Borno

Spread the love

Kwarjinin Mallam Yakubu ya daɗa watsuwa ko ina a ƙasar nan a shekarar 1826 sanda ya ceci Kano da kuma rundunar gamin kai na Daular Usmaniyya daga hannun dakarun Borno. Daga cikin almajiran Shehu Usmanu da aka baiwa tutoci akwai Gwani Mukhtar wanda shi Fulata Borno ne kuma shi ne ya karɓi tuta don yin Jihadi a ƙasar Borno.

A shekarar 1808 Gwani Mukhtar ya ci birnin Ngazargamu da yaƙi ya kuma kori Maina wannan zamani wato Mai Ahmad. Bayan haka ne wani malami mai suna EL-KANEMI daga ƙabilar Kanembu (suma makiyaya ne kamar Filani) ya kawo gudunmawa ga Mai Ahmad har dai EL-KANEMI ya sake kwace Ngazargamu kuma ya kashe Gwani Mukhtar.

A shekarar 1811 Shehu Usman ya bai wa Mallam Ibrahim Zaki tuta da umarnin ya kame Borno.  Mallam Zaki ya sake kama Ngazargamu na dan locaci kafin Mai Dunama ya gama ƙarfi da EL-KANEMI suka sake komawa da Mallam Zaki baya zuwa Katagum. EL-KANEMI ya dunfaro Kano haiƙan bayan ya lashe ƙasar Hadejia da Katagum da Misau.

Maza-maza aka tada Wazirin Sokkoto Gidado don ya tattara askarawan Usmaniyya don kare gabashin wannan daula amma Ina! Rundunar Kenembu ta bunƙasa ainun. Don haka Shehu ya aika wa Sarkin Bauchi Mallam Yakubu cewar ya kawo ɗauki kan askarawan Kanembu wanda sun fuskanto Kano.

Shi kuma Yakubu a wannan lokaci yana Dass. Shehu ya ce Yakubu ya bar Dass waɗannan ‘yan uwane kuma zasu shiga addinin Musulunci Insha Allahu. Yakubu sai ya juya ya nufi inda Amirul-Muminina ya umarce shi.

Madaki Hassan sarkin wase ke kan gaba. An fara gabzawa tsakanin Bauchi da Borno a wani wuri da ake kira Ganzul in da akayi kwana huɗu ana ɗauki ba daɗi.

A rana ta biyar Madaki Hassan ya aika wa Mallam Yakubu cewar abin fa yayi tsauri don haka ya taso da kansa. Yakubu sai ya aikawa Madaki cewar in ya tsorata ne to ya sheko da gudu ya shiga aljuhunsa ya ɓoye.

Ko da Madaki Hassan ya sami wannan sako sai maza ya aiko wa Mallam Yakubu da amsa yana cewa ” A tambayi Mallam ko aljuhunsa ya yi ya al’janna ne ? (Wacce Allah ya yi alƙawari wa masu shahada a yaƙin Jihadi). A shaida masa idan aka kasheni ya sami gawata tana fuskantarsa (wato madaki ya juya don gudu) karya sallaceni. A shaida masa Allah shi sada fuskokinmu a darassalamu. Kadan bayan isowar wannan sako ga Yakubu sai kuma manzo yazo ya shaida masa Madaki Hassan ya yi shahada.

Nan da nan Yakubu ya dunfaro fagen fama tare da ‘yan baka tamkar bayan bushiya don haɗuwa da EL-KANEMI kusa da kwai-kwai. Rundunonin biyu sun gwabza a wani wuri da ake kira FAKE. Wurin na nan kamar kilomita 80 kudu maso gabas da kano tsakanin Garko da Dutsi.

An yi turnuku, yaƙi ya murda,maza sunyi Jan ido kuma yau bakan Bauchi ma’abuta zabgai da ƙare dangi sun takura rundunan Kanembu. Daga ƙarshe dai mutanen Kenambu da shi kansa EL-KANEMI suka juya da gudu.

EL-KANEMI ya tsere ya bar wassu yan kayayyakinsa da kuma TAMBURANSA na mulki. Daga nan Mallam Yakubu bai tsayaba sai da ya haɗe da Dan Kawwa wanda Kenembu suka kora daga garinsa Katagum.

Tare suka gama ƙarfi suka kama snira. Daga baya wajen tsakanin shekara ta 1827 zuwa 1828 suka huɗu suka kama Misau wadda ita ce tungar habe na ƙarshe tsakanin Daular Usmaniyya da Daular Borno. Bayan hakan ne Shehu ya umurci Yakubu da ya damka Misau ga Mallam Mamman Manga wanda Shehu ya bashi Shugabancin Fulata Borno.

Wanda Mallam Yakubu ya bai wa matsuguni a Buri-Buri yayin iso warsa daga Borno. Mallam Yakubu ya rasu a shekara ta 1845 bayan ya share kamar shekaru Arba’in yana jagorancin Jama’arsa. Yakubu ya rasu ya bar ‘ya’ya ashirin da biyar. Fitattu daga cikinsu sune Ibrahim, Salmanu, Abdullahi, Mamudu da Kuma Halilu.

Waɗannan sune tushen gidan sarautan nan biyar na Bauchi kuma dukkan sarakunan Bauchi daga waɗannan gidaje suke.

Tarihin ya tafi daidai. Sai dai abinda aka ruwaito daga masana tarihin Kano, farko farko ya ɗan sha banban.

Abinda Kanawa suka ruwaito shi ne Shehun Borno yazo Kano da yaƙi, lokacin Mallam Dabo yana Sarki. Amma ba a yi yaƙin da Kano kai tsaye ba, Shehu ya juya baya.

A juyawar sa ne bayan mayaƙan sa sun gagara cin Sumaila, ya wuce har ya gamu da rundunar Madakin Bauchi, har abinda kuka ruwaito ya faru

A karon da aka yi da Shehun Borno da Yakubun Bauchi, an ce rundunar Barebari ta fi su yawa ainun.

Amma mazajen Bauchi sun firgita Barebari ta hanyar nuna carnivalism. An ce idan suka. Kashe barden Borno, sai su yayyanke gabobin sa, wasu su daga hannu ko kafa suna cizgar naman suna ci. Ko wasu su farka cikin su ɗebo hanji su rataya a wuyan su.

An ce wannan ya firgita dakarun Borno, wanda yasa suka juya baya suka gudu.

By ukarofi