Daga AISHA ASAS
A matsayin wani mataki na ƙoƙarin bunƙasa jami’an ‘yan sandan Nijeriya, Babban Sufeton ‘Yan Sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya amince da sauya wajen aiki ga Mataimakan Sufeto Janar su 24 zuwa ofisoshin shiyya.
Sanarwar da Mai Magana da Yawun Rundunar na Ƙasa, CP Frank Mba, ya fitar a ranar Talata ta nuna yadda IGP ya bai wa ƙasa tabbacin cewa sauye-sauyen wurin aikin da aka yi wa manyan jami’an hakan zai taimaka gaya wajen ƙarfafa wa rundunar ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a kanta wajen yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata.
Mba ya ce matakin sauya wa jami’an wurin aiki ya soma aiki ne nan take.
Ga jerin sunayen jami’an da lamarin ya shafa kamar haka:
i. AIG SPU FHQ ABUJA – AIG ZAKI M. AHMED
ii. AIG ZONE 4 MAKURDI – AIG MUSTAPHA DANDAURA
iii. AIG CTU FHQ ABUJA – AIG DANSUKI D. GALADANCHI, mni
iv. AIG ZONE 17 AKURE – AIG OKON ETIM ENE, mni
v. AIG BORDER PATROL FHQ ABUJA – AIG USMAN D. NAGOGO
vi. AIG ZONE 7 ABUJA – AIG BALA CIROMA
vii. AIG ZONE 9 UMUAHIA – AIG ADELEKE ADEYINKA BODE
viii. AIG ZONE 13 UKPO-DUNUKOFIA AWKA – AIG MURI UMAR MUSA
ix. COMMANDANT POLAC WUDIL-KANO – AIG LAWAL JIMETA TANKO
x. AIG FCID ANNEX LAGOS – AIG USMAN ALHASSAN BELEL
xi. AIG DOPS FHQ ABUJA – AIG ADEBOLA EMMANUEL LONGE
xii. AIG INVESTMENT FHQ ABUJA – AIG MUSA ADZE, fdc
xiii. AIG DICT FHQ ABUJA – AIG PHILIP SULE MAKU, fdc
xiv. AIG ZONE 6 CALABAR – AIG USMAN SULE GOMNA
xv. AIG COOPERATIVE – AIG ADAMU USMAN
xvi. AIG ZONE 3 YOLA – AIG DANIEL SOKARI-PEDRO, mni
xvii. AIG DTD FHQ ABUJA – AIG AHMED MOHAMMED AZARE
xviii. AIG FCID ANNEX KADUNA – AIG MAIGANA ALHAJI SANI
xix. AIG ZONE 12 BAUCHI – AIG AUDU ADAMU MADAKI
xx. AIG MARITIME LAGOS – AIG JOHN OGBONNAYA AMADI, mni
xxi. AIG ZONE 8 LOKOJA – AIG EDE AYUBA EKPEJI
xxii. AIG ARMAMENT FHQ ABUJA – AIG MOHAMMED L. BAGEGA
xxiii. AIG ZONE 15 MAIDUGURI – AIG BELLO MAKWASHI
xxiv. AIG WORKS FHQ ABUJA – AIG BALARABE ABUBAKAR