Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da Nijeriya ke bikin cikar shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 2025, wata kira ta katse shagulgulan saƙonnin taya murna daga wani tashar rediyo a Legas — kira daga wani mazaunin Mubi, Zephaniah Yako, wanda ya bayyana wahalar rayuwar dubban al’ummomin da ke zaune a lunguna da saƙunan ƙasar, inda gwamnati ba ta isa, kuma ’yan ta’adda suka yi ƙatutu.
A cikin wani rahoto da jaridar intanet ta News Point ta wallafa, ta ce, Yako ya yi magana cikin murya mai cike da raɗaɗi, ya ce: “Ku aika mana da jami’an tsaro kafin ‘yan ta’adda su ƙarar da mu.”
Ya ce, birane suna da taimakon gaggawa idan an kai hari, amma a mafi yawan ƙauyuka hare-hare na iya ɗaukar kwanaki ba tare da jami’an tsaro sun isa ba, saboda tsananin nisa da birni, rashin hanyoyi da kuma katsewar sadarwa.
Wannan kukan ya bayyana yadda dubban ƙauyuka ke rayuwa cikin fargaba a wannan ƙasa mai faɗin kilomita murabba’i 923,770, inda akasarin fili ya koma mafakar Boko Haram, ‘yan bindiga da sauran miyagu.
A arewacin ƙasar, tazarar da ke tsakanin ƙauyuka ta kai kilomita mai yawa, kuma galibin hanyoyin ba su da amfani. A kan layin Yola–Mubi, Yako ya ce akwai ɗaruruwan kilomita tsakanin ƙauyuka — filayen da ba a kula da su waɗanda suka zama mafaka ga ta’addanci.
Wani babban jami’in soja ya shaida wa News Point cewa ko da an samu kiran gaggawa, babu hanyoyin da za a bi. Ya zargi gwamnatocin jihohi da sakaci da gine-ginen karkara, duk da biliyoyin kuɗin da suke samu.
Ya ce: “Ba za a iya yaƙar rashin tsaro ba idan babu hanyoyin shiga yankunan da abin ya shafa.”
Masu nazari sun gargaɗi cewa filayen da ba a kula da su ba suna ƙaruwa. Daga Kano zuwa Dutse, masanin fasaha Theo Adams ya ce filayen da ba kowa ke zaune ba sun sa ya fahimci yadda a iya hallaka al’umma gaba ɗaya ba tare da duniya ta sani ba.
Garin Sambisa mai faɗin 518 km2 ya daɗe yana kasancewa matsugunin Boko Haram, amma masana sun ce akwai ɗaruruwan irin waɗannan wurare.
Tsofaffin jami’an tsaro irin su Bem Hembafan sun bayyana arewacin ƙasar a matsayin “kyautar daji ga ’yan ta’adda” — wuri da suke iya ɓoya dare da rana, su kuma kai farmaki ba tare da tsoro ba.
Hembafan ya yi gargaɗi cewa faɗin ƙasar da ƙarancin jami’an tsaro sun sa ba za a iya shiga dukkan yankuna ba.
Nijeriya na da ’yan sanda 370,000 da sojoji kusan 300,000 — lamba da ba za ta iya rufe kusan rabin ƙasar ba.
A Benuwe, gonakin mangwaro da lemu sun lalace saboda tsoro. A Filato, Bauchi da Borno, jami’an tsaro na ritaya su bar gonakinsu bayan ‘yan ta’adda sun mamaye su.
Wani manomi a Kogi, Idrisu Ocheno, ya ce yanzu gonarsu ba sa zuwa sau da yawa saboda tsoron garkuwa da mutane.
A Kudu maso Gabas, wasu filayen gwamnati sun koma hannun wasu jama’a saboda dogon rashin amfani — kowa ya manta mallakin gwamnati ne.
