Amnesty ta nuna damuwa kan yunƙurin rufe bakin Malam Yahaya Masussuka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar kare Haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana tsananin damuwarta kan matsin lambar da ake yi wa Malam Yahya Masussuka — wani malamin addini da aka sani da wa’azi cikin natsuwa da neman zaman lafiya.

Kungiyar ta ce, yunƙurin wasu ɓangarori na amfani da ƙarfin gwamnati domin dakatar da malamin ko rufe makarantunsa, ba tare da wani shaidar karya doka ba, abu ne da ya saɓa wa doka kuma ya saɓa wa ’yancin ɗan Adam.

Ta ce, irin wannan tsattsauran ra’ayi da wariyar ra’ayi na tauye ’yancin addini, tare da murƙushe masu faɗin ra’ayoyinsu cikin lumana.

Amnesty International ta ƙara da cewa babu shakka akwai hannun wasu ɓangarori da ke son hukunta Malam Masussuka saboda kawai ya ke bayyana ra’ayinsa cikin lumana.

Malamin, kamar yadda aka sani, ya jima yana gudanar da wa’azi da koyarwa ba tare da tashin hankali ba, tare da ƙarfafa tattaunawa da zaman lafiya.

Kungiyar ta jaddada cewa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da dokokin ƙasa da ƙasa suna kare ’yancin addini da tunani, kuma kowane ɗan ƙasa na da damar gudanar da waɗannan haƙƙoƙi ba tare da tsangwama ko tsoro ba.

Amnesty International ta buƙaci hukumomin Nijeriya da su tabbatar da kare haƙƙin Malam Yahya Masussuka da kuma duk sauran ’yan ƙasa, bisa nauyin da gwamnati ta ɗauka na mutunta haƙƙin bil’adama.

By ukarofi