Wata mata a ƙasar Indiya ta kafa tarihi bayan ta yi abin da ake zaton shi ne bikin aure na farko irinsa a ƙasar.
Rahotanni sun ce, matar mai suna Kshama Bindu mai shekara 24, ta auri kanta da kanta ne tare da gudanar da bikin auren a gidanta a gaban ƙawaye da abokan aikinta a ranar 8 ga Yunin da ya gabata.
Da farko ta shirya yin bikin auren ne a wani wurin bauta tare da wani limamin wurin bautar a birnin Badodara, amma Shugabar Jam’iyyar Bharatiya Janata, Sunita Shukla, ta yi adawa da bikin auren a wurin bautar.
An gaya mata cewa, a addinin Hindu ba a yarda mace ta auri kanta ‘sologamy’ ba, don haka bikin ba zai gudana ba.
Sunita ta ce, “ina adawa da zaɓin wurin kuma ba za a bar ta ta auri kanta a kowane wurin bauta ba.
“Irin wannan aure ya saɓa wa addinin Hindu kuma hakan zai rage yawan al’ummar Hindu.
“Idan wani abu ya saɓa wa addini, to babu wata doka da za ta yi tasiri a kan wannan abu,” inji ta.
Amma ga Kshama, auren kanta ‘tamkar sa kai ne’ na tallafa wa kanta da ‘ƙauna marar iyaka’.
Da wannan tunani ta yanke shawarar cigaba da auren kanta kuma ta samu sabon wuri – duk da ana jayayya.
Ta ce, “ban taɓa son yin aure ba, amma ina so in zama amarya – don haka na yanke shawarar in auri kaina.
“Ba zan iya kwatanta hakan da kalmomi ba, amma kowa yana mini fatar alheri tare da kwatanta lamarin da barkwanci, faruwar hakan ya ɗauki hankalina.
“Ina zubar da hawayen farin ciki idan ina karanta saƙonni da labarai kuma ina matuƙar farin ciki da ranar aurena,” inji ta.
Kshama ta fuskanci ƙalubalen dakatar da burinta, kamar yadda limamin wurin bautar ya fara shirin yi mata, an yi shirin soke alwashinta tana daf da auren.
A ƙarshe, ta samu damar kammala auren kanta ta hanyar bin al’adun ‘Mehendi’ da ‘Haldi’ – nau’in fasahar yin zane a jiki da amfani da hodar Turmeric don gyara jikinta.
Duk da koma-baya da ta samu, ta tabbatar da muradinta- kodayake iyayenta sun goyi bayan zaɓinta kuma sun kasance tare da ita a shirin auren kanta.
Kshama ta shirya tafiya hutun amarcinta a garin Goa a cigaba da shagalin bikin auren kanta.