Wani taron ni ke biya kafin a bar ni na yi wasa a wurin – Bilya Kwatarne

“Sana’ar barkwanci ke ciyar da matana biyu har ma da ‘ya’yana”

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Sakkwato jiha ce daga cikin jihohin da Allah ya albarkata da ‘yan wasan gargajiya tun a zamanin baya da su Ɗan Wanzam, Ta rana, ‘Yar mai Albasa, Boka Mai Kwankeli da makamantansu har zuwa wannan lokaci da ake samun matasa masu tasowa da ke wasan kwaikwayo na barkwanci domin nishaɗi ko kuma neman abin saka wa a bakin salati. Wakilin Blueprint Manhaja a Sokoto, Aminu Amanawa, ya zanta da Bilya Kwatarne, matashin da ke wasan barkwanci da tauraruwarsa ke haskakawa, yake kuma ci gaba da jan zarensa a wasan, wanda ya ce, a yanzu ta zamar ma shi sana’ar dogaro da kai. Ga yanda tattaunawar ta kasance:

Da farko ka fara da gabatar da kanka ga masu karatu.
Sunana Bilyaminu Ibrahim Sanyinna, wanda aka fi sani da Bilya Kwatarne.

Za mu so mu ji taƙaitaccen tarihinka?
Ni dai an haife ni a ɗaya ga watan Janairun shekarar 1990, a unguwar makafi nan Jihar Sokoto, na yi firamare a Sultan Muhammadu Macciɗo, da kuma primary school ‘yar gabas , na yi JSS a ‘Govment day’ Ƙofar Marke, daga nan na je na yi sakandare a ‘Giginya memorial secondary School’, daga nan kuma na je Poly na yi diploma a ɓangaren shugabanci, watau Diploma in Public Administration’.

Ta yaya ka tsinci kanka a sana’ar barkwanci?
Yanda na tsinci kaina a cikin wannan sana’ar ta barkwanci shine, tun Ina firamare wata rana a ka yi walima ta yaye ɗalibai, a ka shirya dirama to daga nan dirama ta shiga rayuwata, har Ina tunanin ta ya za a yi ace na tsinci kaina cikin masu yin dirama, to fa kafin in kammala firamare sai da na kai duk za a yi wasan kwaikwayo a makarantar ana sawa da ni, ta dalilin nuna sha’awata ga wasan da na yi ga mataimakin shugaban makarantar, wanda ya kasance mijin yayata.

yayin wata karramawa da Biliya kwatarne ya samu


To daga nan har na je JSS a secondry school Ƙofar Marke. Da yake a gida an siya min mashin, na kan yi kabu-kabu (achava) lokaci-lokaci, don ɗaukar ɗawainiyar karatuna. A nan ne na haɗu da wasu ‘yan wasanmu na Sakkwato. Lagwani shine mutum na farko da na haɗu da shi, na nuna mi shi ai ina da ra’ayi ga harkar ‘industry’ ya ce min ba matsala sun da shi ma ita ya ke yi. To fa daga nan abin ya samo asali.

Kenan ka samu biyan buƙata cikin lokaci tunda dai ka haɗu da masana harkar ko kuwa an sha doguwar gwagwarmaya?
Eh! A haka tashin farko dai a ƙalla na yi shekara ta kai goma ba abinda na ke bayan riƙa wa masu gidajena custom, wato jakar tufafinsu na aiki.

Ba ka ma kai matsayin da za a haska ka ba kenan?
Sosai kuwa.

Bari mu ɗan koma baya, ka ce kana ɗaukar jakar kaya na tsawon shekaru. Shin ya aka yi aka fara ba ka dama?
To, ma sha Allahu, na bi hanya ne tashin farko abinda na koya yadda zan iya canja muryata daga Bilya in koma kwatarne, wanda mu ke karya harshe cikin baiwar da Allah Ya ba mu, shi kuma wannan na koye shi ne a wurin Nura Ɗan Dolo wanda yake fito wa a matsayin Ɗan Ƙwambo a cikin shirin wasan kwaikwayo na ‘Gidan Badamasi’. Amma nan Jihar Sokoto Kalanzir shine mutum na farko wanda ya ba ni tufafi in sa ‘custom’ kuma ya fara sa ni cikin dirama.

A yanzu kana cikin ‘yan wasan barkwanci da Jihar Sokoto ke ji da su. Ko ya ka cimma wannan nasarar duk da dogon lokaci da ka ɗauka kana fafutuka?
To kasan abu na Allah yadda yake, amma lallai tabbas na samu ƙalubalai da yawa, mussaman wurin mahaifiyata, kasancewar ana zugata kan cewa ta bar ni in lalace. Saboda har yau wasu mutane na wa harkar fim kallon lalaci da iskanci, bayan kuma ko kaɗan ba haka abin yake ba. Kamar kowacce sana’a ce, idan ka ɗauke ta sana’a, ta zama hakan gare ka, idan kuwa kasa shashanci za ka ga hakan. Yanzu ka ganni nan, matana biyu da yara biyu, kuma na rantse ma duk da wannan sana’ar na ke ciyar da su. Ban iya sarrafa Naira goma ta koma ashirin ba sai ta wannan sana’a.

Wacce nasara wannan sana’ar ta samar ma ka?
Kai kai kai kai! Ai ko da dama gaskiya! Saboda wata rana Ina daga cikin waɗanda suke diramar ‘Madubi’ a BBC Media Action daga nan muke tashi mu je Abuja cikin jirgi, daga ma unguwarmu zuwa airport Naira dubu goma ne kuɗin tasi ɗina, idan na je airport yadda kasan idan kana kallon fim idan babba ya zo ana kiran sunanshi, a yi ‘welcoming’ ɗinshi, haka ake yi min, na kan ji daɗin wannan abu a rayuwata. Hakazalika albarkacin wannan harkar na je ƙasashen Afrika aƙalla ƙasashe biyar.

Akwai wasu ƙalubalai da ka kasa mantawa da su duk da cewa an fara shan romon wahalar? 
Gaskiya ɗaya ne, kamar yadda na faɗa a baya, yadda ake kai suka ta wurin Innata, duk da cewa, takan bi ni da addu’ar mafita da samun albarka da kare sharri a cikin abin da na ke yi. Kuma alhamdulillahi, Allah Ya karɓa.
 
Shin akan yi jinga ne da ku a lokacin da za a gayyace ku wani taro ko kuwa ya abin yake?
Yawwa Alaji Aminu, na gode ƙwarai da ka yi min wannan tambayar. Tsakani da Allah akwai taron da ni ma na ke biyan kuɗi a sani.

Bilya Kwatarne tare da jarumi Umar M. Sharif

Ko ya hakan ta ke kasancewa?
Yawwa, abinda ya sa haka, Ina son a ga ina yi. Muradina a lokacin da na ke hakan kawai a sanni, don haka ba na duba me zan samu, kawai a san ina yi. Wannan kuma hanya ce ta tallata kai. Ta hakan za a ga iyawata, sai kaga ana nema na idan wasu suka taso, wannan shine riban da na ke su. Misali haɗuwata da uwar gidan gwamna Hajiya Dakta Mariya Aminu Waziri Tambuwal, kaga ai na fara ne da bibiyar masu yi mata hidima a ‘social media’, da na ga ta yi wani abu, sai in yi sauri in haɗa ‘comedy’, in sake shi ga duniya.

Ba tare da ma ta sani ba?
Eh, ba tare da ta sani ba. Har Allah ya sa duk za ta yi taro sai ta neme ni, saboda tasan Ina da rawar da na ke taka wa a wannan wurin. Dalilin haka ma watan da ya gabata, a taron na uwar gidan gwamna, wata ‘yar Ƙasar Nijar, mazauniyar Nijeriya da ta halarci taron, Dakta Amina, ta gayyace ni, na tafi Abuja na yi mata wani program, kuma bayan na ta a nan na ƙara samun wani taron da zan je Togo na yi ƙarshen watan nan, insha Allah.

Na’am, mu na godiya.
Ni ma na gode.