Me ya sa maza suke kasa sauke haƙƙin iyalansu?

Daga AMINA YUSUF ALI

Wai meye ma haƙƙoƙin da suke kan namiji na iyalinsa? Musulunci Addini ne wanda cikin hikima za a ga ya kawo dukkan wasu hukunce-hukunce na zamantakewa. Don haka zaman aure ma bai bar shi a baya ba. Ya tsara haƙƙoƙin mace da miji a aure. Kuma ya jaddada su a cikin Al-Ƙur’ani da hadisai, domin a samu daidaito da fahimtar juna.

A cikin haƙƙin da aka ɗora wa mace babba daga ciki shi ne ta yi biyayyar aure. Ta bi mijinta sau da ƙafa tare da ƙauna da tausayawa. Sannan mace ita ke da haƙƙin kula da mijinta da kuma yaran da za su haifa ko suka haifa ta fuskar ƙauna da tarbiyya. Shi kuma namiji shi ke da kaso ma fi yawa na haƙƙoƙin aure. Saboda shi ke da haƙƙin kula da dukkan buƙatun iyalansa ta fuskar kuɗi. Wato ciyawarwa, shayarwa, tufatarwa, magani, sai saduwar aure da muhallin da za ta zauna da sauran buƙatunta da yaranku.

Haka zalika, namiji Allah ya ɗora wa nauyin tarbiyyantar da iyali da ilmantar da su da sauransu. To amma abin mamakin a ƙasar Hausa saboda wasu dalilai, sai ka ga maza suna matuƙar wasarere da waɗannan haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansu. Sai ka ga haƙƙin da maza da dama suka fi ba wa muhimmanci shi ne, saduwar aure.

Shi kaɗai suke ba wa mata ba tare da ƙwange ba. Wani zubin ma idan aka yi rashin dace da namiji mai neman mata shi kansa wannan haƙƙin ba ya samuwa ga mace. Sai ya tsallake halaliyarsa i zuwa wasu matan banza marasa daraja da Shaiɗan ya ƙawata masa. Ko da kuwa ba su fi matarsa ko matansa daraja da kyau da komai ba.

Haka zalika, wasu lokutan ma idan ba mace guda ba ce, sai ka ga shi ma nan wani mijin hankalinsa ya ɗauke i zuwa wata yana zaluntar wata ta hanyar rashin ba ta haƙƙinta na saduwar auratayya. Amma ma fi yawan lokuta ɓangaren kula da iyali ta fuskar kuɗi an fi samun tawaya wajen sauke haƙƙi. Ƙarshe ma idan ma matan na aiki ko sana’a, sai ka ga su za su ɗauke sauran nauyin. Amma kuma duk da haka, wasu mazan ba sa iya barin mace ta yi aiki ko sana’a. Sun gwammace a yi ta zama a haka cikin wahala. 

Dalilan da suke sa maza rashin sauke haƙƙin iyali:

*Rashin lissafi da almubazzaranci: Shi sha’ani na kuɗin ya kamata a ce ana tsara shi ba wai a bar shi kara zube ba. Wasu masana rashin lissafi da kashe kuɗaɗensu a wani wajen shi yake sa kuɗin ya kasa isar su wajen ɗaukar nauyin iyali. Wani fa sai ya raba albashinsu gida biyu ya yi wa matar banza hidima ko budurwa, ko ya yi wa wani abokinsa bajinta. Ko kuma ya dinga sayen sutura ko wayoyi masu tsada da suka fi ƙarfin arzikinsa. A ƙarshe abinda zai ragu ba zai tava isa ya yi wa iyalansa hidimar da za ta ishe su ba. A qarshe sai ka ga ba abinci isasshe, kuɗin makarantar yara babu, abubuwa dai ga su nan. Idan ba a ci sa’a matar na aiki ko sana’a ba, sai dai a zauna a haka. 

*Zamani ya zo na raba ɗawainiyar gida tsakanin mata da miji: Yanzu zamani ya zo mana da abinda ake kira 50:50 a turance, wato raba dai-dai. Su kansu mazan sun riga sun sangarce, sun manta Allah ne ya ɗora musu wannan haƙƙi. Sun ɗauka kawai da zarar sun ƙyale mace tana aiki ko sana’a, to dole a yi wannan raba dai-dan ɗaukar nauyin gida. Su kansu matan da zarar an bar su suna aiki sai su ga ai dole su saka wa namijin saboda alfarmar da ya yi musu. Sai ka ga sun amshe rabin ragamar gidan. Su dai kawai suna son a zauna lafiya, kuma kada watarana a hana su yin sana’ar. 

*Sakacin matan da na iyayensu: Sakaci daga ɓangaren matan aure ko iyayensu yakan sangarta miji ya gaza ɗaukar nauyin gidansa. Mata da dama saboda so, sai ka ga suna ɗauka wa maza wahalhalun gida. Wani lokacin ma iyayen matan sukan ba mijinta kuɗin ko su ɗauke masa wasu wahalhalun. Wani lokacin ma har gida za ka ga an ba wa mace ta zauna da mijinta saboda ba shi da shi. Su suna ganin sun yi haka don ‘yar su ta zauna lafiya. Sai dai kash! A tarihi mazan da aka yi wa hakan ba su yi butulci ba kaɗan ne. Daga an fara taimakawa, shikenan sai ya sangarce ya qi ɗaukar nauyin iyalansa. Komai yana jira ta yi ko iyayenta. Idan gida ne ma sai ya qi saye saboda yana cikin na matar ko na iyayenta.

*Ƙyashi da sa ido a kan samun da matar take yi: Wani namijin da zarar ya ga matarsa tana sana’a shikenan fa shi kakarsa ta yanke saƙa. Domin kawai ta sauke masa rabi ko dukkan nauyin da Allah ya ɗora masa. Da ma ko ka sa mata ido, ko ba ka sa ba mace idan tana aiki kusan duk abinda ta samu naka ne da yaranka. Ita ce canza kwanon ka da azumi, ƙara wa yara kayan Sallah, sayen kayan kwalliya ko sutura don birge ka da sauransu. Amma sai ya zo ya sake mata ragama ta dawo ma ita da namiji da banbanci.

Sannan kuma ya zama abinda take samu ma ba lallai ya wadata ku dukkan ba. Shi kuma wani fa ko matansa biyu ne, sai ya ƙi ɗaukar nauyin mai sana’ar sai ya yi wa mara aikin hidima ko a munafurce ne. Ka ga a nan ka shiga hurumin da Ubangiji ba zai ƙyale ka ba. Matarka ko biloniya ce kai lebura indai ba ta ce ta yafe maka haƙƙin ɗaukar nauyin ta ba, to yana nan a kanka Allah kuma ba zai qyale ka ba idan ka yi buris da haƙƙoƙinta. 

*Talauci/babu: Wani kuma namijin mai son ɗaukar nauyin iyali ne, kuma mai nema ne. Sai dai talauci da babu sun yi masa dabaibayi. Wannan ko a wajen Allah yana da uzuri. Idan Allah ya haɗa mace da irin wannan sai ta yi ta addu’a kuma ta nemi abin yi don tallafa wa mijinta. 

*Lalaci: Akwai kuma malalacin namiji marar zuciya wanda ba zai fita ya nema ba sai dai ya yi ta zaman gida kamar mace. To bai nema ya samu ba ta yaya zai ɗauki nauyin iyali? Idan Allah ya haɗa mace da wannan kuma tana son sa, sai dai ita ta zama namijin ta dage ta nema ta dinga ɗaukar nauyin iyalin har da shi mijin. Sai dai irin wannan bakinta alaikum ko aure ba zai fara tunkara ba balle ya ce zai mata kishiya, saboda tsoron kada ta janye tallafi. 

*Nauyi ya yi musu yawa: Wasu mazan zahirin gaskiya nauyi ne yake musu yawa. Wani a dangi su kaf shi Allah ya zava ya ɗan buɗa wa. Shi ma ɗin ba wai samu yake da yawa ba, amma ya fi da yawa daga danginsa. Iyayensa ma wataƙila da shi suka dogara. Ga ‘yanuwa ga dangi sun yi masa ca! Idan ya hana su a ce ya ƙi zumunci. Dole kuwa wani haka zai rage wadata nasa iyalin ya yi ta hidimar dangi. Wasu mazan kuma ba Allah ne ya ɗora musu ba, su suka tara mata da yawa alhalin sun san ba za su iya ɗaukar nauyinsu ba. Irin waɗannan mazan shawara, kada su hana matansu aiki ko sana’a. Su ƙyale su a rufa wa juna asiri. Ita ma mace kada ta sa ido sosai duk da haƙƙinta ne, ta yi ƙoƙarin neman na kanta, watarana sai labari.

*Dogon buri da tanadi: Wani namijin kuma Allah ya yi shi matsolo, wani kuma mai tanadi. Duk da ba abu guda ne ba, amma aƙidarsu ɗaya, wato ba sa iya ba wa iyali abinda zai wadace su. Shi matsolo marowaci ne wanda ba ya son a ɓamɓare shi ko sisin kwabo. Iyalansa kuma su ne mutanen da suka fi kowa shan wahalar wannan hali nasa. Shi kuma mai tanadi Wani mutum ne mai tsoron gobe. Duk kuɗin da zai samu a yanzu ba ya iya cin su sai ya yi ta adanawa saboda tsoron talauci a gaba. Wani kuma tanadi ne da shi ko zai gina gida ko sayen mota ko dai wani abu. Sai ya tsuke iyalinsa don cimma wannan buƙatar tasa. Maimakon ya bari arzikinsu ya ƙara faɗaɗa sannan ya cimma waɗancan burikan. 

*Horo ga mata masu almubazzaranci: Wasu kuma matan ne suke jawowa. Namiji yana kishin ya kawo abu gida a wulaƙanta. Idan mace tana almubazzaranci tana kashe wa miji gwiwar cigaba da kyautata wa iyalinsa. 
Waɗannan su ne dalilan da maza suke ƙin ɗaukar nauyin iyalansu. Wataƙila ma akwai wasu da ba mu faɗa ba. 

Mene ne illar rashin sauke haƙƙin iyali ga maza?

Ai tun daga ranar da namiji ya kasa ɗaukar nauyin iyalinsa, to ya riga ya rage wa kansa daraja kuma ya saya wa kansa raini da kuɗinsa a wajen iyalinsa. Daga hikimar ɗaukar nauyin iyali da Allah ya ɗora kan maza, don su bayyana a matsayin shugabanni. Mace bayan aure za ta ji kamar ta rabu da iyayenta ne ta kuma samu wani uban. Shi ya sa a farko take ba wa miji wannan girma da yarda da shi ta juye maka dukkan sirrikanta.

Daga lokacin da ka fara kyararta a kan buƙatunta ko kuma sirrikanta da take gaya maka ka fara ginawa ko amfani da shi don cutar da ita ko yi mata guri, to sai ta ja maka layi. Za ta gane ashe kai ba ka da e da matsayin uba a wajenta ba. Kuma hakan Yayana zai rage muku soyayya da girmama wa daga ɓangarenta.

Haka namiji mara ɗaukar nauyin iyali yana rage wa kansa damarmaki kala-kala. Misali idan matarka ke ɗaukar nauyin ka ko kuma gidanta kuke zaune ko ba a gaya maka ba kai ka san ba kai ba rakito maganar aure. Ba za ka fara ba kuma sai dai ka ga ana yi. Ko ka yi sai dai ta fita don ba kowacce ta saba kuma za ta jure ɗaukar nauyin kanta ba. 

Haka zalika, maza da yawa ba sa kula idan suna sauke haƙƙin iyalansu samun su ya fi yawaita. Wani fa da ma saboda matarka da yaranka Allah yake ba ka arziki. To ka hana su kuma, sai ka ga kai ma Allah ya sa samunka ya yi ƙasa ko kuma kana samu amma ba albarka. Kaɗan daga uqubar wasarere da haƙƙin iyali. Ko ba kwa ganin wasu an da ba su da arziki amma daga sun auri wata sai ka ga arziki yana ta habaka? Kai a ganinka arzikin ba shi da nasaba da ɗaukar nauyin ta? Sannan kuma Allah ba zai ƙyale ka ba ko a Duniya ko Lahira sai ya hukunta ka a kan ƙin yin biyayya ga dokar Sa. Idan ba za ka iya ba me zai sa ka rakito auren? To Allah dai ya kyauta.

Mu cigaba da karanta shafin zamantakewa a jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Allah ya kai mu wani makon.