Ƙasar Sin za ta cigaba da taimakawa Sri Lanka iya ƙarfinta

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada yayin taron manema labarai na yau Talata cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da taimakawa iya ƙarfinta, wajen kyautata yanayin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasar Sri Lanka.

Har ila yau a yau din, Wang Wenbin, ya musanta furucin da babban jami’in ofishin jakadancin Amurka a yankin Hong Kong, Hanscom Smith ya yi game da yanayin yankin, yayin da yake gabatar da jawabinsa na murabus. A cewar kakakin, Amurka ta yi watsi da gaskiya, tana tsokacin da bai dace ba game da manufar shugabanci a HK, inda take ƙoƙarin bata yanayin siyasa da tattalin arzikin yankin.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa