Yadda cigaban fasahar sadarwa ke barazana ga aikin jarida

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba da jimawa ba a ranar 3 ga Mayu aka gudanar da bukin ranar bayyana ’yancin ‘yan jarida na gudanar da bincike da samar da bayanai ga jama’a, da nufin faɗakar da al’umma, musamman hukumomi da jami’an tsaro da sauran su muhimmancin tsare hƙƙoƙin ɗan jarida da masu neman labarai, da mutunta su.

Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware kowacce wannan rana a kowacce shekara ta zama ranar da za a riƙa haɗuwa ana tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar manema labarai a fagen samar da bayanai. 

An fara gudanar da bukin wannan rana ne shekaru 30 da suka gabata, domin tunawa da Yarjejeniyar Windhoek da aka qulla a ƙasar Namibiya a 1991, game da muhimmancin ‘yanci da sake wa ‘yan jarida mara su gudanar da ayyukan su ba tare da wata tsangwama ba. Har wa yau bukin wannan rana ya zo daidai da muhimman ranaku kan ‘yancin ‘yan jarida a wasu ƙasashen duniya irin su China, Koriya ta Arewa, Biyatnam, Laos, Eritiriya, Djibouti, Turkmenistan, Sa’udiyya, Siriya, Iran da Cuba. 

A kowacce shekara ana zaɓar wani darasi da ya dace da wani ƙalubale ko cigaba da aikin jarida ke fuskanta a duniya, domin a tattauna a kai, da samar da shawarwari ga mahukunta. A bana bukin ya mayar da hankali ne wajen duba ‘Ƙalubalen Fasahar Zamani ga Aikin Jarida’, da nufin nazari kan yadda aikin jarida ke gwagwarmaya da canjin fasahar sadarwa ta yanar gizo, inda mujallu, jaridu, tashoshin talabijin da rediyo  ke komawa yanar gizo ko raba ƙafa tsakanin buga jaridar takarda da bugawa a yanar gizo. Haka ma da yadda canjin ke shafar wasu ma’aikatan cibiyoyin watsa labarai, da a baya suke da muhimmanci a yanzu kuma tasirin aikin nasu ya dusashe. 

A irin wannan rana ne masu faɗa a ji a harkar sadarwa da watsa labarai ke tunatar da hukumomi su kula da buqatun ‘yancin faɗin albarkacin baki, ’yancin neman bayanai, da watsa labaran da aka tattara cikin kiyaye ƙa’idoji da sharuɗɗan aikin jarida. 

Aikin jarida ya yi matuƙar canzawa, sakamakon bayyanar sabbin kayan aiki na zamani da na’urori na aikawa da saƙonnin kar ta kwana, abin da ya kawo canji a yanayin ba da rahotanni, fitar da labaru ba tare da samun jinkiri ba, da kuma inganta tsarin hoto ko sauti na yadda labari zai ja hankali ya kuma isar da saƙon cikin sauri. 

An samu ƙaruwar tashoshin watsa labarai, masu amfani da yanar gizo wajen isa ga masu sauraro da bibiyar labaran su a zaurukan sada zumunta da tashoshin satilayet na digital da ke watsa shirye-shirye a ko’ina a ƙasashen duniya. Sai dai kuma bazuwar sabbin kafafen sadarwa da zaurukan watsa labarai na bogi da wasu ke buɗewa a shafukan sada zumunta, na yaɗa labaran ƙarya da watsa rubuce-rubuce na angiza rikice-rikice da savani a tsakanin al’umma, saboda rashin ƙwarewa da son zuciya da wasu baragurbin ‘yan ƙasa suke nunawa. A dalilin haka, aikin jarida na fuskantar ƙalubale na jaddada yardar jama’a da amincewar da suke nuna wa kafafen watsa labarai na ainihi, saboda ingancin labaran da suke samarwa. A maimakon sabbin shafukan sadarwa marasa inganci da tsari. 

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust, shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) Chris Isiguzo ya bayyana takaicin sa na yadda wasu baragurbin ‘yan ƙasa da suke kiran kansu ‘yan jarida, ke fakewa da kima da martabar da wannan aikin ke da shi, suna aikata abin da ya savawa ƙa’idojin aikin jarida, da sunan yaxa labarai da ‘yancin faɗar albarkacin baki. Sannan ga kuma yadda ake tauye haƙƙoƙin manema labarai, inda ya zargi jami’an tsaro da hukumomi da bibiyar ‘yan jaridu na gaskiya, suna sauraron hirar su ta waya, da yi wa rayuwar su barazana, abin da ke haifar da tarnaqi wajen tafiyar da ayyukan su cikin walwala da ‘yanci. A maimakon su farauci ‘yan jaridar bogi masu yaɗa ƙarairayi da jirkita gaskiya. 

Daga cikin irin ƙuntatawa da tauye haƙƙoƙin da ake yi wa ‘yan jaridu a ƙasar nan cikin shekarar da ta gabata, har da tsarewar da aka yi wa wani ɗan jarida da ke wakiltar jaridar People’s Daily a Jihar Binuwai, Sunday Ode, bisa umarnin Gwamnan jihar Samuel Ortom. A Jihar Imo, a ranar 30 ga watan Mayu, an kama wasu masu tallen jarida su 6 bisa zargin suna sayar da wasu takardu da masu nasaba da ayyukan ‘yan awaren Biyafara. A ranar 29 ga watan Yuni, aka kashe wani ɗan jarida mai gabatar da shirye-shirye a tashar rediyo ta Naija FM, Titus Badejo, a birnin Ibadan na Jihar Oyo. An kuma rawaito cewa, ‘yan sanda sun ci zarafin wani wakilin jaridar Turanci ta Punch, Friday Olokor, tare ƙwace wayar aiki da wata ’yar jarida Patience Ihejika da ke aiki da jaridar Leadership. 

A wani rahoto da Kwamitin Kare ’Yancin ’Yan Jarida na CPJ ya fitar an bayyana cewa, aƙalla ‘yan jarida da ma’aikatan gidajen watsa labarai 27 aka kashe cikin wannan shekara, daga ciki har da ɗan jaridar nan Tordue Salem da ya yi aiki a jaridar Vanguard, wanda aka kashe shi a Abuja cikin watan Oktoba na shekarar 2021. 

A yayin rubuta wannan sharhi, ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ a Jihar Filato na nan cikin alhini da jimami, biyo bayan, yadda wasu ‘yan jarida su 13 suka sha da ƙyar a wani hari da wasu fusatattun matasa suka kai musu yayin da suke tafiya a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke kudancin jihar cikin wata mota ƙirar safa, mallakar ƙungiyar, abin da ya haifar da kona motar ƙungiyar ƙurmus. Lamarin da ya auku yayin da ‘yan jaridar ke yi wa Sanata Nora Daduut mai wakiltar Shiyyar Filato ta Kudu a Majalisar Ƙasa rakiya don ƙaddamar da wani aiki da ta yi a yankin Namu, inda ta samar da cibiyar koyar da dabarun sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa. 

Abin takaici ne, a yayin da ‘yan jarida ke sadaukar da rayuwarsu, suna shiga haɗari don yaɗa ayyukan ‘yan siyasa da gwamnati, amma a ɗaya ɓangaren rayuwarsu ba ta zama a bakin komai ba. Mutuncin su da darajar su ba su zama abin kulawa ba, kowa na iya wulaƙanta xan jarida ko ya ci zarafinsa, don ba ya ganin kimarsa da girman da ya cancanta a bashi. Sakamakon yadda gwamnati da hukumomi suka yi watsi da shi aka rasa wanda zai masa gata. 

A Nijeriya da wasu ƙasashen da ke cikin fitinar ta’addanci irin wannan rayuwa ce ’yan jarida ke fuskanta, bayan ƙunci da tsananin da suke rayuwa a ciki na rashin kyan albashi da rashin muhallin da ya dace na gudanar da aiki. 

Ba a ƙarƙashin gwamnatin mulkin soja ba hatta a wannan mulkin na Dimukraɗiyya ma ‘yan jarida na ganin tasku iri-iri daga hannun jami’an tsaro da shugabanni dake zargin ‘yan jarida da hassala wutar rikice-rikicen ƙabilanci da siyasa wanda yanzu haka ƙasar nan ke fuskanta, ko kuma batun ɓata sunan gwamnati a idon talakawan ƙasa. 

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar da wani rahoto da ke bayyana cewa, a duk bayan kwana 4 ana kashe ɗan jarida ɗaya, a tsawon shekaru goma da suka gabata, musamman a ƙasashen da ake fama da ƙalubalen tsaro da yaƙe-yaƙe. Rahotanni sun bayyana cewa a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2020 an kashe ‘yan jarida kimanin dubu 12, a yayin da suke gudanar da aikin su na neman rahotanni. 

Gwagwarmayar da ‘yan jarida ke sha wajen sadaukar da lokacin su da rayuwarsu don ganin sun samar da muhimman bayanan da za su taimakawa al’umma, ta hanyar faɗakar da su da wayar musu da kai game da yadda za su inganta rayuwarsu, ba ƙarama ba ce, amma kuma abin takaicin shi ne ƙalilan ne daga cikin al’umma su ke yabawa da wannan ƙoƙarin nasu. A wajen hukumomi kuwa ai ba su da waɗanda suke kallo a matsayin riƙe-wuya ko barazana, kamar ‘yan jarida. 

Wannan hali da ‘yan jaridar Nijeriya da wasu ƙasashe masu tasowa, ke fuskanta ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin ƙasar Amurka ke tsawatar wa gwamnatoci da kwamandojin yaƙi a fagagen fama daban-daban, game da buƙatar sakar wa ’yan jarida mara su gudanar da aikin su cikin ‘yanci da aminci!

Yayin da muke qara jinjina da yabawa ga irin rawar ganin da ’yan jarida na gaskiya ke takawa, muna kuma fatan ganin canje-canje na cigaban aikin jarida, da ya haɗa da inganta muhallin aiki, da kyautata albashi da samar da sabbin na’urorin aiki na zamani da za su dace da aikin jarida a ko’ina a duniya.