Yadda Gwamnatin Tarayya ta bankaɗo ma’aikatan bogi 45,000 ta hanyar BVN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohuwar Ministar Kuɗi ta Tarayyar Nijeriya, Kemi Adeosun, ta bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta gano dubban ma’aikatan bogi a cikin tsarin albashi, bayan haɗa bayanan Lambar Tantance Asusun Banki (BVN) da tsarin biyan albashi na gwamnati.

Ta yi wannan bayani ne yayin wani taron tattaunawa na makarantar shugabanci da aka gudanar a Legas, inda ta yi ƙarin haske kan yadda aka yi amfani da fasaha wajen gyara kura-kurai da suka daɗe suna addabar tsarin biyan albashi na gwamnati.

A cewarta, kafin aiwatar da wannan gyara, kuɗin albashi na ma’aikata shi ne mafi girman kaso a kashe-kashen gwamnati, amma tsarin na cike da gibin da ya sa ake samun almundahana da rashin daidaito.

Ta ce, yunƙurin baya-bayan nan na amfani da bayanan yatsu (biometric) domin tsaftace tsarin ya fuskanci cikas, musamman daga wasu hukumomin tsaro kamar ‘yan sanda da sojoji, waɗanda ba su amince da tsarin tantancewar ba.

Saboda haka, maimakon ƙirƙirar wani sabon tsari, ma’aikatar ta koma amfani da bayanan BVN da ke riga suna hannun bankuna, inda aka gwama bayanan albashin ma’aikata da bayanan BɓN.

“Mun yi amfani da BVN, kuma sakamakon ya ba mu mamaki — mun gano ma’aikatan bogi 45,000,” inji ta.

Sai dai ta yi karin bayani cewa ba lallai ne duk waɗannan su zama “bogi” kai tsaye ba, domin a wasu lokuta mutum guda ne ke karɓar albashi fiye da guda daya ta hanyoyi daban-daban.

A cewarta, wasu matsalolin ma sun samo asali ne daga gazawar tsarin aiki, kamar yadda aka samu sunayen mutanen da suka mutu ko suka bar aiki amma har yanzu suna cikin jerin masu karɓar albashi.

Domin tabbatar da ɗorewar wannan gyara, Madam Kemi Adeosun ta bayyana cewa an ƙara tsarin ɗaukar alhaki, inda aka wajabta wa manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati su sanya hannu kai tsaye a kan jerin albashin ma’aikatunsu, domin hana shigar da bayanan bogi.

Ta kuma jaddada muhimmancin amfani da bayanai da fasaha wajen tafiyar da mulki, tana mai cewa hujjojin da suka dogara da bayanai su ne mafi ƙarfi wajen yanke shawara.

A yayin taron, wasu manyan masu ruwa da tsaki irin su Tunde Bakare sun yaba da jajircewar Adeosun, tare da jaddada bukatar kawo sauye-sauye da gaskiya a harkokin gwamnati.

Masu halartar taron sun amince cewa gano ma’aikatan bogi 45,000 babbar nasara ce, amma suka buƙaci a kafa dokoki da za su tabbatar da ɗorewar irin wannan gyara domin kare dukiyar al’umma.

By ukarofi