Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da farashin shanu da nama ke ci gaba da tashi a faɗin Nijeriya sakamakon matsin tattalin arziki da hauhawar farashi, iyalai masu ƙaramin ƙarfi na ƙara cire nama daga cikin abincinsu na yau da kullum, lamarin da masana ke gargaɗin cewa na iya ƙara jefa miliyoyin mutane cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Rahoton da jaridar PUNCH Healthwise ta wallafa ya nuna yadda talauci da raguwar ƙarfin saye suka sa iyalai da dama ba sa iya sayen nama, kifi, kaji, talo-talo ko sauran abincin da ke ɗauke da sinadarin furotin.
A kasuwar Kara da ke Isheri a kan iyakar jihohin Legas da Ogun, wata mai sayar da kayan lambu mai suna Olaide Alarape ta bayyana cewa ta shafe sama da watanni biyu ba tare da sayen nama ba saboda tsananin tsadarsa.
Ta ce, a yanzu ma idan mutum ya kai Naira dubu biyu wajen masu sayar da nama, ƙananan gutsattsarin nama kaɗan ne kawai za a ba shi.
“Yara na suna son nama sosai, amma yanzu ya zama tamkar kayan alatu. Saboda haka na fi sayen ƙwai na Naira dubu ɗaya domin yin miya maimakon sayen nama mai tsada da zai ƙare lokaci guda,” inji ta.
Haka ita ma Nnena Victor, wata mata mai yara huɗu da ke rayuwa da abin da take samu daga wankin kaya a yankin Berger na jihar Legas, ta ce yanzu iyalinta sun fi rayuwa da garri, taliya da doya saboda rashin ikon sayen nama ko kifi.
Ta bayyana cewa kafin tsadar rayuwa ta ƙaru, suna iya cin nama sau da dama a mako, amma yanzu ƙwai ne kawai suke iya saya lokaci zuwa lokaci.
Binciken ya nuna cewa a kasuwannin Legas, Kano, Enugu, Fatakwal da sauran birane, farashin kayan furotin ya yi tashin gwauron zabo.
A yanzu kilogram ɗin naman sa na kaiwa sama da Naira dubu takwas, naman akuya ya zarce Naira dubu goma, yayin da turkey da kaji ke kaiwa tsakanin Naira dubu bakwai zuwa sama. Farashin kifi kuma yana tsakanin Naira dubu uku zuwa goma, gwargwadon iri.
Ko ƙwai da mutane da dama suka koma amfani da shi a matsayin madadin nama ya yi tsada matuƙa, inda farashin kiret ɗaya ya haura Naira dubu shida.
Masana harkar abinci mai gina jiki sun bayyana cewa wannan yanayi na iya ƙara haddasa matsananciyar matsalar rashin gina jiki musamman ga yara ƙanana, mata masu juna biyu da iyalai marasa ƙarfi.
Hukumar Asusun Kula da Yara ta Majalisar ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ta bayyana cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da matsalar ƙarancin gina jiki a duniya, inda kusan yara miliyan biyu ke fama da matsananciyar yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Rahoton ƙididdigar Lafiya da Yawan Jama’a na Nijeriya na shekarar 2023 zuwa 2024 ya nuna cewa kusan kashi 40 cikin 100 na yara ’yan ƙasa da shekara biyar a Nijeriya suna fama da ƙarancin tsayi sakamakon rashin abinci mai gina jiki.
Haka kuma Majalisar ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa mutum miliyan 35 a Nijeriya na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa a shekarar nan.
Mata da dama da suka zanta da jaridar sun bayyana yadda suke rage amfani da nama a gidajensu saboda tsadarsa.
Wata uwa mai suna Idayat Olayemi daga yankin Alagbole a jihar Ogun ta ce yanzu ta fi amfani da ganda da ƙwai domin ciyar da ’ya’yanta.
Ita kuwa Toyin Alawode, mai sana’ar gyaran gashi a Ogba na jihar Legas, ta ce idan mutum ya kai Naira dubu ɗaya wajen mahauta yanzu, ƙananan gutsattsarin nama kaɗan kawai zai samu.
A cewarta, “Saboda haka na fi sayen ƙwai ko busasshen kifi domin yaran su samu abin haɗawa da abinci.”
Masu sana’ar sayar da shanu da mahauta sun danganta tashin farashin nama da cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi, wanda ya jawo hauhawar kuɗin sufuri da na ciyar da dabbobi.
Sakataren Kuɗi na ƙungiyar Dillalan Shanu ta Nijeriya, Alhaji Isa Muhammad, ya ce kafin cire tallafin mai, babbar saniya ba ta wuce Naira dubu 700 ba, amma yanzu wasu shanu a Arewa suna kaiwa har Naira miliyan 2.5 zuwa miliyan uku.
Ya bayyana cewa kuɗin jigilar shanu daga Maiduguri zuwa Legas sun tashi daga kusan Naira dubu 500 zuwa sama sosai, yayin da farashin abincin dabbobi ma ya ninka sau da dama.
Shugaban ƙungiyar Dillalan Shanu ta Isheri-Olofin a jihar Ogun, Alhaji Kolo Muhammad, ya ce yanzu akwai manyan shanu da ake sayarwa sama da Naira miliyan uku.
Shi ma Shugaban ƙungiyar Mahauta ta Jihar Legas, Ismaila Babalola, ya ce mahauta da dama sun bar sana’ar saboda tsadar shanu da tarin basussuka.
Ya yi kira ga gwamnati ta tallafa wa mahauta da dillalan shanu domin rage tasirin tsadar rayuwa a harkar.
Masana abinci mai gina jiki sun yi gargaɗin cewa rashin samun isasshen furotin na iya haddasa matsaloli irin su ƙarancin jini, raunin garkuwar jiki, matsalar girma ga yara da kuma matsalolin haihuwa ga mata masu juna biyu.
Tsohon Daraktan Ayyukan Gina Jiki na Jihar Osun, Mista James Oloyede, ya ce yara ƙanana ne suka fi fuskantar haɗari idan aka ci gaba da rage cin abinci mai ɗauke da furotin. Ya ce idan yara ba su samu isasshen furotin ba, hakan na iya hana kwakwalwarsu bunƙasa yadda ya kamata tare da jefa su cikin matsalar rashin girma da rashin lafiya.
Wata ƙwararriyar masaniyar abinci, Olufunmilola Ogunmiluyi, ta ce furotin daga dabbobi na ɗauke da muhimman sinadarai da jiki ke buƙata domin ci gaba da lafiya. Ta yi gargaɗin cewa idan matsalar ta ci gaba, Nijeriya za ta iya fuskantar ƙarin matsalar “ɓoyayyiyar yunwa”, wato mutanen da suke cin abinci amma jikinsu ba ya samun sinadaran gina jiki da ake buƙata.
