Wadada ya zama ɗan takarar gwamnan Nasarawa a APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanata Aliyu Ahmed Wadada ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC a Jihar, Farfesa Theodore Maiyaki (SAN) ya sanar da haka a gidan gwamnatin jihar da ke Lafiya a yammacin ranar Juma’a.

Ya ce, Wadada ya yi nasara ne bayan samun ƙuri’a 195,285, lamarin da ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na kuma tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, wanda ya samu ƙuri’u 39,675.

Da fari, Gwamna Abdullahi Sule ya ayyana Sanata Wadada a matsayin magajinsa a kujerar gwamnan jihar.

Shugaban kwamitin zaɓen ya ce an gudanar da zaɓen fidda gwanin cikin lumana ba tare da samun ƙalubalen da ya haifar da wani tsaiko ba.

A ƙarshe, ya yaba wa Shugaban jam’iyyar na jihar, Aliyu Bello bisa samar da yanayi mai kyau da haɗin kan kwamitin wajen gudanar a harkokin zaɓen.

By Babaji