Yadda ISWAP suka kashe Janar Dzarma Zirkusu a wani kwanton ɓauna

Daga BASHIR ISAH

A juma’ar da ta gabata sojojin Nijeriya suka far wa mayaƙan ISWAP jim kaɗan bayan sun idar da sallar Juma’a, inda sojojin suka yi wa ‘yan ISWAP luguden wuta ta sama da ƙasa, lamarin da ya haifar da samun galabar sojojin a kan ‘yan bindigar inda suka halaka da damansu tare da jikkata wasu.

Bayanai sun nuna ‘yan ISWAP na tsaka da tattaunawa ne tare da sabon kwamandansu, Sani Shuwaram a Sabon Tumbun da kuma Jibularam a yankin ƙaramar hukumar Marte, jihar Borno yayin da sojojin suka yi musu kwanton ɓauna.

Majiya daga rundunar sojojin sun shaida wa jaridar PRNigeria cewa harin haɗin gwiwa tsakanin sojojin sama da na ƙasa da aka kai a ranar Juma’a shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar sabon kwamandan ISWAP da aka naɗa, wato Sani Shuwaram tare da wasu manyan kwamandoji daga ɓangarorin mayaƙa mabambanta.

Majiyan sun ce ganin irin ɓarnar da aka yi musu da kuma hasarar da suka tafka, hakan ya ɗugunzuma hankalin mayaƙan ISWAP inda suka kai wa sojoji hari a ƙauyen TomsuKawu tare da kashe dakaru guda uku sannan suka ƙwace motar yaƙi ɗaya.

Kazalika, an ce mayaƙan sun sake kai wani harin ranar Juma’a da da dare kusa da Maiduguri babban birnin jihar, sai dai babu wani cikkaken bayani da aka fitar a kan haka.

Daga nan, aka ce ɓacin rai da raɗaɗin dandaƙar da sojiji suka yi musu, ya sa mayaƙan ISWAP suka soma lalata turakun sadarwa (masts) da ke yankuna da zummar katse sadarwa a yankin domin ba su damar shirya babban farmaki.

Majiyar PRNigeria ta ce a wannan halin ne mayaƙan ISWAP suka kai hari cikin garin Askira inda suka lalata turakun sadarwa (masts) ta amfani da bindigoginsu da sauran makaman da suka mallaka wanda hakan ya tilasta wa mazauna yankin ficewa daga garin.

Majiyar ta ci gaba da cewa ana cikin haka ne sai aka kashe wani kwamandan sojoji, wato Janar Dzarma Zirkusu, a daidai lokacin da yake jagorantar dakaru wajen sake sabon shirin kai wa ISWAP hari. Haka ma wasu sojoji sun ransu a wannan lokaci.

A cewar majiyar, bayan haka wasu gungun ‘yan bindigar sun kai hare-hare a wurare daban-daban inda suka ci gaba da lalata turakun sadarwa da kuma satar shanu.