
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun taru a wajen gidan Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da ke Fatakwal babban birnin jihar, domin su bayyana kokensu.
Wata ɗaukar bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa ya nuna yadda masu zanga-zangar su ka yi dandazo inda da dama daga cikin su ke riƙe da takardun da ke ɗauke da saƙonni masu yawa.
Haka nan, an ga sinƙi-sinƙin jami’an tsaro da su ka bazu a wajen cikin shiri don tabbatar da tsaro a yankin.
A lokacin zanga-zangar, an samu wasu na rera tsohon taken ƙasa yayin da ɗaya daga cikin su ya yi nuni da cewa “wancan ne gidan Wike”.
