Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya kira wani taron tsaro na gaggawa a hedkwatar tsaro da ke babban birnin tarayya Abuja.
Taron ya biyo bayan umarnin Shugaban ƙasa Bola Tinubu na cewa a tabbatar an kawo tsaro saboda zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar. Taron ya sami halarcin hukumomin DSS, NIA, DIA da sufeton ƴan sanda.
Taron ya sami halartar manyan sojojin ƙasar kamar su, Janar Lagbaja, Air marshall Hassan Abubakar da kuma wakilan hukumar kwastom da hukumar shige da fice ta Immigration.
A na sa rai taron zai fara nan ba da jimawa ba.
