Daga MAHDI M. MUHAMAMD
Kungiyar Masu Tace ɗanyen Mai ta Nijeriya ta bayyana cewa, a yayin da Gwamnatin Tarayya ke fito da sabbin matakai, farashin man fetur da matatar man Dangote ke samarwa na iya sauka a ƙasa da Naira 600 a kowace lita.
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Eche Idoko, ya shaida wa manema labarai a wata hira cewa har yanzu ƙungiyar tana da yaƙinin cewa matatun mai na cikin gida kamar Ɗangote da sauran su na iya rage tsadar man fetur.
Idoko ya ce, N898 a kowace lita da kamfanin man fetur na Nijeriya ya yi ikirarin cewa farashin da ya sayi man fetur daga Ɗangote kenan, ya nuna tashin farashin canji.
Ya yi bayanin cewa N898 za ta ragu zuwa N550 idan har aka sanya kuɗin canji a kan N1,000 a kowace dalar Amurka na kayayyakin man da ake samarwa a cikin gida.
A cewarsa, man da matatar Ɗangote ke sayar da ita tun a makon jiya Lahadi, an samar da ita ne daga ɗanyen man da aka shigo da ita daga waje da kuma wanda ake saya a gida da dala.
