Yadda na samu kaina a harkar fim, Saratu Giɗaɗo (Daso)

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da sunan Daso, jaruma ce da ta daɗe ana damawa da ita a cikin masana’antar, wadda a yanzu idan ana maganar dattawan cikin harkar fim to Saratu za ta iya shigowa cikin su.
Tsawon shekarun da ta shafe a matsayin ba tare da an daina yayin ta ba ya kai ta ga zama kaɗan daga cikin jaruman da su ka kafa tarihi a cikin masana’antar domin wasu ɗan lokaci kaɗan su ke ci sai a daina ganin su, ko dai a ce sun bar harkar, ko kuma su na ciki amma ba a yi da su, sai dai ita jaruma Saratu Giɗaɗo Daso abin ba haka ya ke ba a gare ta saboda har yanzu tauraruwar ta ta na haskawa. Domin jin yadda ta shiga harkar fim da kuma irin gwagwarmayar da ta sha, wakilin Manhaja a Kano, MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da ita, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance.

Da farko za mu so ki gabatar mana da kan ki ga masu karatun mu.
To Assalamu alaikum, ni dai suna na Saratu Gidado wadda aka fi sani da sunan Daso a cikin harkar fim. Ni ‘yar asalin garin Kano ce haifaffiyar cikin birni. Iyaye na da kakanni duka ‘yan Kano ne, mu ne asalin ‘yan Kano. Alhamdu lillahi, iyaye na sun ba ni tarbiyya sun saka ni a makarantar zamani, sun saka ni a makaranta ta addini duka. Na yi ilimi mai zurfi tun daga firamare, har zuwa Kaduna Polytechnic, kuma Alhamdu lillahi na karanta fannin kasuwanci, inda na samu National Diploma, sannan na je Landan na karanta ilimin halayyar ɗan Adam wadda Allah ya ba ni baiwa a haka cikin ilimin da na yi duk wani motsi da mutum zai yi ko wani kallo, to gaskiya na kan fassara shi daidai da abin da ya ke nufi, ba ma sai ya furta da baki ba, sai dai ɗan abin da ba za a rasa ba. Don shi wannan karatun da na yi mutum zai iya yin aikin jami’in tsaro kamar DSS da dai sauran su, kan abin da ya shafi bincike, to Alhamdu lillah sai kuma Allah ya sa na shiga harkar fim, kuma na yi karatun addini daidai gwargwado, don ni Musulma ce iyaye da kakanni, duk zuri’ar mu Musulmai ne.

Ko za ki iya tuna shekarar da ki ka shiga harkar fim?
To shekarar da na shiga harkar fim dai ita ce shekara ta 2000, ka ga yanzu ina da shekaru 21 kenan a cikin masana’antar, kuma Alhamdu lillah, na yi gwagwarmaya sosai, na yi ayyuka da mutane da yawa, kuma fina-finan da na fito da farko akwai wani fim mai suna Feleqe wanda a wuri ɗaya aka nuna ni a matsayin ƙawar Amina Garba. Fim  ɗin Ali Indabawa ne. Bayan shi na yi Linzami da Wuta na kamfanin Sarauniya, sai na zo na yi Nagari, sai kuma Garwashi, sai kuma fim ɗin Mashi na kamfanin H R B kuma na yi fina-finai bayan waɗannn da yawa sosai tun a wancan lokacin wasu ba zan iya kawo sunan su ba, saboda sun yi shekaru, amma dai na yi aiki da kamfanonin fina-finai masu yawa.

To gwagwarmayar ki ta kasance a cikin masana’antar tsawon lokaci?
To zan iya cewa an sha gwagwarmaya abubuwa sun faru ma su kyau da marassa kyau, amma dai masu kyau ɗin sun fi yawa, don ka ga lokacin da na fara fim ba yarinya ba ce, don haka ban tava fitowa a budurwa ba, sai dai na fito a matar aure har ta kai na zo ina fitowa a matsayin uwa, kuma har yanzu matakin da na ke takawa kenan na uwa, sai dai ko na fito a matsayin bazawara.

Ko za ki faɗa mana irin nasarorin da ki ka samu a cikin harkar fim?
To nasara dai ta farko da na samu ita ce jama’a, don na samu arzikin jama’a na yi farin jini sosai duniya ta sanni saboda harkar fim ɗin Hausa da na ke yi, to ka ga wannan babbar nasara ce na yi fice na zama wadda kowa ya sani don duk in da aka ce Daso an sanni ni ɗin ce dai, kuma ga aikin Hajji na je sanadin harkar fim sau biyu ana ba ni kujerar Makka wanda su ka ba ni babu dangin iya babu na Baba sai ƙauna da kuma sanadin harkar fim ce duka ta janyo, sai kuma abin hawa duk Allah ya hore duk ta sanadin harkar fim, da sauran rufin asiri na rayuwa. Amma abin da ya shafi matsaloli, bai wuce kamar yadda mutane su ke nuna mana ƙyama ba saboda mu ‘yan fim ne don haka a ke yi mana kallon kamar mu wasu mutane ne na daban, ana cewa karuwai ne, da dai sauran su, amma dai ita karuwa dai suna ta tara, don akwai karuwa da ta ke zuwa ta kama gida ko ta kama ɗaki ko ta tafi ma gidan Magajiya, akwai karuwa wadda a cikin gidan uwar ta da uban ta ta ke yin karuwanci. To Wai mene ne karuwancin nan ma? Ina cewa a yi zina, shi ne karuwancin ko? Na ga dai waɗanda su ke gidan uwar su da uban su ma suna yi, su je su yi su dawo gida, don haka ni mutane suna ba ni mamaki domin duk jinsin da ka gani, akwai nagari akwai vatagari a cikin gidan kowa da akwai, saboda a iya baki a kuma kiyaye don haka a daina yi mana kuɗin goro ana aibata mu ana cewa ba mu da aikin yi, kuma ai ba sata mu ke yi ba, ba wani mugun abu mu ke yi ba, duk abin da mu ke yi saya ku ke yi da kuɗin ku kuna kallo, kuma ku yi mu’amala da mu, amma sai ƙyamatar ba za a ba su aure ba, kada a auro ‘yar fim, da sauran magana iri-iri, abin dai babu daɗin faɗa.

Ko harkar fim ta ba ki damar yin tafiye-tafiye zuwa wasu ƙasashe?
Sosai ma kuwa, domin na faɗa maka ta dalilin fim na je aikin Hajji, kuma na shiga ƙasar Nijer babu adadi, domin duk jihohin da ke ƙasar Nijer babu in da ban shiga ba, na je ƙasar Kamaru ta sanadiyyar fim, na je Ghana da ma wasu ƙasashen da ba zan iya tunawa ba, sai dai Allah ya ba mu sa’a, amma dai an yi tafiye-tafiye sosai, wasu a mota wasu a jirgi kuma Alhamdulillah har yanzu dai ana ci gaba da yi.

Saratu

Kina cikin fim ki ka yi aure, ko yaya rayuwa ta kasance miki bayan kin yi aure a matsayin ki na ‘yar fim?
To gaskiya bayan na yi aure a matsayina na ‘yar fim babu wani sauyin rayuwar da na samu don ina kallon kaina a matsayin matar aure ne, don haka sai na mayar da kaina kamar yadda matar da ta ke aikin asibiti tana da aure ko malamar makaranta to haka ni ma na ke gudanar da aiki na, don ko a harkar kasuwanci za ka ga mata sun tafi ƙasar waje sun saro kaya to ni ma haka zan fito na yi aiki na in dawo a wata ƙasar ko a wani garin, na gama kwanakin da zan yi na dawo gida na Lafiya to babu wani bambanci da ina da aure da ba ni da aure, kawai dai a yanzu zan tsare hakkin miji na ne a duk inda nake, don haka sai ma daɗi da na ke ji da kuma albarka da take ƙaruwa, don in dai mace za ta kare mutuncin ta tsakani da Allah, to babu wani abu, domin babu wani aiki a duniya da a yanzu babu matar aure a cikin sa don haka ban ga dalilin da zai sa a rinqa yin magana a kan wai mai aure bai dace da ta rinƙa yin fim ba.

Ko bayan harkar fim akwai wasu harkokin kasuwanci da ki ke yi?
To zan iya cewa akwai, don an ce sana’a goma maganin mai gasa, kuma zama waje ɗaya tsautsayi in ji Kifi, Kodayake wannan ba tsautsayi ba ne alheri ne, don haka bayan harkar fim ina tafiyar da harkar Gidauniyar tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi wanda ina da rajista da komai za ka ga ina saka abubuwan da na ke gudanarwa a shafukana na soshiyal midiya wanda mu na tallafa wa mabuqata da abinci da sauran kayan buƙatar yau da kullum, duk lokaci zuwa lokaci mu na gudanar da aikin da ya ke ba mu kaɗai mu ke samar da kayan ba, mu na samu daga wajen jama’a ko daga Gwamnatin tarayya ko ta jihohi, wani lokaci kuma zan fitar da kuɗi na na bi lungu da saƙo na sayi abinci na raba wa mutane duk wanda ya ke son ya ga irin ayyukan da na ke yi sai ya bi shafuka na zai gani. Kuma mu na bin gidajen masu taɓin hankali mu kai musu kayan sakawa da tabarma da ma duk wani abu da ya samu. Kai har ma sansanin ‘yan gudun Hijira duk muna kaiwa, sai dai a yanzu na ɗan kwana biyu ban fita ba, saboda abin ya ɗan yi ƙasa, don haka mu na roƙon jama’a da hukuma da su ci gaba da tallafawa wannan Gidauniyar wajen ci gaba da aikin lada da na ke gudanarwa.

To wani abu da na ga ki na yi a yanzu shi ne sanƙira za a kira abin, wato MC a gidan biki shi ma wannan wata harkar kasuwancin ne daban?
E haka ne ina yin harkar MC a gidan biki domin na nishaɗantar da jama’a, domin da yawa su na son su ga Daso ido da ido amma ba sa iya gani, da na fara yi kuma a nan mu ke haɗuwa da masoya a yi hotuna, don haka duk in da aka gayyace ni ina zuwa, don haka ina yin MC wato mai gabatar da taro zan kira abin kenan, don haka kowanne irin taro ne in dai an gayyace ni mun yi ciniki, ina zuwa na yi a kowanne gari ne har ma da ƙasar waje.

Wane buri ki ke da shi a rayuwar ki?
To burin da na ke da shi dai bai wuce cikawa da imani ba, ina fatan Allah ya yi mini kyakyawar ƙarshe, domin kuwa, daidai gwargwado Allah ya rufa mini asiri, kuma na ji daɗi gabas da yamma sai dai babu abin da ba za a rasa ba, wannan kuma na bar wa Allah shi ne kaɗai ya san sirrin ɓoye, don haka ni dai a yanzu fata na cikawa da imani.

Mun ga kin buɗe shafin ki na YouTube mai suna Saratu Giɗaɗo TV  shi ma wani ɓangare ne na kasuwanci ki ka fara?
To dayake komai ya na tafiya da zamani, duk in da wani abu na ci gaba ya zo to ba kamata a bar mutum a baya ba, kuma Alhamdulillah ina da ilimin da zan hau kan Computer, ina da waya ta da zan shiga  Internet to ka ga ba zan bari a bar ni a baya ba, don harkar YouTube ba sai yara ba, to wannan shi ne dalilin da ya sa na buɗe, don ya zama ina yin wasu abubuwa ina turawa, kamar abin da ya shafi fim da kuma wasan barkwanci da na ke yi, da kuma harkar Gidauniya ta duk ina sakawa wannan shi ne dalilin buxewa.

Wanne kira za ki yi ga mata ‘yan fim a game da rayuwa a yanzu?
To kiran da zan yi musu dangane da rayuwa a wannan lokacin shi ne su rinƙa riƙe mutuncin su kawai, duk wata mace da ta ke cikin harkar fim ta san cewa ita mace ce kuma uwa ce wata rana, idan yanzu ki na kallon ke budurwa ce to wata rana za ki wuce wannan matakin, kuma akwai tarihi na rayuwa ya na nan ajiye duk abin da ki ka yi, don haka a rinqa yin shiga ta mutunci a fili da kuma cikin fim ku rinqa kalamai na tarbiyya wanda zai nuna daga gida ku ka zo da tarbiyyar ku mai kyau, don haka yara mata da su ke cikin harkar da kuma masu shigowa, a bi a hankali, duk wani abu na zubar da mutunci kada a yi, domin tarihi ya na nan ajiye, ko da kin bar harkar nan gaba duk abin da ki ka yi mai muni ya na nan ajiye, don haka da masu yin tsiraicin nan da samarin su su ke saka su don su tura musu ta waya ku rinƙa kiyayewa domin ana ruɗar ku da kuɗi a zubar muku da mutuncin ku.

Mene ne saƙon ki na ƙarshe?

To saƙo na na ƙarshe dai shi ne ina godiya ga masoyan mu a duk in da su ke a duniya, domin su abin alfahari ne a gare mu, mu na godiya Allah ya bar mu tare da ku mun gode sosai. Alhamdu lillahi.