Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Shugaban mulkin Soji, Yakubu Gowon ya bayyana yadda ya roƙi marigayi Sani Abacha kan ya ƙyale Obasanjo da rai.
A shekarar 1995 ne gwamnatin Abacha ta kama Obasanjo bisa zarginsa da laifin shirya juyin mulki. Daga bisani a shekarar 1998 aka sako tsohon shugaban ƙasar
Shekara ɗaya bayan haka ne, Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a ƙarƙashin jami’yyar PDP.
A lokacin da ya ke magana a taron haɗin kan kiristoci game da bikin Kirismas a Jos, Gowon ya hakaito yadda ya rubuta saƙo ga Abacha akan rayuwar Obasanjo, ya na mai cewa ya shiga ƙunci game da halin da Obasanjo ya ke ciki.
Akan haka ne ya ɗauki matakin rubuta saƙon magiyar, sannan kuma ya ce sun cigaba da addu’o’i kan kada a aiwatar da hukuncin kisa ga Obasanjo a lokacin.