Atiku da Obi sun musanta ganawa don yin takara tare a 2027

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a 2023, Peter Obi, sun musanta jita-jitar cewa suna tattaunawa kan haɗa kai don tsayawa takara a zaɓen 2027.

Wannan ya biyo bayan hotunan Atiku da Obi da aka gani suna tare yayin karin kumallo a gidan Atiku da ke Jihar Adamawa, wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta. Atiku ya wallafa bidiyon ganawar a shafinsa na X ranar Asabar, inda aka nuna su tare da wasu mutane suna zaune a teburin cin abinci.

Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana cewa ganawar ta kasance wata haɗuwa tsakanin abokan juna. Ya ce Obi ya halarci bikin cika shekara 20 na Jami’ar AUN da kuma ranar tunawa da kafuwarta ta, wanda Atiku ne ya kafa. Ya ƙara da cewa “Abokai ba su rabuwa saboda siyasa.”

A nasa ɓangaren, mai magana da yawun Obi, Ibrahim Umar, ya musanta cewa taron karin kumallon yana da alaƙa da shirye-shiryen siyasa. Ya ce Obi kawai ya amsa gayyatar Atiku don gabatar da jawabi a bikin, kuma babu wani alaƙa da batun siyasa. Ya ce, “Abun na bashi dariya in mutane na ganin siyasa a duk wata ganawar manyan ‘yan siyasa.”