Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Shugaban ƙungiyar direbobi na ɗaya a ƙaramar hukumar Mokwa da ke Jihar Neja Malam Abubakar Ahmed ya nuna damuwarsa bisa ga yadda jami’an tsaro musamman sojoji ke tursasawa direbobi da ke sufuri a kan babbar hanyar da ta haɗa Arewa da Kudancin ƙasar nan wajen karɓar kuɗi babu ƙaƙƙautawa.
Malam Abubakar Ahmed ya yi wannan koken ne a garin Mokwa ranar Talatar da ta gabata lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke garin Mokwa.
Shugaban ya bayyana cewa yanzu haka direbobi suna nuna damuwarsu bisa ga yadda jami’an tsaro ke tursasa musu wajen karɓar kuɗi hannunsu inda yanzu har ta kai ga sojojin ba sa karɓar kudi kasa da naira dubu daga hannun direbobi musamman na manyan motoci da suka soma daga Dogonbaro zuwa manyan motocin ɗaukar kaya. Wani lokacin ma ta kan kai ga harbi idan aka hadu da direban da ya ki yarda da ya ba su kudin da suka nema hannunsa idan aka soma rigima da shi.
Ya bayyana cewa ba wata kungiyar a kasarnan da ta kai kungiyar direbobi bayarda kudin shiga ga gwamnatin tarayya sannan kuma a ce kowane direba ya dauko kaya ya soma rabon kudi a kan hanya kenan.
Malam Abubakar ya kuma nemi gwamnatin tarayya da ta gyara musu wannan hanyar da ta hada arewaci da kudancin ƙasar nan musamman a jihar Neja inda a nan ne ta fi muni da ta kai ga sai da yawa idan aka sami hatsari ko lalacewar wata babbar mota a hanyar wadansu motoci kan iya kwashe sati daya a hanya ba su isa inda za su je bawanda sai da yawa ya kan haifarda hasara mai yawa.
Haka-zalika Shugaba Abubakar Ahmed ya ja kunnen direbobi da su kiyaye hakkokan da suka rataya a wuyansu na kare rayukan fasinjojin da suka dauka a motocinsu. A duk lokacin da ka ɗauki fasinja a mota to rayuwarsa tana hannunka saboda haka a rinka tuki da kulawa a daina shaye-shaye da tukin ganganci da waɗansu ɗabi’u na banza musamman a lokacin da ake tuƙi.