Yadda tsadar rayuwa ke janyo lalacewar tarbiyya

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Da fatan mun same ku lafiya, a wannan mako. Yau za mu yi magana a kan tsadar rayuwa da muke fuskanta ta ko’ina. Ita ma ta ba da gudunmowar taɓarɓarewar tarbiyya. Saboda sai da akwai arziki kowa ke iya rayuwa cikin farin ciki. Yanzu abin da za a ci ma nema yake ya gagari mutane. Talaka na ganin rayuwa! Kana so ka yi abu ba dama, saboda rashin kuɗi.

Kafin goma ta shigo maka hannu, wallahi Naira ɗari ta fita daga hannun ka. Ba a ma ta sauran abubuwa kowa ta abin da zai ci yake yi. Abinci ya fara zama zuma. Idan ana ci sau uku a rana, yanzu fa ba dole ne a ci sau ukun ba. Hatta yara sun fara laƙantar cewa, ba fa rayuwar da suka saba ba ce yanzu.

Saboda haka, da mazaje da matayen, da yara kowa sai ya yi haƙuri, saboda kowa ba yin kansa ba ne.

Ana fita nema, amma ba dole ne, idan an fita a samo ba. Idan kuma an samo, to sai an yi haƙuri. Don yanzu ba kowanne gida ke rayuwar ci a ƙoshi ba ne, ana dai turawa don a zauna lafiya.
 
Yanzu ne uwargida za ta nuna jarumta ta ganin komai mai gidan ya kawo, sai an yi masa uziri, a karɓa da haƙuri, da nuna farin ciki, don Allah. Ba wai ki tashi fitina ba ke wanan ya yi kaɗan ba. Ko ki ce ke ba za ki ci wannan ba sai abunda ranki yake so. An wuce gurin yanzu komai aka samu karɓa ake da haƙuri. A yi godiya da addu’ar Allah ya cigaba da dafa wa mazanmu. Amma idan kin ce faɗa da mita za ki yi yar uwa, da sauran aiki a gabanki. Don kuwa kullum cikin takaici da ɓacin rai za ki zauna.

Yanzu yadda komai ya lalace mata sai mun ta karkato da hankalinmu jikinmu, mun duba yadda yau ɗin take gyarawa. Sannan za mu faɗakar da yaranmu su ma su san rayuwar don Allah. Saboda shi fa yaro kullum burin sa a ce akwai. Ba ya so a ce masa babu. To idan ba a nuna masa babun ba, to haka zai yi ta tafiya har dai ya tashi da wannan halin ya zame muku ƙarfen ƙafa.

Yaro fa yanzu ɗan shekara bakwai ko ma ƙasa da haka, ya san kuɗi, ya san jin daɗi, ya san abinci mai daɗi, da mara daɗi. Kowanne kika ba shi in har kin koya masa, zai amsa. Amma in kin saba ba shi mai daɗi, kika ba shi mara daɗi, wallahi ba zai karɓa ba.

Shi ya sa ko kina da shi, watarana kawai ki ce masa babu. Saboda ya tashi da sanin ba komai ake nema a samu ba. yaran yanzu in kin musu abinci ba nama ba za su karɓa ba sai kin yi da gaske. Saboda sun riga sun saba. Da ma haka ake ba su. To yanzu kowanne gida ne za ki samu abincin ba nama, ɗai-ɗai ne suke sa wa, Allah ya sa mu dace.

Tun daga yanzu ne uwa zata fara gyara gidanta da rayuwar yaranta. Wallahi duk yadda muke zato da, abun ya shallake. Nema yake komai ya fi ƙarfinmu, wanda Ba ma addu’ar hakan.Yanzu sai ki tashi ki nemi Naira hamsin ki rasa. Saɓanin da ba ruwanki. Kin ga ina ga yaro da ya saba shi kawai a ba shi. Idan ba a ba shi ba, komai yana iya faruwa, wanda ba a buƙatar hakan.

Shi ya sa ita uwa komai ake cewa ita ce, ba don komai ba sai don ita ce mai ba da tarbiyya. Da zarar yara sun yi ba dai-dai ba, ita za a ce. Saboda ita ce mai zama da su. Ke kika san zafin su fiye da uba da shi sai ma kwanciyar bacci. yana gidan ma wallahi sai ya ga dama zai ba da kulawar, saboda shi bai saba ba. Kuma shi harkar fita nema ta fi masa komai fiye da sa ido a kan gidansa.

Maleji; Yanzu duniyar ta canja, komai ba a samun sa ta sauƙi sai an sha wuya. Ta abinci ake duk sauran abubuwan buƙata na rayuwa ya yi wuya, kullum farashin kaya daɗa sama suke yi. To ba dole mu sauke wa kai buri ba?

Rainuwa: Ɗaya daga cikin abunda ke haddasa fitina a rayuwar auren yanzu muddin za a ba ki ki raina, to ki sani kun ɗaura rashin zaman lafiya da miji. In kin yi wasa ma, wallahi daina nemowa zai yi. Eh mana. Ya kawo, kin ƙi nuna bajintar sa kin bi shi da mita da maganganun da za su dama masa lissafi. Kin ga kin ja wa kanki rashin girma da kuma imani.

Saboda shi gani zai yi ba ki san babu ba, kuma ba ki da imani. Ba ki san ta yaya ya samo ba, kuma ya kawo kin raina. Kin ga ba daɗi, dole kuma ku samu matsala. Da kanmu mu mata muke rusa zaman lafiya a gidajenmu. Yana da kyau mu yi wa juna uziri a rayuwa. Yanayinki kaɗai ya isa ya sa miji ya san ke mai kwantar da zuciyarsa ce ko baƙanta masa.

Duniya faɗi gare ta, amma matsalolinta sun sha kan kowa. Wallahi babu babba, babu yaro. Allah ya sa mu iya ba wa yaran mu tarbiyya ta gari. Tarbiyya ita ce mai wuya kuma aba ce mai da]i. Idan ka yi sa’ar tarbiyyantar da yara, to ka gama. Kowa sha’awarsu zai yi. Amma idan kin ce sai yadda suke so za ki yi, ki sa musu ido, to dukkanku kuna cikin muguwar ɗabi’a ta fuskantar ƙalubale a rayuwa. Shi ya sa masu magana ma suka cewa, ka so naka, duniya ta ƙi shi. Ka ƙi shi kuma, duniya ta so shi. Ka ga ka zaɓi duniya ya fi naka. Sai mun cire son rai, sannan mun kau da kai mun nuna wa yara cewa ba kallon su muka zo yi ba.

Mata iyaye ne, kuma ƙawaye ne, abokan rayuwa ne. Su ne kan gida, dole tafiya sai da su. Maza iyaye ne kuma abokan shawara. Dole sai an tallafi juna, an kyautata wa juna.

Yanzu tarbiyya ta yi wuya, sai an yi jan ido.Yaran yanzu duk da wayo wallahi za su iya sai da iyaye ma. Eh mana, to ita uwa ta yi galau ita yaranta nagari ne ba ta san suna can suna rusa tubalin da ta fara ginawa ba. Idan Allah ya taimaka ta farga da wuri ta gane, to da sauƙi. Idan kuma ba ta sani a kan lokaci ba, to sai dai addu’a. Don yanzu wallahi yara sun fi iyayensu wayo. A gidan ma fitina suke ba ki sani ba. Saboda haka, don Allah mu sa ido sosai wallahi.

Waya ta riga ta gama rusa tarbiyya, babu babba, ba yaro. A ciki ma wasu abubuwan ake koya. Ya ilahi! Don me iyaye suka sakarwa yara ‘yan ƙasa da shekara ashirin waya to kuwa dole ɓarna ta yi yawa kuma ba gata ba ne. Wanɗanda ma suke da manyan shekaru yaya aka cika, balle yara? Wallahi akwai gagarumin aiki a gabanmu wanda Allah ne kaɗai zai fidda mu.

 Sannan sabuwar masifar da ta tinkaro mu ita ce ‘TikTok’. Wannan ta sako mu a gaba ta fara zama shaiɗanci. Don kuwa yanzu ta haɗe manyan mata da yaran mata a fito ana rawa da waƙoƙi da shiga ta rashin ɗa’a da ladabi, a tura duniya ba kunya ba tsoron Allah. Iyaye sai su fito suna nuna halittarsu ba sa tunanin shekarunsu da yaransu da surukansu. Abun da ya zama abun takaici, tsohuwa ta fito tana karairaya wai ƙara’i take. Hasbunallahu wa ni’imal wakil! Zub da mutuncin ya yi yawa, wallahi.

Ba cinyewa ba ne, rashin daraja ne da rashin kama kai. Su ma yaran matan haka suke yi. to a garin yaya za a samu abokin rayuwa nagari? Kin fito kina nuna tsiraici ga duniya da sunan burgewa. Ba ki san kuma lalata rayuwarki kike ba. Don wallahi namijin arziki ba zai zaɓe ki a matsayin mata ta gari ba. har ya sa ran zai samu yara a gurinki. Ke ma tarbiyyar ba ta ishe ki ba, balle ki ba wa ɗanki.

Mata mu farka! Mu san wannan duniyar ba matabata ba ce. Idan yau mu ne, gobe fa?

Yana da kyau mu san me muke yi don Allah. daga na gaba ake gane zurfin ruwa. Allah ya sa mu gane insha’Allahu sati na gaba za mu kawo wani sabon maudu’in. Abun da muka yi na daidai, Allah ya gyara mana.

Ku ci gaba da kasancewa da jaridarmu mai farin jini, da ilimanta wa, Manhaja. Wa’assallam.