Yadda ’yan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 25 da su ka haɗa da hakimi da kuma wasu sarakunan gargajiya a Ƙaramar Hukumar Bukkuyyum da ke a Jihar Zamfara a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

‘Yan bindigar dai sun afka ƙauyen Ganar Kiyawa ne a ranar Lahadi kuma suka kashe mutanen, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.

Mutanen garin sun ce ‘yan bindigar sun shiga garin na Ganar Kiyawa ne saman babura, kuma bayan mutane sun tsorata sun fara tserewa, ‘yan bindiga suka dinga harbinsu, cikin waɗanda aka kashe har da hakimin garin Bala Muhammadu da Magajin gari Sani Salihu da wani bafade da ake kira Sharu.

“Da ni da Hakimi da Magajin Gari mun yi gudun kilomita uku, kuma da suka cimma Magajin Gari suka tambaye shi me yake wa gudu ya ce wahala, sai suka ce to ta qare, suka harbe shi,” a cewar wani mazauni garin da yake bayar da labarin da ‘yar magajin garin da aka kashe ta faɗa masu bayan sun tsira.

Ya ce sun samu gawar mutum 25 da maharan suka kashe, kuma ana ci gaba da binciken wasu gawawakin a daji.”

Ya ce an yi wa gawar mamatan sallar jana’iza ne a garin Adabka. Ya ce adadin na iya ƙaruwa saboda har yanzu akwai mutanen da ba a gani ba.
Maharan sun tarwatsa garin Ganar Kiyawa, inda dubban mutane suka tsere zuwa wasu ƙauyuka maƙwabta.
Hakimin Adabka ya shaidawa BBC cewa mutanen da ke cikin garinsa sun kai kusan mutum 3,000.

A cikin wata sanarwa bayan kai harin, gwamnatin jihar Zamfara ta jajanta wa mutanen garin tare da bayar da umarnin kai masu tallafi.

Mazauna garin Ganar Kiyawa sun daɗe suna fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a kwanakin baya-bayan nan.
Sun ce sun biya kuɗi kusan miliyan uku da ‘yan bindigar suka tilasta masu.

Wani mazaunin garin wanda ya ce an kashe masa ‘ya’ya bakwai ya ce: “mun biya Naira kusan miliyan uku na fansa da suka ce dole sai mun biya.”

Da farko ya ce maharan sun fara kore shanu ne daga baya suka dawo suka sake shiga gidaje suka ce sace mutane suka ce dole sai an biya kuɗi miliyan uku da wasu dubu ɗari.

Mutanen garin sun ce duk da sun biya kuɗin amma ba su iya barci cikin kwanciyar hankali.

Tun watan Janairu jami’an tsaro ke kai farmaki a yankin domin kakkaɓe ‘yan bindigar.

‘Yan bindiga da ke ɓuya a dajin Gando sun daɗe suna kai hari a ƙauyukan ƙananan hukumomin Bukkuyyum da Anka.

Jihohin Arewa maso yammaci na Zamfara da Kebbi da Sakkwato sun daɗe suna fuskantar hare-hare na ‘yan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa.