Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (2)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata mun kawo wa masu karatu bayyanin yadda matsalar kogon haƙora ke samun gindin zama da kuma yadda mu ke zafafa ta ba tare da sanin mu ba.

Kazalika mun tavo asalin cutar, kafin mu kawo wasu daga cikin hanyoyin da za a magance matsalar.

A wannan satin da yardar mai dukka, za mu ci gaba daga inda mu ka tsaya.

Amfani da gishiri:

Kasancewar gishiri na ɗauke da sinadarai da ke kashe ƙwayoyin cuta da kuma gyara ɓarnar da suka yi ta hanyar waraka ne ya sanya ya shigo cikin jerin ababen da ke iya yaƙar cutar kogon haƙora.

Don haka ga wanda yake fama da wannan matsalar zai iya zuba babban cokali ɗaya na gishiri a ruwan ɗumi, sai ya juye ruwan a bakinsa, tsayin mintina biyu, yayin da zai fi bai wa gefen da matsalar ta ke ƙarfi, ta hanyar juya kansa ta ɓangaren, don ba wa ruwan gishirin damar shiga wurin su gudanar da aikinsu. Ana maimaita wannan sau uku a kowacce rana.

Wata hanya kuma ta amfani da gishiri a wannan matsala ita ce, matsa rabin lemun tsami ƙarami cikin ɗan man zaitun (kaɗan shi ma), sai rabin cokali na gishiri.

Za a haɗe su sosai, kafin a shafe ɓangaren da matsalar ta ke a haƙoran, tsayin mintuna uku zuwa biyar, ya danganta da yanayin nisan matsalar. Sannan ki wanke bakin da ruwan ɗumi. Shi kuwa wannan haɗin an so ka yi amfani da shi sau biyu a rana.

Amfani da tafarnuwa:

Tauna ɗanyar tafarnuwa a ɓangaren da matsalar kogon haƙora ya samu na bada sakamako cikin ƙanƙanin lokaci, kasancewar tafarnuwa na ɗauke da sinadarai masu yawa da ke hana ƙwayoyin cuta rawar gaban hantsi, kuma su warkar da matsalar da ta samu kafin zuwan su.

Tafarnuwa ta kasance ɗaya daga cikin manya a layin magunguna da suka shafi haƙora, kuma tana ƙara wa haƙora da dasashi lafiya, ta kawar da zafin haƙora tare da hana shi disashewa.

Bayan wannan, ana amfani da tafarnuwa tare da gishiri don samun waraka daga kogon haƙora.

Za a samu tafarnuwa uku zuwa biyar (ya danganta da nisan matsalar), a daka ta, sai a zuba gishiri ƙaramin cokali ɗaya, a haɗe su, kafin a sa a inda kogon yake, tsayin mintuna 10, sannan a wanke da ruwan ɗumi.

Ana maimaita wannan sau biyu a rana. Da yardar Allah za a ga sakamako cikin sati ɗaya.