Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Barka da wannan lokaci Malama Aisha. Allah ya yi jagora. Na karanta wasu daga cikin shawarwarin da kike ba wa ‘yan’uwa a jaridar Manhaja, sai na ce tunda dai Ina da lambarki bari na turo da tawa matsalar a nan.

Tun ina ɗan shekara tara na fuskaci wata matsala, inda kawuna ya yi lalata da ni. Kawuna na zaune ne a gidanmu, kuma yana sona sosai da siya min duk abinda ya gani na yara. Wannan dalilin ne ya sa kowa gidanmu yake kirana ɗan kawu.

Da ya dawo gida zai kaiko kirana in same shi ɗakinshi da ke ƙofar gida, wanda ƙofarshi ke a waje. Ni mamanmu ke ba abincinsa da komai nashi in kai masa.

To, tun da ya yi wannan lalata da ni a wata safiya da na je kai masa kalaci, sai na fara gudunshi. Idan ya aiko kirana sai na ƙi zuwa. Bazan manta ba, mamanmu ta taɓa yi min dukan tsiya kan ya aiko kirana na ƙi zuwa, a ranar da kanta ta raka ni ɗakin shi, ta kuma tilasta min kwana gurin sa. Kuma ba irin abinda bai yi min ba.

To yanzu na girma, na isa aure, kuma ina sana’ata daidai ina samun abin da ya isa na yi aure, to amma duk lokacin da na ga macen da na ke so muka fara soyayya da zaran na yi tunaninta a shimfiɗata sai inji ta fita raina gabaɗaya haka alaƙar za ta ruguje. Kuma ba wai bana sha’awa ba, har mafarki ina yi, kuma ina ɗan kallon nan da samari ke yi don rage zafi.

Har zargin na yi ko maza na ke so, don jin da na yi ana cewa, duk wanda aka yi wa wannan abin sai ya yi, to har gwada alaƙa na yi da wani, amma yana matsowa kusa da jikina wallahi sai na ji tamkar an kusanto ka da wani abin ƙyama, nan da nan tsoro ya rufe ni.

Matsalar dai ita ce gida an taso ni a gaba, dole sai na yi aure, ban san ta yadda zan iya faɗa masu matsalata ba, kuma a yadda na ke ji, bana jin zan iya haɗa jikina da wata ko wani don yin wannan alaƙa. Zan so ki bani shawarar hanyar da zan bi. Na gode.

AMSA:

Cin zarafi ta fuskar jima’i na layin farko da masana hallitar ɗan adam da kuma likitocin ƙwaƙwalwa suka yi matsaya ɗaya kan cewa, yana layin farko a nau’ukan cin zarafi da illarsa ba iya gangar jiki ta ke tsaya wa ba. A lokacin da aka tursasa wata hallita kan abinda ya shafi sha’awa, musamman ga ƙananen yara, wannan tsoro da za su ji a lokacin da ake masu fin ƙarfin, yana da reshe biyu.

Na farko tsoron abin wanda ya kasance baƙon abu da ba su san da zaman sa ba, sai kuma tursasawa zuwa ga abinda zuciyarsu da gangar jikinsu ba ta so.

Sha’awa ko ga baligi aba ce da ke zuwa da amintar mai ita, wanda wasu masana suka ce asalinta daga ƙwaƙwalwa ce, yayin da ta ke tafiya tare da saƙon zuciya. Saukarta lokuta da dama yakan samo asali ne daga ɗarsuwa daga zuciya zuwa ƙwaƙwalwa, da wannan ne wasu suka ba wa maniyi muhali, inda suka ce saukar sha’awa zuwa wani ƙashin baya ne ke haifar da maniyi, wanda sha’awar ce ke tunkuɗo shi zuwa mara.

Yayin da wasu ke ganin ana hallitarshi ne daga ƙirjin ɗan adam kafin ya koma gadon baya, zuwa mara. Koma dai wane ne, sha’awa aba ce da ke zuwa tare da ra’ayin mai ita. to a lokacin da aka tursasa mutum kanta zai zama matsala, ita wannan matsalar kan haɗe da wancan nau’ukan tsoron biyu da muka faɗa, su zama tamkar wani asid, su ɗiga a wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke da alhakin kula da damuwa, wanda hakan zai haifar da disorder ma’ana ‘yar ƙaramar hauka.

Ita wannan haukar ba kowa ne zai iya gane wani na da ita ba, asalima ko masu ita wani sain sai an ankarar da su, domin bata taɓa hankali na mu’amallat na ɗan adam, duk wanda zai yi mu’amala da kai, zai ga cikakken mai hankali, sai dai idan ya shiga ɓangaren da ya shafi sha’awa ne za kafahimci yana tare da matsala, domin zai iya dawo da irin yanayin tsoro da yake shiga a lokacin da ake yi masa da ƙarfi, ko ya shiga tashin hankali da har zai iya sumar da shi, ko ya sanya shi ya kai wa abokiyar tarayyar ta sa duka a ƙoƙarin kare kansa, duk da cewa a wannan lokacin ba ƙarfi ake ƙoƙarin nuna masa ba.

A kwai wasu hanyoyi da dama bayan waɗanan da waɗanda aka ci zarafi ke bayyana matsalarsu.

Da yawa musamman ma a mata cin zafari ta fuskar saduna kan zama silar rashin jin daɗin zamantakewar aure gare su, domin lokuta da dama ko sun yi nasarar cire tsoro, rashin son alaƙar zai tsaya a zuciyarsu, wanda hakan zai hanasu jin daɗin shi. Dalilin rashin bin dokokin magance wannan matsala.

Abin da zan fara faɗa kan matsalarka ita ce, kaso mai ɗan nauyi na cin zarafin da ake yi wa yara ta fuskar fyaɗe za ka samu akwai laifin iyaye a ciki, ba wai su ke sa a yi masu ba, sai dai rashin kulawarsu lokuta da dama takan kai yaran ga irin wannan.

Wajibi ne a wajenku, musamman ma ke uwa, ki saka ido akan lamain ‘ya’yanki fiye da kowa. Zamani ya canza, haka mutanen da ke ciki sun lalace, babu wanda za ki iya yarda ɗari bisa ɗari ba zai iya lalata ma ki ‘ya’ya ba, hakan zai sa duk wata kafa da kika gani, ki yi saurin leƙawa, don tabbatar da ba wai cutar da ‘ya’yanki ba ce.

Ba wannan ne karo ne na farko da na ci karo da labari irin na ka ba, wato na cin zarafin ‘ya’ya a ƙarƙashin hancin iyayensu, don haka zan yi amfani da wannan damar wurin kira ga iyaye, musamman mata da su ba wa ‘ya’yansu kariyar da suke buƙata.

Yaro na da rauni, ba shi da wani ƙarfi sai na iyayensa, idan kuwa kuka kawar da ido, duk abin da ya zo ma shi ba zai iya kare kansa ba.

A lokacin da ɗanki ya fara gudun wani da yake so da zumuɗin zuwa wurinsa, ko da kuwa mahaifinsa ne, ya kamata ki tambaye kanki dalilin da ya sa ya yi hakan, domin an ce ruwa ba ya tsami banza.

Akwai hanyoyi da dama da ke uwa za ki fahimci ana cin zafarin ‘ya’yanki ta fuskar fyaɗe, ba sai ke jira sun sanar da ke ba, wanda ba lallai ba ne su yi hakan, duba da wasu lokuta su masu aikata hakan gare su na masu barazana, ko kuma su yaran su ji tsoron abinda ku iyaye za ku yi masu idan sun sanar da ku abinda aka yi masu. Ba na so in saki layi, don haka ba zan zurfafa wurin kawo ma ki alamomin ba, sai dai za ki iya samun saninsu cikin sauki, ta kafofi da dama.

Mataki na farko na samun mafita a kan matsalarka ɗan’uwa ka riga ka ɗauke shi, wato bayyana abin da aka yi ma, wanda masana suka ce shi ne hanya ta farko da ke sasauta raɗaɗin cin zafari, wato samun wanda za ka gaya ma abinda aka yi ma. Duk da ba iya nan zai tsaya ba, za mu ci gaba da tataunawa da kai, tanan za ka samu damar faɗar duk abinda yake ɓoye da ke cin zuciyarka kan al’amarin.

Mataki na biyu, kamar yadda masana suka faɗa shine, renon ƙwaƙwalwarka akan bambancin da da yanzu, ma’ana bambance mata matsayin da kake a yanzu, wanda ka kawo shekarun da ba mai iya fin ƙarfinka, kuma duk wadda za ka kula don sha’awarta ce ta matso kusa da kai, ba don ta cutatar da kai ba.

Mataki na gaba shine, ba wa zuciyarka dama ta zavo matar da ta aminta da ita. Ka kuma buɗe mata ƙofa ko ta yi nasarar samun muhalli a cikinta, wanda hakan ma wata waraka ce za ka iya samu cikin sauqi, saboda soyayya tsakanin mabanbantan jinsi, ma’ana mace da namiji waɗanda ba muharraman juna ba, na ɗaya daga cikin magunguna da ke warakar da irin wannan matsala, domin son da za ka yi zai iya yaƙi da ƙwaƙwalwarka da ke sanar da kai duk wanda ya nufo ka da wannan alaƙa zai cutar da kai ne, kuma da taimakon zuciya, za ta bambanta ita wadda kake so da sauran mutane, wanda hakan zai iya sa a hankali ka fitar da ita a jerin waɗanda ke ganin wannan taɓin hankalin naka.

A matsayinmu na Musulmai, zan iya cewa a wannan kafa ba ka da mafita face auren, kuma Ina mai tabbatar ma idan ka yi dacen matar da ke sonka kuma ta kirki, za ta taimaka ma wurin taka matakalan waraka har zuwa idan za ka samu rabuwa da damuwar ba tare da ta gajiya ko ta nemi ta ma abin da aka yi ma a baya ba. Domin mata sun fi maza haƙuri ta wannan ɓangaren.

Baya ga haka, akwai buƙatar sanin ko akwai wata cutarwa da wannan cin zarafi ya haifarma na daga lafiyar jiki. Domin a ɓanagen maza, wannan matsala na iya haifar da rashin ƙarfi ko wata cuta da za ta iya kawo rauni a zaman aure, kamar yadda a wurin mata ma akan samu wasu matsaloli ta sanadiyyar fyaɗen. Don haka akwai buƙatar sanin ko akwai matsala a wannan ɓangaren don magance ta.

Ɗan’uwa ba zan ce ma matsalarka mai wucewa ba ce cikin ƙiftawar ido ba, asalima wasu sukan ɗauki tsayin lokaci duk da cewa suna bin dokokin kafin su samu sauki. Don haka ka ɗaura aniyar ganin bayan matsalar duk inda za ta kai ka, domin wasu da sun samu sun kusanci mace sau ɗaya matsalar ke barin su kamar fitar aljani, wasu kuwa suna jimawa kafin zuciyarsu ta natsu su daina jin tsoro da tsanar da suke yi wa abin.

Daga ƙarshe zan ce ka guje wa bin ‘yan hanyoyi don kawar da sha’awa, wato istimna’i (wasa da al’aura) saboda da yawa cikin mata da maza da aka yi wa fyaɗe na ɗaukar wannan hanyar a matsayin mafita ga matsalarsu, a ganinsu ba sai sun kusanci wani ne za su iya samun biyan buƙata ba, don haka sai su auri kansu don kauce wa shiga mawuyacin hali a yayin da suka kusanci ɗaya jinsi.

Sai dai ko kaɗan wannan hanyar ba ta zama mafita, musammam ma ga maza, domin jimawarka a cikinta irin illar da za ta yi wa ƙarfinka, sai kaga ko ka bar ta kana fuskantar rashin kuzari, shekaru kaɗan idan ka ƙara, sai ka koma sai da taimakon magani za ka iya yin wani abu.

Dukka waɗannan hanyoyin za su yiwu ne ta neman taimakon Allah, don haka addu’a ce jagaba a duk matakan warakar da muka lissafo. Ka tsarkake kanka daga laifukan da ka ambata kana yi, kafin ka nemi mafita daga mahaliccinka. Tabbas zai ji kukanka.

Ku aiko da tambayoyinku ta [email protected] ko [email protected]