Tare da AMINA YUSUF ALI
Masu karatu barka da wannan lokaci. Ina ƙara godiya ga waɗanda suka kira ni a waya da waɗanda suka yi tattaki suka zo don yi min ta’aziyya da taya ni jimamin rasuwar mahaifina Sheikh Dakta Yusuf Ali.
Allah ya jaddada masa rahama ku kuma Allah ya bar zumunci da qauna kuma ya saka muku da alkhairi. A makon da ya gabata mun fara tattaunawa a kan yadda soyayya take mutuwa bayan aure da kuma dalilan da suke sakawa hakan ta faru.
Sau da dama za ka ga an yi auren soyayya sosai amma sai ka da ɗan lokaci ya ja a zaman auren sai ka ga soyayya ta yi ɓatan dabo an neme ta an rasa. Duk da dai mun faɗi wasu daga dalilan a makon da ya gabata. Kuma mun fara kawo muku wasu dabarun warware hakan. Masu karatu ga ƙarin wasu dabarun da za a bi a samu soyayya ta cigaba ɗorewa har bayan aure, har ma gaba da Mahadi. A sha karatu lafiya.
- Hanya ta takwas ita ce, toshe kunne daga zuga: Idan ma’aurata na so soyayyarsu ta ɗore sai sun kiyaye shigo da mutum na uku cikin alaqarsu. Wato dukkan abinda ke tsakaninsu su bar shi tsakaninsu. Kusan kowaɗanne ma’aurata suna fuskantar zuga daga ɓangarori da dama. Walau daga dangoginsu ko abokanai. Sai dai kuma ma’auratan suna da zaɓi a kan su bar zuga ta shafi rayuwar aurensu ko a’a. Dole ma’auratan da suke son soyayyarsu da zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa tsakaninsu. To sai sun ɗaura ɗamara sun toshe kunnuwansu daga gulmammaki da zuga daga mahassada kuma maƙiyansu na voye.
- Yin biyayya da girmama ra’ayin juna: In dai abokin rayuwarka/ ki ba a kan wata mummunar hanya yake ba, bai kamata ka yi ƙoƙarin canza shi ƙarfi da yaji ba. Kodayake ma idan zaman ya yi zama halaye sukan saci junansu. Maimakon abokin zama ya dinga yi wa abokin zama ƙorafi da faɗa a kan ya canza wata ɗabi’a (In dai ba mummunar ɗabi’a ba ce). Kawai gara ya dinga nunawa a aikace idan an dace sai ka ga a hankali ya canza. Idan bai canza ba, a taya shi/ita da addu’a. Kyarar masoyi/ko masoyiya kan sa ƙimarka ta ragu a zuciyarsa/ta. Idan masoya na so soyayyarsu ta ci gaba da bunƙasa, to a guji kyara.
- Ƙoƙarin fahimtar juna da kyau: Wajibi ma’aurata su yi ƙoƙarin fahimtar halayyar juna da kyau kafin da bayan an yi aure. Ana so ma’aurata su fahimci dukkan abubuwan so da ƙi na abokin rayuwarsu. Kuma fahimta ta sosai. Hakan shi zai sa soyayyarsu ta tafi ba tangarɗa. Rashin fahimta na haddasa ruɗanin da zai iya sanya rikici a rayuwarsa. Wanda ka iya yin tasiri wajen varar da soyayyarsu. Saboda rashin fahimta kan haddasa zargi da sauran makamantansa.
- Ba da sarari: Sarari yana da matuƙar muhimmanci a soyayya. Musamman a soyayyar ma’aurata. A nan ya kamata mu yi tunanin me ya sa lokacin suna saurayi da budurwa ko bazawara da bazawari sun fi ɗokin juna a kan bayan sun yi aure? Amsar ita ce sarari da tazara. Saboda rashin ganin juna a kai- a kai ya sa sun zama suna marmari da shauqi gami da ɗokin son ganin juna. Wani lokacin ma ko muryoyin juna suka ji sukan wuni cikin farin ciki.
Zama kullum manne da juna yana kawo gundura. To a nan ba sararin kaɗai ake buƙata ba. Duk da cewa rashin ganin juna na ɗan lokaci kan haifar da begen son kasancewa tare da juna. Kada ma’aurata su zama masu sa ido da shisshigi a al’amuran juna. Amma kuma duk da haka, ma’aurata suna buƙatar lokacin kansu. Wanda za su zauna su biyu rak ko da sau biyu a wata ne. Domin sabunta soyayyarsu. Misali: Za su iya ware rana guda. Mai gida ya ce kada a yi abinci ya ɗauke ta daga shi sai ita ya kai ta gidan abinci. Su ci abinci su yi hira da sauransu. Ko ya ɗauke ta su yi tafiya su bar garin ko na kwana ɗaya ne ko biyu. Su samu kaɗaici da fahimtar juna.
Yin hakan ba ƙaramin taimakawa yake wajen raya soyyya ba. Har ma da farfaɗo da soyayyar da take magagin mutuwa. Amma sai an jarraba. Ko Turawa da Larabawa har ma Indiyawa da muke ganin kamar su ne gwanayen soyayya. Sai ka ga an daɗe da aure amma soyayyar tana nan daram. Su ma irin waɗannan dabarun suke amfani da su wajen tattalin soyayyarsu.
- Addu’a: Addu’a an ce makamin mumini. Kuma in dai ana son a ga dai-dai a rayuwa dole sai an riƙe ta. Abinda ya sa na bar ta a ƙarshe, shi ne: Ita addu’a tana tasiri ne idan kai ma mai addu’ar ka ɗauki matakin gyara tukunna. Ma’aurata suna manta daga sanda ka ɗauki niyyar aure, to ka ɗaura niyyar fito- na-fito da maƙiyanku da kuma maƙiyan aure daga shaiɗanun mutane da aljanu. Wajibi ma’aurata su kasance cikin addu’a domin su yi wa rayuwarsu da soyayyarsu garkuwa. Wannan kira ne musamman ga maza. Sun fi sakaci da addu’a. Da wuya namiji ya dage da addu,’a a kan iyalansa. Ma fi yawan lokuta sun fi yi a kan sauran fannonin rayuwa.