Daga BASHIR ISAH
Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce abin damuwa ne matuƙa yadda ake samun da yawan matasan Nijeriya na shiga harkar damfara a intanet.
Olukoyede ya bayyana a cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na X cewa, wannan bala’in ya kai matsayin da a yau, a cikin kowane 10 na ɗaliban Nijeriya za a tarar da 7 daga ciki suna ta’ammali da harkar damfara ta intanet.
Ya nuna damuwarsa kan wannan batu ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar kamfanin Daar Communication PLC da suka kai ziyarar aiki a ofishinsa da ke Jabi, Abuja, a ranar Litinin.
“Abin damuwa ne ainun ganin yadda a yau za ka samu bakwai daga cikin ɗalibai 10 suna harkar damfara ta intanet,” in ji Olukoyede.
Daga nan, shugaban na EFCC ya yi kira ga kafofin yaɗa labarai da su samar da shirye-shirye da za su riƙa faɗakar da matasan Nijeriya game da illolin aikata manyan laifuka ta intanet.
Ya ce, “Waɗannan su ne matasan da muke sa ran zama shugabanni gobe. Kada kafofin yaɗa labarai su yi ƙasa a gwiwa wajen faɗakar da matasan game da illolin da ke tattare da haka.”