
Daga Abubakar A Bolari, Gombe
Yakubu Da’u Gombe, wanda aka fi sani da Jikan Shehi kuma Almajiri mai kishin addini, ya yi tsokaci mai tsanani kan Gwamnatin Tarayya da wasu malamai daga yankin Arewacin Najeriya, musamman na Arewa maso Gabas, game da amincewa da shirin taron karatun Al-ƙur’ani da aka shirya gudanarwa a Abuja.
Ya ce babu wata hujja ta shari’a da za ta sa malamai su goyi bayan wannan shiri, inda ya bayyana hakan a matsayin wasa da addini.
Ya kuma ce, “A musulunci babu wani abu da ake kira bikin Ƙur’ani. Idan har wasu malamai na sukar Mauludi, wanda ya ke da tushen tarihi a Musulunci, to bai dace su karɓi wannan sabon tsarin da ake kira ‘Qur’anic Festival’ ba.”
Har’ilayau, ya zargi Gwamnatin Tarayya, musamman ɓangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, da rashin adalci, yana mai cewa kwanan nan ta kori almajirai daga Abuja, amma yanzu tana kiran malamai da almajirai sama da dubu 60 don taron bikin.
Yakubu Da’u ya gargaɗi malamai da suka amince su halarci wannan taro, yana mai cewa hakan wasa ne da addini.
“Babu wani malami a kasar nan da zai sake sukar Mauludi idan aka gudanar da wannan taro.”
A cewarsa, wasu malamai sun karɓi gayyatar ne saboda kwaɗayin abin duniya, yana mai zargin cewa an yi hakan ne don siyasa, musamman a zaɓen shekarar 2027.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta guji amfani da addini don cimma burin siyasa, yana mai cewa wannan shiri ba zai amfani addini ko al’umma ba.
