Daga USMAN KAROFI
Aƙalla mutane biyar ciki har da ƴan gida ɗaya su uku akai garkuwa da su yayin da ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Chikakore da ke Kubwa a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare ranar Lahadi, a inda maharan suka kutsa gidajen mutane suka sace wani mutum mai suna Akinropo, matarsa, ɗansa, da baƙonsu, tare da wani maƙwabcinsu. Haka kuma, sun ji wa wata mata rauni a kai ta hanyar dukan ta da kan bindiga, lamarin da ya sa aka garzaya da ita asibiti.
Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga sashin Byzahin sun isa wajen da misalin awa ɗaya da rabi bayan maharan sun tsere tare da mutanen da suka yi garkuwa da su. A cewar mazaunan, akwai filin da aka ware tare da ginin ɗakuna guda biyar don zama hedkwatar ’yan sanda a yankin, amma har yanzu ba a samu tura jami’ai ba. Ya ƙara da cewa irin wannan hari na ƙara tsananta tsoron al’umma, yana mai kira ga gwamnati da ta kawo ɗauki.
A baya-bayan nan, yankin Chikakore ya sha fama da hare-hare, ciki har da na watan Janairu inda aka kai hari da abubuwan fashewa da suka tsere daga Ƙaramar hukumar ƙanƙara a Jihar Katsina.
A lokacin wani abu mai kama da bom ya fashe a makarantar Islamiyya da ke kusa da Kuchibuyi a yankin Bwari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu, kamar yadda rahoton ’yan sanda ya tabbatar. Mazauna unguwar sun nemi a dauki matakin gaggawa don magance waɗannan hare-hare.
